HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

A Dan tsorace ta ‘dago Amma ganin Murphy saitaji tsoranta ya ragu ta sunkuyar dakai batareda tace Masa qalaba.

Zama yayi kusada ita batareda ya kalleta ba yace,

Ayshah…..

Dam gabanta yabuga sbd Bata ta6a tunanin yasan sunantaba.

Cigaba yayi da cewa,

Ayshah inason abokina sosai sbd shine sanadin danake cikin rufin asiri nida mamana da qannena harma nake karatu sbd shine yake biyamana komai.

Cikeda tsoro da mamakin Jin hausa ra’dam a bakinsa ta ‘dago ta kallesa batareda tabude baki tayi magana ba.

Murmushi yayi kafin yacigaba da cewa,

Ayshah akwai abinda nakamu da tsananin so tun farkon ganina da abin Amma yau an wayi gari Nik na tsananin son abin fiyeda tunaninsa wandashi bai gama gano hakanba..
Saidai nayiwa kaina alqawarin bar Masa abinnan natafiyata..

Kallonsa tayi cikin mamakin yanda yake fa’da Mata abinda bai shafeta.

Miqewa yayi tareda juyowa ya kalleta yace,

Goodbye ayshah duk da nasan destiny will bring us together again.

Wucewa yayi tabisa da kallo akaro na farko dataji kamar wani alamari nashirin faruwa da ita saidai abinda batasaniba Mai da’dine ko Mara da’di.

Harya 6ace Mata Bata daina kallonsa ba kamar daga sama saitaji antoshe Mata baki da qyalle an ‘dauketa tareda turata cikin mota akabar makarantar da ita.

Fitowa yayi mota jiki a sanyaye saiyaga wayam Bata gurin yana ‘daga Kai saiga fitar motarsu mujahid makarantar da mugun gudu.

Komawa motarsa yayi yabi bayansu a guje kaman zai tashi sama da motar.

Hanyar wajen gari suka nufa batareda sun lurada Yana biyeda suba suka gangara cikin dajin ka’dan saiga wani qaramin flat Mai kyau sukayi parking suka fito Shahid ne riqeda ita har lokacin bakinta a toshe niqaf dinta ma tuni yacire acikin motar Wanda tuni kyakkyawar fuskarta ta qara rura mugun nufinsu gareta.

Fixgo mujahid yayi tareda ‘daga hannu ya sharara Masa Mari yayi baya Yana yarfe hannu tareda sakin qaramar qara sbd xafin da hannunsa yaji alhalin shiyayi Marin Dan baita6a duka ko marin wani ba bare yaji zafi haka.

Daria suka sheqe da ita suna kallon yanda yake yarfe hannu Shahid yakallesa a ‘dage yace,

You see Mama’s boy you can’t do anything like a man so stop acting like child and leave.

Hasala yayi ya qara ‘daga hannu zai Mari Shahid mujahid yariqe Masa hannu tareda sharara Masa wani lafiyayyan Marin dayasashi qwalla qara tareda zubewa qasa yana riqe kumatunsa.

Kallonsa tayi tareda rintse idanuwanta hawayenta naci gabada gangarowa sbd tasanda bayada wani qarfinda zai taimaketa.

Ganin hawayenta yasashi miqewa cikin ‘yar jarumta ya Sha gabansu yazamto ita tana bayansa yakallesu da idonsa dasukai jajir sbd azaba yace,

If you don’t want to end your lives behind bars let us go.

Wata dariyar suka Kuma sheqewa da ita kafin mujahid yafara rufesa da duka Nan take hancinsa da goshinsa yafara jini gashi ko ka’dan baida kuzarin ramawa.

Lilis sukai Masa suka koma yimasa dariya ganin so yake yatashi yakasa.

Ahankali sautin kukanta yafara fita ta juya Masa baya tafara rero kukanta.

Duqowa Shahid yayi yakalli yanda yake Nishi yace,

Stop being stubborn and leave quickly okay lover boy.

Miqewa yayi a daddafe hannunsa riqeda gefen cikinsa dake ciwo sosai ya nufi motarsa.

Saurin juyowa tayi zuciyarta na karyewa ganin tafiya zaiyi ya barta dasu mujahid ‘din.

Kallonta yayi yaji duk jikinsa yayi sanyi sbd tun yanxu yafara gane bai cancancetaba tunda har yakasa samun qarfin ku6utarda ita.

Motarsa ya shiga daqyar ya iya Zama ya tada ita yayi ribas ahankali.

Saiti yayi dasu ya taho a guje yayo kansu a gigice sukabar gurin yadaki motarsu yayi saurin fitowa tareda bu’de Mata seat din gaba ganin tatsaya kallonsa ya’daga hannunsa yakamo nata yasakata cikin motar sukabar gurin da gudu.

 

Tunda yakamo hannunta shi take kallo ko qyaftawa Bata iyayi..

Did he take all this risks to save me from them..

Daf dazasu Isa cikin gari taga ahankali yafara rage gudu saikuma ya gangara ya tsaya tareda zubewa jikin sitirin motar a sume.

A gigice takallesa takalli waje taga hadari ya ha’du sosai har anfara yayyafi alamun saukowar ruwan.

Fitowa motar tayi hankalinta duk atashe saikuma ga ruwan sama sun 6arke masu qarfi sosai.

Bata damu da qarfin ruwanba ta tsaya bakin titi neman taimako Amma Sam Babu alamar mota bare tasaran samun taimako ga ruwan tuni sunyi Mata jagaf.

Dawowa motar tayi taga shima kusan duk ya jiqe sbd glass ‘din dake sauke.

Wata muguwar rawar sanyi taga jikinsa nayi sbd ruwan dasuka dakesa Nan take wahala ta canxashi taga yanda ruwan ke dukansa Yana Jan numfashin wahala gashi Sam takasa iya tada glass ‘din motar Sai kawai ta fito tazagayo bakin windon dayake ta tsaya ta tare Masa ruwan na dukanta jikinta na rawar sanyi amma bazata iya bari ruwan yaci gaba da dukansa ba.

Kusan awa ‘daya da rabi ana ruwan kafin suka tsagaita zuwa time ‘din daqyar take iya bu’de idonta sbd sanyi da mugun zazza6i Mai qarfi.

Bu’de idanuwansa yayi daqyar ya kalleta yaji wata muguwar zazzafar soyayyarta na sake shigarsa ahankali ya tashi zaune jikinsa na rawar sanyi ya fito tareda kamota daidai lokacinda take qoqarin zubewa yasaka cikin mota tareda kwantarda ita ya tayar da glass ya kunna ‘dumi.

Ahankali ya ‘daga wayarsa yakira wayar Murphy akashe kafin yakira mum ‘dinsa yafada Mata inda yake murya na rawa.

Fuskantar juna sukai ya qura Mata ido Yana qoqarin yaqar tsananin ciwo da zazzan zazza6in dayakeji.

Rintse idanuwanta tayi sbd Bata iya cigaba da kallonsa ko jure nasa kallon.

Ahankali ya bu’de baki cikin qaramin sauti yace,

I love you ayeeshah.

Bu’de idanuwanta tayi da sauri hawaye na taruwa acikinsu…

Kafin yakuma yunqurin wata maganar aka qwanqwasa glass din motar.

Shiyayi qarfin halin ‘dagowa yaga wani mutum da wata tsohuwar bus ya juyo ya kalleta yaga idanuwanta a rufe hawaye na tsiyayo da qarfi.

Cikin sanyin murya ya kalli mutumin yace,

Awuce da ita cikin gari.

‘dagowa tayi takallesa ya lumshe Mata idanu ta bu’de motar ahankali ta Fice jikinta a sanyaye zuciyarta na tsananta duka tashiga bus din suka wuce..

Harsun fara tafiya tajuyo takalli motarsa saita rintse idanu wasu sabin hawaye masu zafi suka gangaro mata.

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to follow, vote and comments_
[7/12, 7:40 AM] ‪+234 902 378 7901‬: *_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

 

*15&16*

Kodasu mum suka iso gurin ya Dade da fita haytacinsa Dan dama Yana daurewane gaban ayshah sbd kar abin kunyar yayi Masa yawa anyi Masa duka gabanta Kuma ya ciwo yayi Masa rigis gabanta.

Hankali tashe mum tasa akai asibiti dashi bayan ankira police sun fara bincike agurin Dan ga alamar duka Nan ajikin ‘dan nata.

Kodata Isa gida kasa tu6ewa tayi ta shige qarshen gado ta zauna tareda takurewa tana kuka ahankali sbd zazzafan baqon alamarin dataji yana shiga tareda Kama kowace kusurwar jijiyar dake aiki cikin zuciyarta.
Zazza6i ne Mai qarfi itama yakamata Nan take Wanda yasa hankalinsu husna tashi Amma ta hanasu fadawa iyayensu.

 

Kwananta ‘daya da yini tana fama da zazza6i da rashin sukunin zuciya.

Gudun zargi da tambaya yasa tashirya tacigaba da zuwa makaranta.

Koda ya farfado kansa ciwo yake sosai Amma haka ya nunawa mum ‘dinsa yaji sauqi dole aka sallamesu duk da mura yake sosai sbd dukan da ruwa sukai Masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button