TAYI MIN KANKANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAYI MIN KANKANTA 16

????????????????????????????*TAYI MIN ƘANƘANTA*

????????????????????????????????

*Zahra surbajo*

*banida lafiya ne,kuma ga mara lafiyan danake kulawa da ita,shiyasa abubuwan suka chushemin,pls asamu a addua,Allah ya bamu lafiya*

*16*

A harabar gidan sukayi parking a gurin da aka tanada domin hakan.

   Fitowa sukayi fuskokinsu ba yabo ba fallasa,suka nufi cikin gidan.

Sallama Hammad yayi afalon amma baa ansa ba,hakanne yasa ya fahimci tana ɗaki.

“zauna mana ka tsaya kamar baƙo,bari inje in kirata ku gaisa”Hammad yace yana ƙoƙarin haurawa benen.

Zama jameel yayi a sanyaye shi ya rasa meke damunsa da yasa yanayinsa ya sauya.

A gefen gado ya sameta zaune,ta lulluɓe fuskarta da jikinta da mayafi,ko baa faɗi ba kuka takeyi.

Sallamarsa ce tasa ta ɗago dara daran idanuwanta ta dubeshi suna tsiyayar da hawaye,

Tausayinta ne ya kama Hammad,a hankali ya ƙarasa kusa da ita ya zauna,ya sa hannu ya dafo kafaɗarta yace a sanyaye.

“kince kina sona ke ba auran dole aka miki ba,to kuma se gashi se kuka kike kamar wacce aka yanka,ko kin dena son nawa ne?”

murmushi tayi sannan ta girgiza masa kai,

“to tunda ba haka bane share hawayenki kizo muje falo gun babban aminina ku gaisa tare muke dashi”

Share hawayen tayi sannan ta miƙe shi kuma yayi gaba,da sauri ta ƙarasa jikinshi ta ruƙo hannunsa ta kwantar da kanta a gefenshi.

Hammad bece komai ba ya buɗe ɗakin sika nufi falon.a hankali.

Jameel tunda suka jero sosai suka burgeshi,yaji dama ace da ƴarfillo yaga aminin nasa dase yafi jin daɗi.

Kujerar dake kallon ta jameel ɗin suka zauna fuskarta a rufe da mayafi.

“A gaskiya ba abinda zamu cewa Allah sede godiya,daya kawomu lokacin da aminina ya fita akasuwa”cewar jameel yana murmushi.

Dariya Hammad yayi sannan yace”zakuma mu ƙara godewa Allah in ya nuna mana ranar da kaima zaka bar kasuwar”gaba ɗaya suka tuntsure da dariya.

Ita de zahra ba dan kar ta gasgata kunnenta ba da se tace tasan muryar nan da jimawa,amma seta kauda tunanin hakan.

Sosai jameel yay musu faɗa da tunasarwa kan suji tsoron Allah inda aƙarshe yace”kuma shi aure ibada ne kowacce ibada abar tambaya ce agurin Allah kaji tsoronsa,kar son da kakewa waccan yarinyar yasa ka cutar da wannan,wallahi Allah baze barka ba”.

A sanyaye Hammad yace”insha Allahu son waccan baze cutar da wannan da komai ba,zan kula”

Miƙewa jameel yayi yana duba agogo,yace yana kallon zahra data rufe fuska da mayafi”Amarya me rowar fuska,gashi har zan tafi banga kamannin amaryar ba”

Da sauri hammad ya kamo mayafin nata yana dariya yace”tuba muke ina zaa yima rowar fuska ay dole ka ganta,”ya ƙarasa buɗe masa mayafin data rufe fuskar.

runtse idonta tayi tana dariya,wanda ya bayyana wushiryarta da lotsawar kumatunta,fess ya ganeta dan duk tsayin zamani da sauyin yanayi,jameel baze kasa tino kamannin ƴarfillo ba.

Sosai gabanshi ya faɗi tsoro ya mamaye zuciyarshi,tambayoyi fall cikinsa,amma a bayyane cewa yayi “masha Allah,daddy gaskiya ya gwangwajeka,to Allah bada zaman lfy bari in ƙarasa gida”yana faɗin haka be jira amsarshi ba yayi sauri ya bar gurin gudun kar ta buɗe idon ta ganshi.

Rakoshi Hammad yayi yaga tafiyarsa sannan yakoma cikin gidan,zuciyarshi cike da damuwa ganin abokin nasa duk abirkice yayin barinsa gidan nasu.

Muje zuwa

Surbajo for life.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button