TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Umar yace”ke kuma granny kada ki kara tunzura mana umma mana.hararar shi kuma tayi shikuma ya sunne kai yana dariya.
Daddy ne yace wannan lamari na jamila ya wuce tunanin kowa saidai Allah ya sawwake, suka amsa da Amin.kaka tace”to ai ni nan banga mata ba yazama dole kuba isuhu matar shi ta koma dakinta kallon hawwa tayi cike da tausayinta tace kiyi hkr takwara ki koma dakin mijinki kinsan komi na rayuwa kaddara ne to wannan ba abunda zaki rike azuciyarki bane ki kaddara haka Allah ya nufa.ke kuma dije bai kamata ki fushi da isuhu haka ba tsaka ninki dashi Addu’a ne Allah ya tsare maki shi daga sharrin wadannan mutane amma ki bar yarinya ta koma dakinta kinji ko?
“To hjy ai magn ta kare yanda kikace haka za’ayi banida wata jayayya Allah ya kyauta gaba.Amin yar albarka ” kaka tace Abba da daddy sunji dadin yanda umma take mutunta masu uwa gsky suna yabawa da halinta.Abba ne yace “to amma hjy kikara gargadinsa akan yazama namiji agidansa ya kuma tashi tsaye da Addu’a domin ita ce makamin mumini kada ya rinka sanya ma kanshi jamila zata iya mashi wani abu arayuwa yadai bar ma Allah kawai kuma tsaya da kafafunshi don mu kinga bazamu tsaya kullum muna mashi shara aba kuma babu mai cewa ya saki jamila don haka idan zata shiryu Allah ya shiryar da ita.
Amin suka amsa gaba daya sannan suka cigaba da tattaunawarsu ta uwa yaranta don umma dasu umar kowa ya bar falon hawwa da nabila ma sun koma daki.
Anan kaka take cewa ” nidai nafi tausayin nabila gaba daya bata biyo halin gidansu ba yanda kasan dije ta haifeta walhi.Abba yace”shiyasa nake tunanin hadata da umar hada baki sukayi da daddy da kaka wurin cewa masha Allah amma fa kayi tunani Alh karami dayake haka take kiransa”ai hjy nasan yar wurin mami ta kd bata da matsala tunda har munyi mgn da babanta ya nuna hakan daidai ne ko don a kubutar da yarinyar daga fitinar mariya don mun tabbatar ko mariya tana shakkar umar don shi kanshi uban abun yafara damun shi ya fara gajiya da halin mariya.daddy yace indai hakane to Allah ya fara taimakonsa.”ai shima gara ku hada mashi biyun yaje can yayita kaya.dariya sukayi tare da cewa suma zasu fita tashi sukayi tare da sallama suka fita
Umar ko yana can ya tasa yusuf agaba sai zolayarsa yakeyi tunda sun shirya meeting a satin amma yusuf yace ma umar cancelled sai next week don shi idan hawwa ta koma yau shida office sai next week????????
Jamila na fita rai bace bata zame ko ina ba sai gidansu wurin mummy tana shiga ko parking mai kyau batayi ba ta fito ta fada cikin gidan hankalinta a tashi ba sallama bakomi kawai sai kiran mum!mum!mummy!!!cikin sauri hjy mariya ta fito a firgice tana fadin lfy kike jamila aiko tana isa ta fada jikinta tare da fashewa da kuka cikin “tashin hankali take tmbyr diyar tata haka ta zauna tafadi mata korar karen da umar yayi mata da iyayensa basu ce komi ba.
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 24
………haka jamila ta gama zaiyyana mata komi.cikin bacin rai tace yanzu hjy batace komi ba walhi mum batace komi ba.”hmmm to ki barsu duk zanyi maganinsu share hawayenki ki tashi ki koma gidanki duk wani shiri nasu zan lalata shi dani suke mgn ai khadija ta gama da family dinmu gaba daya dama nasan ba banza ta bar hjyr mu ba amma ba komi tashi tafi nasan da sun gama shi yusuf din gida zaije to wannan hayakin ki kara yinshi lkcn da yazo hannunki idon shi ya rufe da bukatar ki sai kice bai isaba sai ya rubuta maki sakin yarinyar nan kinga dama ya fita hayyacin sa daya rubuta sai ki bashi hadin kai yayi abunda yake so daga nan bayan kun rabu sai ki kira mai gadinku ki aike shi ya kaima khadija kinga daga nan takare sbd rubutun shi ne bai isa yace ba haka ba.
Cikin murna da ihu jamila tace”mum wai dama kin ma san da wannan dabarar baki bani ita ba tuntuni na gama da rayuwata bari kigani mum sai kinji ni batare da tunanin komi ba ta figi gyalenta da key din mota tayi waje kallonta uwar takeyi har ta fita cikin jin dadi tana fita ta shiga motarta ta figeta a dari biyu sai barhin Allah ya kyauta jin kunya jamila????
Shikam yusuf bai bar office ba saida ya kammal komi sannan ya tashi maimakon ya wuce gida sai ya wuce gidansu domin kaka tace mashi ya dawo sukai mashi matarsa haka kuwa suka nufi gidansu Abba domin ta howa da hawwa.
Suko tun bayan tafiyarsu umma ta aika aka gyara ma hawwa part dinta don lkcn da jamila ta dawo taga motar nabila amma sai tace ita kuma wannan munafukar me tazo yi?aranta tasan dai bai wuce ta daukar mata wani abu tsaki tayi ta saki zancen tace duk zakuci uwarku daga yau kankanba ta kare dole abar mani gidana.
Haka taje ta shirya duk abunda uwarta ta shirya mata ta zauna zaman jiran zuwan mijinta????
Nabila basu bar gidan ba saida ta tabbatar komi need ko ina kamshi ne kala kala sannan suka fito suka rufe ko ina suna fitowa suka san ta dawo gidan babu wanda ya kalli part dinta haka suka wuce dama daga kaka Asabe sai wata makociyarsu bata ji fitowarsu ba sai jin tashin motar nabila ne yasa tayi saurin bude labulen window amma ha nabila ta cilla kan motarta bakin get don haka bata fahimci komi ba tsaki tayi takoma ta zauna tana fadin yar wahala kin koma cikin makiya wai ke mai gsky.
Koda su yusuf suka isa gidan su kaka cewa tayi sam bata yarda ba sai anyi magrib zasu tafi kuma dole umar yaje ya dauko mata Ammi don ba fara bace zasu maida kuma harda su Asabe da makwafta tunda dai kowa yasan bari tayi koda ba haihuwa bace tsaya sukayi suna kallon ikon Allah wurin kaka wai harda gayya to ya zaiyi dole ya lallaba ta ya amshi matarsa don yasan halin rudunta.
Dole umar yaje ya taho da Ammi yana bata lbrn yanda sukayi da kaka tana ta dariya hjy akwai rigima in taso.
Tunda aka gama mgn umma takira wata mai gyaran jiki suka shiga da hawwa part dinta ake aikin gyarata rana daya ne amma abun gwanin sha’awa
Haka aka gama shirya komi cikin tsari hawwa kuwa auren sake dawo mata sabo yayi anshiryata da wani kaya da aunty zainab ke saya mata cikin irin wanda aka ajiye mata na haihuwa saiga abunda ya faru wanda kowa baiji dadinsa ba.
Kyau kai idan ana ambatonsa to bata lkc ne wurin hawwa don tsakani da Allah ???? tasawace gaban mota????bayan umma da Ammi da kaka sun karayi masu nasiha mai ratsa jiki haka hawwa ta rike umma tana kuka Ammice tace ya isa haka nan hannunta ta kama suka fita zuwa su samu sauran mutane su tafi.kaka ma da bata da wuyar kuka share hawaye kawai takeyi.
Bayan sun fito ne mota biyu sukayi umar ya dauki su kaka da hawwa don kaka cewa tayi hawwa bata shiga motar yusuf saidai su shiga ta umar shiko yusuf cewa yayi aransa lfy zamu rabu tsohuwa ai ni kingama mani komi????????
Haka muka fito ba dadi araina don walhi umma uwace ko ni ta haifa ba yusuf iyakar soyayyar da zan samu kenan.haka muka isa gidan yusuf muna shiga get din naji faduwar gabana ta yawaita duk Addu’ar data zo bakina kira nake tare da tunanin mgnr nabila da tace dole sai na cire tsoron jamila zan zauna lfy nunawa zanyi ban ma santa ba da haka zan kwaci kaina wurinta da mijina tunda ita dai bata da kamun kai.