MATAR UBA COMPLETE

MATAR UBA 37

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

CHAPTER 37

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Mc yace “To Allah Yasa lafiya,tunda Wanda ake taron don su sun watse ina ganin ai gara mu tashi muma,kashe kid’an akayi sai surutai kake ji kowa na fad’an Albarkacin bakin sa.

Sunyi sa’a su Hashim Basu tafi ba,babu Wanda ya tsaya magana suka lodo a mota, hashim ke jaan motar, a guje ya fizgi motar suka bar haraban hall d’in.

💦💦💦💦💦💦💦💦

………….”farees yanzu shi Alhaji khamal d’in ne yace maka haka?” 

“Eh wallahi yace min ya Kira ka baka d’aga ba,ya Kira number faysal da Asiyah duk baku d’auka ba,sai ya Kira ni, ya fad’a min Wannan mumunar Labarin”

Hashim yace “Yanzu yana ina?”

“Yana gida don yace min har sun shirya wajen zuwa dinner d’in,sai aka kirashi aka Sanar dashi”

Asiyah tace “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un Shikenan mun mutu”

Hashim yace “Asiyah ki kwantar da hankalin babu abinda zai same mu kinji”

Kai tsaye gidan su Yesmin sukayi, da sauri suka fito Kai tsaye suka shiga cikin gidan, Khamal da Nana sai Aunty Rukayya suna tsaye sai safa da marwa suke, suna ganin sun shigo a tare sukace “Alhamdulillah dukkan ku Kuna Nan ko?”

Murya na rawa Safiyya Tace “Yanzu da gaske mummy ta gudu?”

Nana tace “Eh bata asibiti Kuma an nema ta ba a ganta ba,Ashe tun da safe ta bar asibitin”

Diyya Tace “Amma ta yaya? How comes ta gudu,me polisawan sukeyi har suka Bari ta gudu”

Khamal yace “Tayi outsmarting d’in su ne ta samu ta gudu sanan ta rubuta wannan wasikar ta ajiye”

Hashim ne yayi saurin sa hannu ta karb’a, ya Fara karanta shi a bayyane kamar haka.

“Na fad’a Muku babu Wanda zai iya kamani, Kun d’auka wasa nake ko to gashi na fito,Kuma yanzu Haka ina farautar ku, Nana daga kanki zan fara yanda Kika ci amanata Sai na kwakule Miki Ido na cinye,ke Kuma Rukayya Sai na yanka ki gunduwa gunduwa har ki mutu, Safiyya ke ‘yatace Kuma gudan jina nace kisa a ranki cewar maza goma zan d’auki hayar su,su Miki fyad’e har sai kin mutu, faysal da farees naku Mai sauki ne Zan sa a kashe min kune kawaii sabida laifin naku Mai saukine, Yesmin ke Kuma hukunci ki shine a gaban idon ki Zan sa a kashe min iyayen ki, Hashim  Kai Kuma da Asiyah hmm bazan fad’a ba sai dai mun had’u daga yau zuwa gobe duk Zaku kwana a makabarta.”

Hashim yace “Wannan ai shirmen banza ce babu abinda zata iyayi,Kuma insha Allah sai an Kama ta” ya nufi hanyar fita khamal ya tare shi ya nuna Masa wuri Zama ma’ana ka zauna,zama yayi Yana huci dukkanin su hankalin su yayi matukar  tashi, Asiyah tunda aka karanta wasikar idanun ta suka bushe ta kasa kukan ma gaba ki d’aya.

Fadeelah sai kiran Hashim take, ganin  yanda ta damu ya koma gefe ya mata bayani Kuma ta fahimta sannan yace ta bawa mutanen da suka tara hakuri hakan kuwa akayi.

WASHE GARI

………. A zaune suka kwana duk cikin su Babu Wanda ya rintsa, sai sallar asuba ne kad’ai ta tada su bayan sun idar suka dawo suka zauna, Yan matan ne suka samu suka lallab’a suka had’o musu tea suka sa cikin su,don duk cikin su babu wanda zai iya cin abincin.

Wai shin ina Baraka??

……. Baraka tunda ta baro asibitin, Kai tsaye gidan ta, ta nufa a zaton ta zata ga Asiyah da Safiyya, dariyar mugunta tayi tace “Yan iska Ashe dai Kuna tsoro na, da ku zauna a gidan Mana kuga yanda zanyi daku”

‘dakinta ta shiga ta ‘debo makudan Kud’i ta fito waje, ta Mika wa mai gadi wasu bandir biyu Tace “kaje na sallme ka”

Zaiyi magana ta daka Masa tsawa, “ka fice min a gida”

Jiki na rawa ya fita ko kayan sa bai d’auka ba, a gidan nata ta kwana duk da cewar ita ma ta kasa baccin ga kafarta da yake ta zogi karaya tafi wata ‘daya amma yaki warkewa, da asuba ta fita, ta tari Keke napep sai da suka bar cikin gari ta umurce shi da ya tsaya, Kud’i Mai yawa ta Mika mishi, tana d’ingisawa har ta Shiga jeji, ta d’auki tsawon Mintuna talatin Kan ta nufi wata karamar bukka irin gaisuwar su ta matsafa ta Masa, ya amsa bayan ta zauna ta juye masa dukkanin kud’ad’en da suke cikin Jakar da ta ratayo,wata iriyar dariya yayi, yace “me kike bukata ayi miki?”

Nan ta kwashe cin amanar da akayi mata ta fad’a Masa ya girgiza kai yace

“Na ji matsalar ki idan na fahimce ki fansa Kika son d’auka ko?”

“Eh fansa nake so,mafi munin fansa”

Ya kyalkyale da Dariya Mai tsoratar wa yace an gama,wasu gari kulli biyu ya Mika mata yace wannan, ki yi wanna dashi wannan Kuma ki watsa musu a jikin su idan suka Shaka Shikenan kin gama dasu”

Murmushi tayi tace “Nagode Nagode”

Tsawa ya daka mata yace “Kin San bana son godiya idan kina so ki gode min kin sab irin godiyar da nake so”

Murmushi tayi tace “Hakane barin shuga daga ciki” 

Cikin bukar ta shiga ta tub’e tsirara haihuwar ta ta kwanta a Kan Yar karamar gadon dake d’akin,boka na shiga dake dama zani kawaii ya d’aura ya kwance ya fad’a mata, Baraka duk da bata jin dad’in abun Amma ta dage wajen bashin had’in kai  a tunanin ta idan yaji dad’in ta aikin zaifi tasiri.

Ya d’auki tsawon awa d’aya Yana Abu d’aya idan ya gaji sai ya huta ya Kuma d’aura daga inda ya tsaya,ya samu na banza ai Dole, sai dai ya gamsu sannan ya kyale ta, kayanta ta Maida ta tashin ta fita, tunda ta hau Kan titi Bata samu abin Hawa ba tayi tafiyar awa d’aya har ta Fara shiga cikin gari wani Keke napep ta hanga tana Masa magana baiji ba, dake yana ta gefen Titin ne ganin in bata karasa  gunsa ba zai iya tafiya, da saurin ta hau Kan titi bata lura ba Ashe akwai babban Mota Daf irin Wanda ake da shanu a cikin yayi kanta jaan kafarta take amma ina har motar yayi kanta ,Mai motar yayi kokarin kacewa amma ya kasa.

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button