TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Haka suka warware babu wanda yasan abunda ya faru tsakanin su .suka gyara jikin su suka fito wurin kawayensu cikin jin dadi.haka shima yusuf yaji dadin yanda littel ta fahimce shi kuma ta yafe masa iluv her ya furta tare da fita daga cikin motar tunda dama ya yanke shawarar zuwa gidan ne idan har hawwa bata fahimce shi ba to ya gode ma Allah da shedancin wannan makirar baiyi tasiri akan su ba Allah ka shiga tsakaninmu da ita nima Amin nace yusuf????haka abubuwa suka kasance har dare karfe 7:30 motocin kai amarya sun cika unguwa hawwa ta sha kwaliya da wani less sky blue komi na jikinta sky blue ne abunka ga farar fata abun sai wanda ya gani.gAmin????kya suna falon Abba aunty zainab ce rike da hawwa ummah na zaune kusa da Abba sai mami dake gefe sai hjy kaka da itama tana kusa da Abba yusuf ne jikinta sai aunty rabi atu da itama tana wurin hakika yau naji abunda ya girgizani na bani tarihin rayuwata ashe mamice mahaifiyata ummah mahaifyar yusuf gsky na shiga rudani asheni marainiyace wanda ban taba sanin maraici ba gsky ina jinjina ma Abbah da ummah da yan uwan mami da ita kanta mami shima kuma yusuf ya cancanci a yaba masa kuka nakeyi wanda babu mai iya tsaida mani shi ashe pic din danke gani adakin ummah shine mahaifina Alh mansir kanin ummah da akace ya rasu?tashi nayi na fada jikin ummah ina kuka mai tsuma xuciya wanda kowa na wurin saida y share kwalla.Abbah ne yayi gyaran murya yace to haka Allah ke nashi ikon don haka kai yusuf ban baka aure ba don kana nawa a a cancanta na gani walhi da baka can canta ba ni zan nemo mata mijin da ya dace da ita amma tunda Allah ya hada kanku bani da bakin gode masa ina maku ftn Alkairi tare da zaman lfy da hkr da juna ka rike amanar da Allah ya baka kuma ka tausaya mata amatsayinka na shugaba sbda kowa yazama sheda bazan raga maka ba natsawar zaka cutar da matarka.”Abba yace zo nan littel cikin rashin kwari hawwa ta matsa kusa da Abba ya kama hannunta yace ma yusuf taso nan shima ya taso kusa dashi kanshi na kasa Abba ya kama hannunsa ya hada dana hawwa yana murmushinsu na manya yace ma yusuf rike matarka ina maku ftn mutuwa ce zata rabaku gaba daya dakin ya amsa da Amin????haka yusuf ya rike hawwa gam kamar za’a kwace mashi ita haka kowa ya mike muka fito ina kuka kamar raina zai fita ga rabuwa da ummah tayi mani daci wannan shine dalilin aurena da yaya yusuf
Bayan ankai ni gidansa dake barhin wanda ya tsaru yayi kyau sosai haka daga nan muka shirya zuwa wuri dinner wadda umar ne ya shirya komi su kansu kayan xuwa wurin dinner ya sha banban da namu na nan don komi daga india aka kawu mana kayan da zamu sanya wurin jamila bata san da wannan shirin ba hankalinta ya tashi sosai ganin wannan shirin namu duk sai ta raina kanta mune karshen tafiya umar ne zai kaimu daga ni sai yaya sai umar da ke jan motar zaune muke abaya hannuna cikin nashi yake rada mani akunnena wai idan munje don Allah bai son inshiga da kunyata in ajiyeta baki kofar mota kafin in fita murmushi kawai nakeyi duk abunda mukeyi umar na kallon mu ta madubi dariya kawai yakeyi har suka isa hall din dai bakin kafar yayi parking da sauri ya bude ya fito ya zagayo ya bude masu kofa kama hannunta yayi suka fito tare ai aka shinfida kafet tunda ga wurin motar har zuwa ciki ga masu binsu da flower suna watsa masu ga kida na tashi abun gwanin ban sha awa haka suka isa har wurin da nasu ne na musamman wapre table suna zama kowa ya zauna sai tafi rab rab rab ke tashi nan da nan mc ya fara jawabi babu wanda amarya da ango basu birge ba haka aka kira babbar kawar amarya tabada tarihin amarya wanda kowa sai da yayi dariya haka nabila ta koma ta zauna aka kira umar shima yayi bayanin ango wanda duk mgnr da sukeyi da turanci sukeyinta sbd abokansu da basa jin hausa haka mc ya kira amarya da ango suka shigo fili haba dan da na wuri y kaure da ihu ana tafi umar kuwa tunda ya balle dolars zuba masu kawai yakeyi haka sauran abokanin su suma dolars ce kawai ke yawo wurin cikin hikima jamila ta shiga filin ta fara zuba nata kudin akan amarya da ango da dabara ta kama rigar hawwa tasa reza ta jata ai ko nan da nan bayanta ya baiyyana umar ne kadai yaga abunda tayi cikin azama ya iso ya rike hannun jamila jikake fas fas fas ya dauke jamila da mari jin karar marin sai hankalin mutane ya dawo gare su.
Masha Allah gdy nake kawata sibara madugu present☝️tace masoyan Tun ina karama ina gdy Allah yabar zumunci
Ku biyoni next page daga nan har ranar monday in Allah ya kaimu.taku ce sa’ar mataaaaaa????????????????????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 18
……….kowa ya juya yaga mai ke faru jin karar wannan mari da mutane suka ji “afusace umar yake nunata da yatsa yace kibar wurin nan tun kafin insa a fitar mani dake ummi dake kusa dashi ya jawo gyalen dake jikinta ya mika ma hawwa yace sanya sbd ita tariga taji abunda ya faru da ita jikinta rawa kawai ya keyi yusuf kuwa mutuwar tsaye ya yi sbda ya fahimci komi jamila dafe fuskarta tayi zata bar wurin hankali tashe cikin azama nabila ta jawo gyalenta fuskarta hawaye na zuba a idonta ” tace aunty jamila baki ji kunya ba kina jayayya da abunda Allah ya kaddara?agsky ke muguwa ce bayan sharrin da kika hada dazun yanzu kuma kin zo da wani cikin takaici nabila ta girgiza kai tace kaicho da kika zama yar uwata ta jini amma walhi baki iya raba hawwa da yaya yusuf duk makircin ki “umar ne ya jawo nabila yace mata kyaleta sis cikin baki ciki ta sake ta tana kukan takaici ” umar ce ma yusuf ya bar wurin da hawwa shi takaici ma ya hana shi cewa komi ita ko hawwa hankalinta yayi mummunan tashi hannun ta ya kama batare da yace komi ba suka bar wurin mutane da ba kowa ya fahimci komi ba kowa sai ya koma hidimarsa yasu yasu ne kawai suka san abunda ya faru cikin family din
yusuf na fita daga hall din wurin motar da suka zo da ita ya nufa ya bude ya zaunar da hawwa wadda ta zama kamar wata status sbd mamakin jamila yana shiga ya tada motar batare da ya tsaya sauraren komi ba ita ko hawwa tana shiga motar taji wani kuka yazo mata wanda tun dazun take son yinshi amma yaki zuwa bai ce mata komi ba sbd iyakar bacin ran dake zuciyarsa yayi yawa shima da zai samu yayi kukan wata kila daya samu sauki aransa.
Har suka isa gidansa na barhin babu abunda hawwa takeyi in ba kuka ba koda suka isa parking yayi ya jingina kanshi da kujera yana tunanin jahilci irin na jamila gata da ilimi amma bata amfani dashi wai me take nufi da nine soyayyace nace mata bana iya tunda tazo mani da bukatar ta amma shine take ta bina da sharri jamila kinyi kuskure ban taba jin sonki ba koda kuwa na second daya ne nisawa yayi yasa hannun shi ya dago hawwa cikin damuwa yace”littel da zaki daure ki bar kukan nan da zan samu sauki araina fadawa tayi jikinsa shikuma bai saurari komi ba ya rungumeta tsam ajikinsa yana sauke numfashi sama sama cikin kuka da shagwaba tace “yaya jamila sonka takeyi zata iya kasheni sbda kai don haka ina jin tsoron ranar da zata samu galabar rabamu, saurin rufe mata baki yayi yana cewa hawwa tunda har kinsan tana sona to me zai hana ki kama mijinki da kyau yanda bata da hanyar samuna kamar yadda ni nasani saitin zuciyarsa ya dafe yace” kinga nan babu sauran wani sauran fili a cikinta son naki ne kaunar taki ce soyayyar ma taki ce ai ban san lkcin da murmushi ya kubce mani ba “cikin shagwaba nace yanzu data yanka ni fa?cikin kulawa yace walhi nima da sai nayi mata kaca kaca abayanta hmm nace to Allah ma ya kyauta Amin yace.