TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Bayan na tashi wurin karfe 10:30 sbd babu wanda ya tasheni saka makon umma tace abarni in huta.ina tashi da addu’a bakina tare da salati na mike na shiga toleit bayi wanka na fito na shafa mai ajikina tare da spray masu dadi ina cikin bude drawer ne in dauko rigar da zan sanya sai wata leda ta fado ina kai hannuna zan dauka gabana ya yanke ya fadi cikin sauri naje wurin window na yaye labulan inda yake parking babu motarsa ya salam!ina ka tafi bayan kace yau zamu bude wannan ledar yaya?why why kayi avoiding me?
To fah???? yanzu aka fara wasan fa menene burin jamila yaya hawwa zata dauki aurenta da yusuf?wace irin kalubale ke tare da rayuwarsu?to koma me kenan mujira dawowar Abba, ngd da kauna masu biyoni a pc suna nuna mani soyayyarsu da littafina mai suna tun ina karama????insha Allahu nima ina tare daku don jin dadinku ????????????masha Allah sai mun hadu a next page takuce ???????????? sa’ar mataaaa????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Cikin jin dadin maganganun mami gaba dayansu sukayi murmushi umar yace mami godiya muke Allah ya kara girma yasa kifi haka mami gaba daya suka amsa da Amin, yusuf tashi yayi yaje har gaban mami inda take zaune ya durkusa ya dora hannuwansa kan gwiwarta tare da kwantar da kansa yana jin wani irin son mami a ransa tare da kaunarta a ransa yadda take nuna masa karamci bashi da bakin gode mata sai yanzu yake jin kulu-kulun dake cikin zuciyarsa yake fashewa hawayen farin ciki ne kawai ke zuba daga idanuwansa yana jin wani rahama na sauka aransa mami kasa cewa komi tayi sai ma daga masa kai tayi tana share masa hawayen dake zuba daga idanuwansa tana jin wani tausayin sa da kaunar sa tana kara shiga cikin ranta tana ganin soyayya amma soyayyar yusuf da hawwa
Tun tuni yayi mata wuri na musamman arayuwa gaba dayansu birgeni sukeyi kuma yusuf yana son hawwa fiye da tunanin mai karatu haka itama hawwa anata haukan na kuriciya kawai yan uwan taka ne, cikin karfin hali mami tace my own son ina son kazama namiji tsayayye bana son ka kara zubar da hawayenka akan matarka wadda itace zabinka bazan so inga mace tana sanya yarona kuka ba gsky bazan lamunta ba sbd haka kada in kara ganin haka my son.cikin yanayin damuwa ya amsa da to mami insha Allahu na bari amma mami ina son hawwa kowa ma ya yasani amma ummah kullum nuna mani take zata iya rabani da hawwa kuma ni a tunanina babu wanda ya dace da ita kamar ni indai har tana son kwanciyar hankalin mu ni gsky bazan iya hkra da ita ba itace mace ta farko dana ji ina kauna tun ban san cewa sonta nakeyi ba sbd haka ina ftn zama da ita arayuwata na har abada.
Kallon ikon Allah umar yakeyi masa tare da tausaya abokin nasa don ya daina bashi mamaki tausayi yake bashi wanda tun tuni ya fada tarkon son hawwa amma yanayi da irin taurin kai irin na abokin nasa yasa yakasa tantance hakan, duba da yanda yanmata ke bibiyarsa amma yana avoiding dinsu lallai so daban ne Allah bamu masoyan gasky Amin.mami ce ta ka tse mas ushirun su wanda kowa da abunda yake kitsawa karka damu yusuf ummanka tafi kowa son zamanka da hawwa don na tabbatar babu wanda zata sallama ma kowa hawwa idan ba kai ba don haka ka kwantar da hankalinka babu wata matsala insha Allahu umar ya nisa “yace hakane mami nima abunda nake nuna masa abi komi a hankali haka dai suka ci gaba da maganganunsu da mami da cewar sun bar mata komi tayi masu jagora daga karshe suka tashi suka nufi part din yusuf da yake mallakinsa ne a gidan.
Sbd shima dan gidan ne suna shiga ko ina a gyare tsab ga kamshi yana tashi ko ina na kusuwar dakin sbd mami ba daga baya ba wurin tsabta koda yusuf ba zaune yake ba amma kullum cikin gyaran shi take ko ta gyara da kanta ko kuma su fatima su gyara sbd tace a koda yaushe yana iya shigowa suna shiga umar ya wuce bedroom bai tsaya yin komai ba ya fada toleit yayi wanka yana fitowa kwanciya yayi akan gadon dakin don ya gaji bai dade kwance ba bacci yayi gaba da shi.shi ko yusuf dama bai shiga ba falo ya tsaya ya zauna kan kujera sai yanzu ya tuna cewa ya kashe masu wayoyinsu cikin hanzari ya yasa hannunshi aljihun suit dinshi ya dauko wayoyin ya kunna don yasan rigima na can sunayi ita da umma kuka kam ya tabbatar ta sha shi har sai ta ba umma haushi kuma sai yaji ba dadi bai kyauta ba bari ya kunna wayar ya kirata ko kara zolayarta yayi
Yanayin dalling din no ta bugu biyu aka daga amma yayi mamaki idan dai har itace bazata daga ba har sai ta katsaye ya sake kira kafin ta dauka indai tana fushi dashi sallamar nabila ta katse masa tunani cikin fargaba nabila ta gaishe shi tace bacci takeyi yaya cikin damuwa yace bacci nabila?ki fada mani gsky fa yasake tmbyrta?cikin tsoro nabila ta baiyyana mashi komi duk abunda ya faru tace yanzu haka tunda abun ya faru batayi ma kowa mgn.cikin tashin hankali yace wasa nake mata fa?yanzu ina ummah ya tmby ta?umma tana part dinta taje ta dauko wani abu cikin hanzari yace to kada ki fada mata munyi waya ma insha Allahu i am my way to katsina.nabila ta amsa da to yaya itama hawwa kada ki sanar da ita daga haka ya kashe wayar yana dana sanin abunda ya aikata “nabila ta sauke ajiyar zuciya taji dadin hakan ko ba komi yar uwarta zata warware ta samu sauki indai yaya ya dawo na tabbatar zatayi kwanan farin ciki batare da damuwa bedroom din ya shiga yasamu umar har ya fara bacci cikin damuwa ya tashe shi tare da sanar masa katsina zasu koma sbd hawwa ba lfy cikin damuwa umar yace littel ba lfy me yasameta shima ya tambya cikin rudewa yana kokarin tashi.sai alkcn ne yake fada masa abunda ya aikata.cikin fushi umar yace walhi yusuf baka da tausayi saida ka kara sanya mata wata damuwa wai kai wane irin mutum ne?kullum a irin damuwar sanya ta ciki to ni gsky bazan yarda ba arinka yin wannan dani ba.
Walhi kuma wannan izzar dake bisa kanka garaka sauketa ka tarairayi abunda tuntuni shine zabinka to kana ji kana gani zakayi asara ka daina ganina kowa yana bayanka haka umar ya gama shiri ya yana bambamin fada shidai yusuf bai kara cewa komi ba tunda dai yasan bai kyauta ba umar nagama sanya kayansa yace ma yusuf bani wayata mika mashi yayi batare da yayi mgn ba yace daga yau kada ka kara yi mani irin haka yanzu ummah cewa zatayi hada baki mukayi yana gama fadin haka ya fita yusuf tashi yayi yabi bayansa ya rufe part din aranshi ya ce dole in lallabaka umar suna fitowa part din mami suka shiga suka sameta a falo ita da fatima da ta dawo daga skul kenan cikin kulawa tace a’a har angama hutawar ne mami ta tmby su.ta cigaba da cewa dama yanzu ummi take tmbyr big bros nace kuna ciki kuna hutawa ban ma san yanzu zaku fito ba ko ta karashe mgn tana dariya.umar ne yayi saurin cewa mami wani aiki ne ya taso mana yanzu ake neman mu a company baki zamuyi shine muke son juyawa insha Allahu yusuf baiyi zaton abunda umar zaice kenan ba kallonsa kawai yakeyi ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da hamdala tunda dai umar bai tona masa asiriba wurin mami fatima ce ta gaishe su tare da cewa nidai banji dadi ba walhi cikin damuwa ta kara she mgn
Umar yarinyar tana birge sa sai yaji ba dadi sbd tana da hankali kuma shu yawancin zuwan shi kaduna don yazo ya ganta ne shima yaso ace ya kwana amma wannan guy din ya rusa komi amma ba komi yasamu lkc ya dawo ya ganta ya fadi cikin ransa.mami ce tace idan banda abunki ummi ai zuwan su ba matsala bane ko yaushe zaki iya ganinsu a haka dai sukayi sallama suka rako su har bakin mota mami ta bada sako akawo ma ummah saida suka fita get din gidan ne suka koma ciki mami ta fahiimci dawamuwa a wurin yusuf sbd tasan waye yusuf?