HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

 

 

Yusuf na komawa ciki yasamu falon ba kowa sai TV shi kadai yana ta yi murmushi yayi yaje ya kashe tv ya kashe wutar falon shima ya wuce part din shi cike da farin ciki da jin dadi aransa.

 

 

 

Hhhhhhhh yaudai ba matsala ran masoya fes yake sai mujira zuwan Abba musha biki dftn yan gidan nan zakuyi mana kara muje mu kwaso shokiiiiii????????????????masha Allah har kullum ina kara jinjina ga readers da kuke bani kwarin gwiwa da comment nikuma nake jin dadin sambado maku labarin TUN INA KARAMA ????takuce sa’ar mataaaaa ????????

TUN INA KARAMA ????????????????????????????????

 

 

 

By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com

 

 

Page 15

 

 

 

Members ayi hkr da rashin jina da akayi na kwana biyu na dan zama busy ne amma nima nayi missing dinku irin sosai sosai din nan ????????????????????????????

 

 

……….kwana nan Abbah biyu da dawowa ya kira hawwa da yusuf domin basu hakkin su na tabbatar mashi da son junansu gaba dayan su sun tabbatar da cewa suna kaunar junansu “masha Allah Abbah ya furta bayan jin ta bikinsu tare dayi masu ftn Alkairi, bayan fitar su ne Abbah ya kalli umma wadda take zaune gefensa kana kallonta kasan tana cikin farin ciki yace hajiyatah insha Allahu zan tabbatar maki da cika alkawarinki da kika dauka batare da wata matsala ba.” Cikin jin kunya ta ce ngd Alh Allah ya kara kauna jawo ta yayi jikinsa tare da cewa Ameen khadi????naga alamar dai Abba da umma soyewa za’ayi shiyasa na rufe masu kofa na dawo ma yaran nasu masu juran gado????suna zaune a falo daga gani suma cikin farin ciki suke hawwa ce tace yaya zan shiga in kwanta nasan nabila na can tana jirana , cikin tsokana irin tashi yace “ai dai tasan tare kike da mijinki ko?cikin jin kunya tace haba tun yanzu ai nabila bata cancanci haka ba.nasani ya bata amsa amma ai nasan gulma zaku kuyi ko kafin kuyu bacci haba yaya mu kuma gulmarwa zamuyi?ta tmby shi tana dariya tawa mana ya bata amsa” to me kayi ta tmby shi?kice mata ina sonki kamar in kashe kaina to fah ta zaro ido tare da dafa gabanta cikin shagwaba tace ai ba sai na fada ba kowa ma ya sani tashi yayi yace to tashi ki shiga nima zanje in kwanta cikin jina danayi nayi missing dinshi muryata a sanyaye nace saida safe yayana , daga mani hannu kawai yayi tare da shigewa part dinsa haka muka rabu tare da kewar junanmu.

 

 

 

Lbr ya isa ko ina aurena da yaya yusuf wanda har kankiya wurin hjy kaka ta bada goyon baya dari bisa dari haka mahaifin ummah tare da sauran yan uwa kowa na murnar auren sai dai ta bangaren hjy mariya da jamila abun yazo masu a bazata wanda hjy mariya saida taje har kankiya wurin hjy kaka tayu korafi akan umma ta gaje masu komi na dan uwansu kuma sannan dole ta hada auren yusuf da hawwa.hjy kaka taka mata birki tayi nacewa kada ta kara zuwar mata da irin wannan maganar banzar idan bazatayi masu ftn Alkairi ba to tayi shiru da bakinta.

 

 

Haka ta koma jiki ba kwari jamila kuwa hankakinta yayi mummuna tashi wanda ya kaiga har ciwo tayi sbd damuwa ana cikin wannan halin ne kawar hjy mariya ta bata shawara akan su nemi mafita tun wuri kada ta jazama diyarta wahala haka kuwa akayi don ta nemo masu mafita wurin zuwa wani kauye dake kafur wurin wani boka da yake can, da wannan shawarar suka yanke zuwa wurin bokan, haka suka kama hanya suka tafi batare dajin tsoron komi ba bare shakkar ubangiji Allah ka tsare mana imanin mu ????Ameen ya Allah.

 

 

Haka suka kurda cikin dajin wurin wannan mushiriki koda suka isa kafin suyi masa bayanin komi yace basai sun fada ba yasan da zuwansu haka ya zaiyyana masu komi kamar yadda suka sani cikin wata irin dariya hhhhhhhh yace masu kar ku damu akwai nasara amma ba yanzu ba sbd wannan auren sai anyi shi kuma duk wanda yace zai raba to zai mutu ne amma bayan auren muna iya juyar da hankalin shi yaron akan diyarki yaji duk duniya bashi da kamarta kuma ko uwarsa da take tsaye akanyi mashi Addu’a baxai saurareta ba har sai ya auri diyarki abisa sharadin bazata taba yarda ta haihu dashi ba sbd shi mutum ne mai son haihuwa kuma har matar daya aura itama bazata haihu ba mudin ta yarda ta barta ta haihu to komi ya lalace kuma da zarar haka ta faru to ni ba ruwana don zai tsani diyarki fiy da tsanar da yakeyi mata yanzu hhhhhhhh kin amince za’ayi aure nan ba da dadewa ba amma ba haihuwa cikin tsoro mariya ta kalli kawarta ita kuma ta daga mata kai alamar ta yarda cikin sauri hjy mariya ta amsa data amince hhhhhhh boka yace to ku tashi ku tafi sai bayan an gama hidimar bikin shi da wannan yarinyar zaku dawo akwai abunda zan baku da zarar sun hadu shikenan angama to boka mun gode kkkkkkk ba ayi mana gdy ku tashi ku tafi haka suka tashi jiki na rawa ta bude jakarta ta debo kudi batama san ko nawa bane ta ajiye mashi tunda ya juya bai sake yi masu mgn ba har suka bar wajen.

 

 

 

Suna cikin tafiya ne hjy mariya ta kalli hjy lami kawarta”tace anya lami jamila zata amince da sharadin bokan nan kuwa?dariya tayi tace to ai ba fada mata zakiyi ba cikin hikima zaki nuna mata kada ta yarda ta saki jiki ta haihu yanzu sbd haihuwa na sanya tsufa ta bari tukunna sai nan gaba kuma sannan duk yanda za’ayi kada ta bari wannan yarinyar ta haihu sbd za’ayi zarginta ace itace bata son haihuwa tunda tafita wayo da gogewa.”kai lami shiyasa nake son harka dake gsky kin kawo shawara ngd sosai “kai haba kawata ai wannan yima kaine to ba komi komi zaiyi daidai zan nuna mata ta saki ranta lkc ne kadan tafawa sukayi tare da shewa a haka suka koma katsina cikin farin cikin samun mafita Allah ya tsare mana imaninmu ????Amin ya rabbi.

 

 

 

Shiri akeyi ta ko ina acikin family don yanzu haka na aunty zainb taje dubai ta hado lefe tunda bikin wata dayane aka sanya haka cikin hikima mami tace ummah ta barta tazo kaduna ta kwana biyu sbd akwai wata kawarta yar maiduguri ce tana yin gyaran amare haka kuwa akayi saura sati biyu ummah ta sanya yusuf ya kai hawwa kaduna ita da nabila don nabila tace bata iya zama ita kadai tunda aunty zainab da nafisa ta tafi dubai haka yusuf yaji ba dadi duk da dai ya kasa fahimtar komi kuma mami tace mashi basai yazo kaduna ba tare zasu dawo katsina da hawwa in lkc yayi

 

 

 

Tabbas wani kaya sai amale hakika mami ta kashe kudi wurin gyaran diyarta don gsky ina tausayama yusuf ko kuma ince yusuf zai shiga gidan alfarma????hmmm nayi shiru aunty zainab ta dawo ta hado kaya kam nagani na fada kowa ya gani sai ya kara kallo koda jamila tasamu lbrin irin lefen hawwa ai saida ganin kwaf dinta yasa mata ranar ta kasa bacci sbd tsakani da Allah sun zubda kudi kamar basu san ciwon su ba hankali tashe ta bar gidan umma sbd tsabar hassada.gidan yusuf dake barhin aka tsansarama hawwa kayanta wanda aikin Abbah ne wanda ya hana kowa yin komi yace shi ya dace yayi agsky gidan hawwa ya hadu kamar a turai komi nata lemon green an white sunyi kyau sosai hidima tazo yau saura kwana biyar haka yusuf ya matsama mami don Allah su taho haka nan sbda akwai abokaninsa a zasuzo da sukayi krtu daga indian zasu fara programm haka mami ta tattaro iyalanta helux biyu sukayo zuwa katsina ta dikko dakin kara kunya gareku ba dai tsoro ba????koda suka iso gida ya fara cika ita kanta umma mamakin canzawar diyarta tayi masha Allah kawai take fadi tare da gdyr Allah da ya ba danta wannan mata kowa yaba kyauwun da hawwa tayi yakeyi lkcin da suka iso yusuf nacan dashi da umar suna busy bai samu shigowa gida ba sai da yamma likis kuma gida ga mutane dole ta baya ya shiga ya nufi part din shi yana shiga ya nufi bedroom dinsa sai yaji kamar motsi cikin sauri ya karasa tare da bude kofar daga ita sai towel daure jikinta ganin mutun yasa ta saki wata irin karaaa!wadda saida shikanshi yayi saurin juyawa a sukwane ya rufe kofar gammm!!!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button