TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Tukucine ga masoyana! ????????????
Ahankali natashi daga kwanciyar danayi na kalli zoben dake hannuna, sansanyar ajiyar zuciya na sauke tare da sakin murmushi abayyane.cikin natsuwa na saukar da kafata daga kan gadon danake kwance na jawo pillow dake kusa dani na rungume ina jin wani shauki da sanyi a raina, na shiga duniyar tunanin dana saba.kamshin turarensa ne ya tabbatar mani da ya shigo dakin.da sauri na dago kaina na kalli kofar dakina sai naji muryar danake tunani.sallamarsa ce ta dawo da hankalina nayi saurin aje pillown dana rungume na amsa masa batare dana kalli kofar ba, na bude bakina cikin sanyin murya na ce shigo mana yayana.
Cikin natsuwa naji ya bude kofar ya shigo na kalleshi cikin kwarjini irin nasa, ya kalleni yayi murmushinsa mai ban sha’awa ya kira sunana hawwa kintashi lfy?na kara sunkuyar dakaina kasa ina wasa da zoben hannuna na amsa masa lfy klau yaya yusuf.
Ya kara kallona sosai yace yau baki zuwa skul ne? Naga har yanzu baki shirya ba?cikin hanzari na tashi nace yanzu zan shirya, kafin ya kara magana nayi saurin cewa ka gama ne?ya juyu ya kalleni ya ya jinjina kansa almar eh.dama na tambayi umma ne kina ina?shine tace in dubaki ko kin gama.na girgiza kaina nace a’a, amma yanzu zan shirya, nima banyi tunanin zaka fito yanzu ba.
Masha Allah ???? ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? taku ceeeee sa’ar mataaaaa????
TUN INA KARAMA ????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Tukuicine ga masoyana! ????????????
Page 2
………..Uhum hawwa kenan, kinsan yadda nake son karatunki arayuwata kuwa?ya jefo mani tmbyr batare da alamar wasa ba walhi ban hada karatunki da komi ba.ya sake juyawa batare da ya kara kallona ba yace ina jiranki bana son ki bata lokaci.nima na amsa da to yaya shikuma ya fita daga dakin.
Ni kuma na shige toleit domin in yi wanka cikin minti bai wuce shabiyar ba nagama shiri na tsab.na fito cikin atamfata mai ratsin blue da mayafina na yane jikina, ga kamshin turarurukan dana sanya ma jikina, don ni din ma ma abociyar kamshi ce.
Nasa takalmina simple da jakata sai wayata dana dauka na fito na tunkari falon mu ina shiga na iske shi da umma suna magana, “ya kalleni sai kuma ya daure fuska cikin daga murya yace umma wai yaushe wannan yarinyar zata yarda ita matar aure ce!!!
To fa ???? babbar magana masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? takuce sa’ar mataaaa????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 3
……….muryar umma ce cikin tsawa tare da daga masa hannu !! Yusuf ya isa haka ! Wai yaushe zaka daina yaudarar kanka ne? Bayan kasan hawwa bazata taba komawa gareka ba, cikin takaici ta girgiza kai tace to ya isa haka nagaji da wannan rashin imanin naka yakamata kabani takardar ta haka nan ko kuma in dauki mummunar mataki akanka.naso mu rabu lfy da kai amma kullum sai ka bata mani rai akan wannan auren naka wanda bashi da ma ana why? Wallahi bazan taba yarda da zalincinka ba cikin sauri ta tashi ta shige daki cike da tashin hankali.
Shi kam yusuf tunda umma ta fara magana kanshi yana kasa ba abunda yakeyi zubda hawaye.ni kuma tsaye nake inda nake kamar an da sani sbd aduk lkcn da irin haka zata faru tsakaninmu ni kaina ina jin tsanar shi araina fiye da tunanin mai karatu.rufewar kofar umma ce tasanya gaba dayan mu dawowa daga duniyar da muka fada.ido cikin ido muka kalli juna ya yunkura zai karaso inda nake, cikin hanzari na juya dakina da gudu sbd wani irin kuka daya taso mani.
Ina shiga na rufe kofata da key, na watsa kayana bisa gado na fada kan gadon na cigaba da tariyo abunda ya faru tsakanina da mijina yaya yusuf da kuma matar shi wadda ayanzu itace acikin gidan shi.”hawwa hawwa hawwa yusuf ya keta kira bayan ya murda kofata yajita rufe.ki fito mu tafi zaki makara, plsss hawwa cikin muryar lallashi.ina jin shi haka na share shi.na cigaba da kukana
Yafi minti goma yana bakin kofata yana rokona in fito.can cikin tsawa naji umma tana ce mashi, yusuf zo kabar mani gidana kafita tun kafin inyi maka hukunci i said get out!!!
Ni kaina saida birona ya fadi????sbd tsoro gsky bari in dan maida numfashi wai Allah umma daga gani akwai fada???? masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? takuce sa’ar mataaaa ????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 4
…….juyawa yayi yana kallon umma batare daya kara cewa komi ba, ya saki kofar ya nufi kofar fita daga falon.yana fita ta bishi ta rufe kofar.
Koda ya fita wajan motar shi ya nufa ya bude ya shiga, yafi minti shabiyar yana zaune acikin mota ya maida kujerar baya ya kwanta.tunani kawai yakeyi yanda abubuwa suka rikice masa a lkc guda.
Bayan shidai yasan ba laifinsa bane amma kowa ganin laifinsa yakeyi, in harda iyayensa babu mai goya masa baya.ita kanta hawwa yana hango tsanar shi a idon ta duk irin soyayyar dake tsakaninsu da kauna da shakuwa amma duk ta kauda kai itama tana gasa mashi aya a hannu.ahankali ya furta why?why hawwa bansan komi ba sai soyyarki babu kowa araina saike kaddara ta kenan auren jamila wanda shine silar lalacewar komi tsakaninmu.tun kina karama, kece araina kuma kece mace ta farko danike ji araina da sauri ya dafe gefen zuciyarsa , insha Allah zaki dawo gareni babu rabuwa tsakaninmu da yardar Allah.
Jin tashin motar shi yasa na tashi da sauri na nufi wurin window na na bude labulen daidai da lkcn da baba mai gadi yake bude masa get ya cilla motarsa kan titin unguwarmu fice daga unguwarmu ta G.R.A.
Ajiyar zuciya na sauke tare da sakin labulen na juyo kenan naji umma na buga mani kofa, cikin hanzari na isa bakin kofar na bude mata, naja da baya gefe tashigo kallo daya tayi mani tasan naci kuka, ba tare da tace komi ba ta kama hannuna muka zauna kan gado.cikin kulawa da tausayina aranta naji ta kira sunana, cikin sanyin muryata na amsa da na’am ummatah.sai ta cigaba da cewa ina rokonki hawwa kada kisa ma rayuwarki zaki koma gidan yusuf.cikin tashin hankali tare da jin wani abu ya bugar mani zuciyata haka naji!ta kalleni ido cikin ido ta jinjina mani kai alamar eh da gaske take.
“Kin sandai ni na haifi yusuf kuma amma bana son zamanki dashi sbd babu adalci zaluntarki kawai akeyi, nikuma bazan taba yarda da cin amanarki ba amatsayinki na marainiya, kaunar da yake maki tun kina karama yasa nayi kokarin ganin ya mallakeki.ashe kash!ba haka bane nayi kuskuren da nake son gyarawa yanzu.
Baroki danayi daga gidan shi ina ganin shine hanya mafi sauki kuma banyi nadamar hakan ba amatsayina na kanwar mahaifinki wanda bana fatan kisama ranki kin rasa mahaifi bayan gani da raina cikin damuwa umma tace baki taba kukan maraici ba haka kuma bazakiyi ba indai ina da rayuwa.
Hjy mariya zan barta da yusuf a matsayinta ta kanwar mahaifinsa tare da diyarta da yake aure na son zuciya.hmm amma hawwa bazan barki cikinsu ba sbd zan iya yafe yusuf acikin jerin yaran dana haifa amma ke amanata ce.
Jin kalaman umma sunyi tsauri nayi sauri dagowa daga kallon kasa da nakeyi, nace ummatah sai kawai ta daga mani hannu ta mike tsaye…