TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Wannan page din naku ne kuyi yanda kuke so dashi mum iliham shatuu tare sis shamsiyya Allah ya bar zumunci????
Masha Allah ku biyoni frns inayin ku walhi takuce sa’ar mataaaaa ????????????????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com.
Page 16
……….cikin sauri ya juya tabbas hawwa ce amma me takeyi haka a dakinsa dama yana mamakin ganin part dinsa bude amma bai tantance ba saida ya ganta, dawowa yayi falon ya zauna bisa kujera yana jiran yaga ikon Allah.hawwa komawar da yayi ya rufe kofar shine ya bata damar sanya key ta rufe kofar cikin tsananin tsoro tare da zama bisa gadon ta dauki turarukan da zatayi amfani da su ta cigaba da shafawa tare da humrar da zatayi amfani da ita.cikin fargaba da tsoro takeyin komi acikin ranta tana cewa dama bata biye ma su nafisa ba da suka bata shawarar zuwa part din shi ta shirya sbd mutane ko ina amma babu wanda yayi tunanin dawowar shi yanzu tunda ansan shi ba mai son hayaniya ba.zaune yake yana tunanin koma ya tashi ya tafi gidansu umar ne.amma bari ya jirata yaji me ya kawota ne?tana gamawa ta dauki rigarta ta sanya ta dauko hijabinta ta sanya ta hada komi nata ajakar data shigo da ita ta zura takalminta ahankali ta tako bakin kofar kamar munafuka haka ta sanya hannu ta murza key din kofar ya bude ganin shi datayi zaune a falo yasa jikinta kyarma cikin dauriya ta karasa fitowa batare data sake kallon inda yake ba shiko kallo daya yayimata yayi tasbihi ga Allah gaba daya yarinyar ta canza mashi tayi wani irin kyau ga jan lallen nan ya zanu ajikinta.rabawa tayi zata wuce shi batare datayi mashi mgn ba cikin sauri ya tashi ya rike mata hijabi saurin juyowa tayi tana kallonsa a tsorace murmushi yayi mai kayatarwa yace me kikeyi adakin mijinki?tmbyr tazo mata abazata cikin inda inda tace mutanene adaki na shiyasa naxo in yi wanka anan bansan zaka dawo yanzu ba amma kayi hkri.”sbd kinzo dakin mijinki kike bani hkri to amma hawwa ko ki kirani kice kin iso bakiyi ba, ta lura son janta yakeyi da magana “yaya ai ni tunda muka iso kaina ke ciwo bacci nayi yanzu ma tashi na kenan nazo nan.murmushi yayi” yasan fadi kawai tayi cikin hikima ya sakar mata hijabi sbd yaji yanayinsa ya fara canzawa ok shikenan yanzu kin gama komi kika fito ya tmbyeta saurin daga masa kai tayi alamar eh sbd a takure take sbd wani irin kallo daya keyi mata are u show?yasake tmbyrta?”yes tabashi amsa ok jeki sai na fito tom ta amsa tare da saurin fita daga dakin kallonta ya tsaya yi yana dariya kasa kasa don yaga yadda take hade step.
Tana fitowa ta yi wata ajiyar zuciya tare da gode ma Allah don gsky taji kunyar ganinta dayayi wai har yana cewa tazo dakin mijinta kai yaya yusuf shi baima jin komi haka yake sakin mgn ba ruwansa da wannan tunanin ta shiga part din su.bayan ya shiga kamshin daya rikita shi ajikinta shine a dakinsa kota ina wai yaushe littel ta canxa turarene haka masu dadi da kamshi lallai zan sha kamshi ya furta tare da nufar toleit don yin wanka shima ga magrib na shirin gabatowa wooow ya furta yanda yaji toleit din ya na tashin kamshi towel din datayi wanka ya dauko ya rike tare da rungume shi a kirjinsa yana wani lumshe ido kamar hawwa ce ya rungume hhhhh kaji su yusuf sabon shiga ????nidai fitowa nayi na bashi wuri don naga abun nashi sai a hankali????????????
Hidima akeyi ba kama hannun yaro ta ko ina yan uwa da abokanin arzuki suna ta fasowa ta ko ina hawwa sun gayyaci kawayensu inda da yawa sun halarci bikin nan yusuf ya kashe kowane party sai dinner kadai sbda yace walhi shidai yana kishin matarsa itama dinner sbd abokaninsa wadanda suka zi daga kasahe daban daban ne kada suga bai kyaut a masu ba shiyasa umar yace lallai yayi hakr ayita amma anyi walima tsakanin mata kadai kuma abun yayi kyau sosai gwanin ban sha’awa anyi wa’azi akan zaman takewar aure kuma da nasihohi sosai abun dai masha Allah.rana bata karya saidai uwar diya taji kunya ayau ne aka daura auren yusuf Bello mado da amaryarsa hauwa’u Bashir mado haka speaker babban masallacin dake GRA ta gauraye da fadi an daura auren akan sadaki mafi karanci naira dubu hamsin wanda Alh bello ne ya biya kowa yaji dadin hakan duk da suna da kudi amma basu nuna alfahari ba.to fah yaufa yusuf baki bai rufuwa yasamu abunda yake so tun tana karama me zaiyi banda gdyr ubangiji bayan angama daurin aure ne suka wuce hotel din da bakin su suke domin yin resption.
Biki kam yayi ashe da dangi muka kuriii????????????gidan Alh Bashir babu masaka tsinke cike yake haka gidan Alh Bello mutanen kankiya sun cika shi kai sai inda kake so zaka zauna su nabila da nafisa kuwa basa ma ganuwa haka aunty zainab ga aunty Rabi atu ta kano autarsu Abba kowa yana cikin farin ciki in ka cire hjy mariya sbd tana cikin hdimar amma ta ciki na ciki hakama jamila sbd hjy mariya tace ta saki jikinta itama lkc kadan ne indai yusuf ne a hannunta yake shiyasa ta fita ta warware ta shiga anayin komi da ita amma kasan ranta kamar ta kashe hawwa ta huta takeji.ummah kam cikin ranta fes alkawarin Allah ya cika Addu’a kadai takeyi dftn zaman lfy atsakanin yaran nata mami kuwa har kuka tayi sbd farin ciki.tun ranar da suka hadu a part din yusuf bai kara sanyata ido ba sbd gaba daya barin gidan yayi shima umar barin gida yayi suka koma hotel da abokansu kasan cewar ba kamun kai jamila take dashi ba takan zo hotel din wurin wasu data sani da sukayi karatu tare kuma ko don tazo taga yusuf ko bazai kulata ba shiko kamar ya shaketa yakeji yana tir da hali irin nata, haka nan taji tana son jin muryar yayan nata cikin sanyin jiki tace “nabila dauko mani wayata ki kunna mani nasan yaya fushi yakeyi dani tunda na kashe wayar nan murmushi nabila tayi ” tace kyaji dashi yarinya idan ma zaki cire kunyar nan ki rike mijinki hannu biyu biyu to tun wuri kisan abunyi don akwai kuraye ta karashe maganar tana dariya tare da dauko mata wayar tana mika mata.amsa tayi ta bude wayar batare da tunanin komi ba ta danna kiran yaya yusuf .yasanya wayar caji a falon dakin daya ke ya shiga yayi alwalla ita kuma shigowarta kenan zata shiga wurin frnd dinta ta lura da wayar yusuf na neman agaji cikin sauri ta duba screen din wayar my angel taga ni yana yawo tabbas hawwa ce murmushin mugunta tayi ta daga wayar hawwa sallama tayi cikin sanyi murya.murmushi jamila tayi”tace to ke banda abunki tunda kinyi nasarar auren shi mu kuma ai sai ki barmu mu huta dashi kafin mu mika maki sauran.cikin tashin hankali tasaki wayar kasa gaba daya ta tarwatse shikuma daidai da fitowarsa yana gyara hannun rigarsa ya jamila rike da wayarsa tana kallon wayar tana murmushi mai hade da mugunta.????
Masha Allah Aunty uwani ina gdy sosai Allah ya bar zumunci???????????? masoyan littafin TUN INA KARAMA ina ma kowa ftn Alkairi ngd sosai da kauna????????????????????ku biyoni page na gaba takuce sa’ar mataaa????????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 17
……….cikin azama ya karasa wurinta tare da fisge wayarsa a hannun jamila wani mugun kallo yayi mata wanda sai da zuciyarta ta buga sbd tsoro amma cikin dakewa ta ce masa”daga na taimaka na amsa maka ma shine zaka wani karya mani hannu, “uban wa yace ki daga mani waya?yusuf ya tmbyta cikin tsawa da hasala ke dai walhi baki da hankali baki san ciwon kanki ba am last waning kika kara shiga hurumin da ba naki ba sai na ci ubanki nonsens fita yayi batare da ya kara saurarar ta ba.cikin jin zafin abun ta juya itama ta bar wurin.yana fita ya duba yaga angel ce ta kira cikin sauri ya dalling number ta amma swittch up ya kira yakai sau biyar amma shiru mamaki yakeye Allah yasa ba wani mummunan abu ta fada ma littel ba haka ya kara sa masallaci yayi sallah.nabila cikin sauri ta kara so wurin hawwa tana tmbyrta lfy me yasamu yaya?zubewa kasa tayi batare da tace komi ba hawaye ne kawai ke zuba a idonta matsawa nabila tayi tana girgizata hawwa gaya mani don Allah me ya faru kallon nabila hawwa takeyi cikin kuka ” hawwa tace nabila yaya ya cuceni ashe yana da yan mata awaje wadanda ya ajiye yanzu cikinsu ne wata ta daga wayarsa bata boye mata komi ba ta fada mata cikin rashin fahimta nabila ta bude baki zatayi mgn wayar nabilace tayi kara gaba dayansu dubansu yakai ga screen din wayar sunan yayane ya baiyyana a wayar nabila.cikin sauri ta daga tare da sallama bai tsaya amsa gaisuwarta ba ya tmby ina littel?”yaya ban san ya akayi wata ta dauki wayarka ba ta fada mata mgn gashi can kuka takeyi kuma ta jefar da wayarta ta fashe.abunda yake zargi ya tabbata “cikin damuwa ya ce walhi nabila caji nasanya na shiga inyi alwalla jamila ta daga mani waya kuma ke kin san jamila bata da hankali .” nabila cikin mamaki tace aunty jamila?tabbas zata iya amma menene ribarta in tayi haka?katse mata tunani yayi da cewa ki hadani da hawwa, to yaya ta amsa tare da mika ma hawwa wayar wadda tunda suka fara mgn take saurarensu amsa tayi tare da sake fashewa da kuka bata yi mgn ba shikam jin kukanta yakeyi tamkar saukar wuta a zuciyarsa cikin damuwa yace littel nima kukan kiso inyi ne?”ya tmbyt cikin rauni girgiza masa kai tayi kamar yana kallonta ya cigaba da cewa don Allah littel kiyi hkr walhi ban san komi ba shirin jamila ne kuma walhi zanyi maganinta plsss my sweety nah kada kowa yaji wannan mgnr ku barta daga ke sai nabila plssss ya kara she mgn cikin sanyi murya “cikin damuwa tace ni yaya ban san me nayi ma aunty jamila ba ta tsane ni haka?amma ya dace ta fada mani wannan mgnr me nayi mata?ta kara she mgn cikin yanayin damuwa harga Allah baya jin zai kyale jamila sai ya wulakanta ta kamar yadda taso ruguza mashi farin cikin sa na yau amma zai rama shima haka yaci gaba da lallashin matarsa har hankalinta ya kwanta sannan yace mata ta fadu irin wayar datake so ya kawo mata ” cikin jin kunya ta ce duk wadda ka saya mani inaso yayana.”cikin jin dadi yace kin yarda da choice dina kenan?”yes ur choice is my choice my dear husband tsunkulin kansa yayi wai ko mafarkine yakeyi kafin ya kara mgn yaji dif an kashe wayar.bin wayar yayi da kallo yana smile, ita ko dariya takeyi nabila ma dariya takeyi suka rungume juna nabila na jin dadin yanda hawwa take daukar shawararta akan lkc kuma tana tir da halin yayarta na son zuciya.