TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

oho????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 22
……..koda yusuf ya fita daga gidansu gidansu umar ya nufa yana zuwa ya sami umar a bakin get din gidansu zai fita ganin shi ne yasa ya gyara parking din motarsa wanda dama fita zaiyi yana zuwa shima parking yayi kowa ya fito yana wlcming dan uwansa hannu suka mika ma junansu tare da sallama murmushi umar yayi yace”frnd gidan Abba zani yanzu nayi tunanin ko kana can?sosa keya yusuf yayi yace”daga can nake bros yanzuma zuwa nayi in sameka muje kankiya.”kankiya lfy umar ya tmby shi?”eh to lfy kam da sauki wannan karon hjy kakace kawai zata taimakeni “amma ai dazun mun fara mgnr da daddy kuma nasan zaiyi komi umar ya fada cikin kulawa.kayi hkr bros mu gani” hmmm walhi idan bazakaje ba ni inyi tafiyata yusuf ya fada cikin fushi!a’a yi hkr frnd ni na isa ince ban zuwa ai mu wuce na kira Ammi in sanar mata.kiran mai gadin yayi yace mashi ga key din motar nan zan fada ma nabila tazo ta shiga da ita gida.”to ranka shi dade adawo lfy “Amin ya amsa tare da bude kofar motar yusuf ya shiga suka dau hanya sai kankiya kan tsiyar katsina????
Ba wani lkc mai tsawo suka dauka ba suka isa kankiya, suna zuwa basu zame ko ina ba sai gidan hjy kaka suna zuwa mai gadi ya bude masu kofa suka shiga.bayan sunyi parking ne suka fito da fara’a suka gaishe da mal sale mai gadi cikin mutunci da mutun tawa.wucewa sukayi zuwa cikin gidan suna shiga da sallama cikin murna kaka ta amsa masu tare da cewa” yau kuma kun tuna da ni na ganku haka ko dariya dukayi gaba dayansu tare da zama yusuf yace”to ba ance kikoma birni ba kin ki kina nan kauye kina cin dawa da gero eh din ai ku baku da abinci sai shinkafa sai kayan kwalaye da gwan gwanaye umar yace da kina cinsu da yanzu kin kara girma.uwaka nace umaru yo ni Allah na tuba ai saidai akabari idan anayin girma ai kin ji ki menene kuma umaru my name is umar bashir mado kuma kema kin sani dariya sukayi gaba daya wanda shi yusuf har isa wurin da take ajiye furarta ya dauko ya fara sha.”oni yasu daga zuwa ba’a tmby sai kawai a dauke ma mutum abu akama sha kaga isuhu ka kiyayeni, ko kula ta baiyi ba umar ne yace ke kinyi baki amma baki basu ko ruw ba.to ai kunsan inda komi yake koni yar aikenku ce takara she mgn tanayi dariya
Kaini yanzu dai me ya kawoku?don da ganin wannan tafiya ba banza ba tunda dai dazun ai munyi waya da iyayenku kuma kowa lfy to amma ku me kuka zoyi?”yusuf yace walhi indai kina sona to ki ceto rayuwa ta sbd kowa so yake ya rabani da hawwa bai boye mata komi ba ya fada mata.cikin damuwa tace ai ni banga abunda yasa ka kyale jamila ba akan wannan aika aikan datayi sbd Allah umaru nasan da kaine da yanzu kaci ubanta Allah dai yayi wadaran mariya da ta lalata yarinyar nan shi kuma ubanta ba katabus agidan shi kai kuma da yake sakarai ne kaki daukar mataki to ai gashi nan sun rabaka da matar arzuki kai kuma ka kasa zama lfy.tunda ta fara fada babu wanda yace mata komi har ta gama.nisawa tayi tace suma ai basu kyauta ba tunda ai dai ba hawwa tace bata komawa dakinta ba ko?daga mata kai yayi alamar eh, “to kwantar da hankalinka babu wanda ya isa ya hanaka matarka murmushi yayi wanda yasa har yasa wushiryarsa ta bayyana cikin jin dadi yace shiyasa muke maki Addu’ar nisan kwana hmm haka dai zan barku nan dai suka ci gaba tattauna yanda zasu bullowa alamarin daga karshe dai tace masu su bari sai gobe su taho katsina tare.
Suna zaune afalo suna hira domin kaka har ta kwanta wayar yusuf ce tayi ringing ganin su nan my angel ne yasa ya daga wayar tare da tashi yana shigewa cikin bedroom.” Hello my heartbit ykk?”i’m fine cikin shagwaba kamar tana gabansa tace”nifa na kasa natsuwa banjika ba kuma banji ka dawo ba kuma umma da Abba banji sunyi mani wata mgn ba.murmushi yayi yace ai nace maki littel karki damu komi zai zo da sauki kedai ki bani nan d 24hrs insha Allahu dariya tayi har saida yaji sautinta tace ok my lovely husband cikin jin dadi yace kina ina ne,?hmmm ina nan kwance da kewarka to bari in kiraki video call dif ya kashe wayar murmushi tayi tare da kunna data tana hawa online yana kiranta dagawa tayi zaune take kan gado daga ita sai wata yar karamar riga ajikinta ganin juna dasukayi sai kowa hankalinsa ya tashi kusan minti biyu babu mgn can yusuf yayi karfin halin cewa littel anya zan iya hkr da rashinki don Allah ki tausaya mani bani da wani buri da ya wuce naki banso rayuwar mu ta kasance haka ba amma bana kara kuskuren danayi baya ya kara she mgn cikin juyayi”walhi yaya bana ganin laifinka tunda nasan burin dakayi ma wannan cikin.runtse idonshi yayi yace insha Allahu gobe zan kara ajiyata kuma walhi bazan kara sakaci akan cikina ba kunya ya bata ta rufe fuskarta haka suka dade suna waya amma bai nuna mata yana kankiya ba son surprised dinta yake so yayi bayan sun gama ne ya fito falo umar yace masoya kai nima dai dole inzo in matsama mami ta bani matata.zama yayi yace kaidai zauna nan kaji da gulmarka
Yana kwance ya fara bacci yaji karar wayarsa dauka yayi batare da ya duba mai kiran ba ya kara akunnensa ba sallama ba komi cikin fada”tace to na mamajo sarkin mata duk biya maka bukatar da najeyi amma baka kyale wannan yarinyar mai kama da zubin mayu walhi yusuf kaji kunya ka zauna kaita yi mata ciki.kafin ta cigaba da mgn yusuf yace ai bawai dadin mu amalar nake ji da ke ba kawai ina rage yawa ne ko kibani kanki ko kada ki bani nothing me “o haka kace ko to walhi yusus zaka san kayi dani walhi sai na rama kashe wayarsa yayi cikin bacin rai ya koma
Washegari gaba daya suka kama hanya komawa gida harda kaka suna isa katsina gidan su Abba suka nufa.mamaki ne ya cika Abba da yaga gansu tare da mahaifiyarsa itama umma haka ne cikin karfin hali kowa ke yin abunsa gaisheta sukayi sosai cikin girma mawa.bayan angama komi ne kowa ya natsu ta sanya aka kira mata Alh bello bayan kowa ya hadu ne a babban falon gidan anyi shiru aji abunda hajiyar kankiya zata fada ta bude baki zatayi mgn kenan, sai mgnar ta makale sakamakon jin jamila da sukayi tana cewa kaka kada ki shiga hurumin da ba naki ba gaba dayan su juya wa sukayi suna kallonta yanda take shigowa cikin falon cike da rashin kunya da wulakanci.
To fa meya kawo jamila kuma?????ya
zasu kare?hawwa zata koma kuwa?to wadannan amsoshin na cikin next page????
Bacci walhi ????kuyi manege da wannan sai Allah ya kaimu gobe ku biyo ni next page takuce sa’ar mataaaa????????????ina yinku masoyan Tun Ina karama Allah ya bar zumunci ????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 23
……..cikin mamaki gaba daya wanda ke falon suka juya don ganin jamila Abba aransa yace wannan wane irin bala’ine ke tun karar rayuwar yarana.kowa da tunanin da yakeyi aransa in ka fidda ni dana sume awurin, kara sowa tayi ta rike kugu cike da masifa.kafin ta fara mgn umar yayi karfin hali a hasale ya tashi yaje gabanta ya nunata da dan yatsa yace “cikin tsawa !!! kibi hanyar da kika fito ki koma inda kika fito tun kafin kiga kalar haukan nawa ke karamar mara kunyace amma rufin asirinki kada ki sake furta koda kalma daya agidan nan, fita kawai!yace tare da nuna mata kofa da hannunsa.tasan waye umar idan tayi sake yanzu zai jibgi banza babu kuma mai kwatarta haka ta juya cikin bakin cikin batayi abunda ya kawo ta ba tafita da sauri tare da banko masu kofar, kaka tace” yau naga abunda ya isheni ni hauwa’u yanzu nan isuhu haka kake zama da wannan shedaniyar yarinyar tanayin yanda taga dama?to tun wuri kasan cewa wannan ba matar mutunci bace ba dolene dije tace bazata baka diyarta ba.