TAYI MIN KANKANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAYI MIN KANKANTA 2

 

???????????????????????????????? *TAYI MIN ƘANƘANTA*

????????????????????????????????

*Zahra Surbajo*

*2*

 Gudu-gudu sauri-sauri Zahra’u ke tafiya zuwa gida,dan azahar ta kusa,

   Tana shiga gida bukkar innarta ta shiga da sallamarta.

“wai har kun siyar?”cewar inna bayan ta amsa sallamarta,

Murmushi Zahra’u tayi sannan tace”wallahi inna mun siyar,yanzu ma wasu sojoji ne,suka roƙeni in dafo musu abinci,yunwa sukeji gashi suna da me ulcer acikinsu,shine na dawo in musu”daga haka ta kwashe komai ta faɗa mata,gami da bata kuɗin.

Sosai inna ta tausaya musu sannan tace”Allah miki albarka Batulu na, daɗina dake akwai tausayi, maza zo kije ki cefano abinda yadace ayi sauri ayi musu”

Daga haka miƙewa sukayi suka fito tsakar gida,inna ta bata kuɗin cefanen ta tafi.

Kamin la’asar sun kammala komai,abinci lafiyayye bame cewa daga rugar aka girkoshi,domin,harda,cincin,dublan,duka masu jimawa basu lalace ba kasancewar  can cikin garin falgoren Zahra’u tazo cefanen,shiyasa tasamu komai.kasancewarta ƴar makarantar gaba da primary,kuma ɓangaren sciece yasa ta iya komai,sabida food and nutrition da ake koya musu.

Ga kaji da zabbi da suka soya musu rabi da mangyaɗa,rabi kuma da manja sabida me ulcer shima yasamu yaci,suyar sosai tayi kyau.a ledoji ta juye sannan ta zuba abincin a kular abincin baffanta,

A babbar roba ta zuba komai sannan tayi gammo ta ɗauka,inna ta bata canjin dubu biyar daya rage tace ta mayar musu,amsa tayi sannan ta juya ta nufi barikin.

Kusan mintuna arbain ta kwashe tana tafiya kamin ta iso bakin titin,sannan ta ƙarasa gurin da sojojin ke tare.

Inda sukayi dashi zasu haɗu nan ta ƙarasa,ga mamakinta yana tsaye agurin yana jiranta,yana hangota ya taho da sauri ya tarbeta yana murmushi.

Kama mata kayan yayi ta sauke,sannan tace”kuyi haƙuri wallahi gidanmu da nisa ne shiyasa” 

Murmushi yayi yace”Ko kaɗan baki buƙatar bamu haƙuri,mune yakamata muyi hakan,mungode sosai,Allah saka miki da alkhairi,”

Canjin ta miƙo masa tace “ga canjin ku inna tace in dawo dashi,kuma tace tanawa abokin naka me ulcer ya jiki dafatan Allah ya bashi lafiya”

Sosai wani jin daɗi ya bayyana a fuskarshi,aranshi ya yaba da tarbiyyarta,cikin murmushi yace”ki maidawa inna kuɗin kice mungode”

Fafur taƙi amsar kuɗin,duk yadda jameel yayi da ita ƙin amsa tayi dole ya maida kuɗin aljihunsa, 

“gobe in munzo talla zan tafi da kwanukan”tace sanda take ƙoƙarin tsallaka titi domin ta koma gida.

Sallama sukayi ta tafi,jameel yabi bayanta da kallo yana yaba natsuwarta da hankalinta.

Duƙawa yayi ya ɗauki,robar abincin ya nufi tantin da suka haɗa na tempol sabida ruwa da rana,kamin ay musu izinin shiga cikin barikin.

Zaune yake daga ƙarshen tantin,yana latsa wayarshi,hannunshi ɗaya,riƙe da bindigarsa,

Farine sosai yana da ɗan faɗin fuska kyakkyawa ajin farko,sede ko kaɗan ba fara’a fuskarsa.

Sanda jameel ya shigo tantin,a yatsine ya ɗago kyawawan idanuwansa ya kalleshi sannan ya amsa sallamarsa.

Robar abincin ya ajiye akusa da shi sannan ya shiga ciro kayan dake ciki,

Buɗe ledar soyayyun kajin yayi,sosai yayi mamakin ganin harda wanda aka soya da manja,

Ƙamshin abincin ne,yasa ya ɗago kansa da sauri yana bin ledar da kallo,da sauri ya matso kusa da jameel,yana faɗin”kunyi waya da mummy ne?”ya tambaya cikin zaƙuwa.

“me ka gani”jameel ya tambaya.

“itace kawai take soyamin kaza da manja sabida ulcer ta,shiyasa nayi zargin kunyi wayane”

“ko kaɗan,wannan wasu nasamu suka dafo mana,daga cikin garin nan,ka matso kaci abinci kasan tunda mukazo baka ci abinci ba tun ɗazu hankalina be kwanta ba sabida baka ci abinci ba”

Tausayin jameel ɗinne yakamashi ganin yadda yadamu dashi fiye da kansa,yasan duk ƙoƙarinnan yayine domin shi.

Ba musu ya matso yasa hannu ya ɗauki cinyar kazar yasa abakinsa,daɗin daya gauraye bakinsa sosai yatafi dashi,zagewa yayi yaci abincin sosai dan wannan girkin ma yafi na mommynsa daɗi.

Bayan sun gama cin abincin,su cincin da dublan din duk acikin jakun kunansu suka saka,sabida taimakon gaggawa,abincin kuma rufe sauran sukayi,sabida dare.

Se a lokacin suka samu natsuwa,Jameel ne ya dubi abokin nasa yace cike da kulawa”Gaskiya Hammad yarinyar nan ta iya girki,ba me cewa ita ta girka,ji abinci don Allah sekace a birni”

Cikin rashin fahimta,Hammad ya kalleshi,yace”dama yarinyace ta dafo abincin?”

“eh yarinya ce dan bata wuce sa’ar su surayya ba,ma’ana bazata wuce 14 to 15 years ba,nono suke siyarwa na roƙeta ta girko mana”

Sosai abun yaba Hammad mamaki dan shi de in ze iya tunowa ba ya jin ko gas surayya ta iya kunnawa bare ayi zancen dafa ruwan zafi,to taya yarinya sa’arta za’ace har tafi mummynsa iya girki,ta ya?

“Dan haka in munyi settling komai  zan bita inga gidansu,dan mu dinga zuwa cin abincin can gidansu mudena sata wahalar kawo mana”jameel ya faɗi yana kallon Hammad ɗin.

“ba damuwa “Hammad ya faɗi yana  nazarin zancen.

“innarta ma tace aymaka sannu gameda ulcer da take damunka “jameel ya faɗi yana murmushi dan yasan bazasu wanye lafiya ba.

A fusace Hammad ya dubeshi yace”Au kace bara kaje kayi da ciwon dake damuna,amma wallahi ka cuceni kuma ba inda zani wallahi bazan je gidan nasu ba”ya faɗi sanda ya miƙe ya fice daga tantin.

Muje zuwa

Surbajo for life

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button