HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

 

 

Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing????????????takuce sa’ar mataaaa ????

TUN INA KARAMA ???????????????? ????????????????

 

By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!

 

 

Page 5

 

 

…….”tace hawwa kiyi tunanin zan saurara masu, kedai kawai ina son ki rike abunda na fada maki aranki.tana fadin haka ta juya har takai bakin kofa ta juyu, tace mani kuma daga yau na hanaki bin shi ya kaiki makaranta, yanzu ki tashi kije ki dauki key din motar ki idan kinada sauran lkc ki tafi, idan kuma lkc ya wuce to kiyi hakurin gobe idan Allah ya kaimu.kuma mota duk wace kike so a gidan nan ki hau ba sai wai taki ba kamar yadda kika sani ne baki da shamakin komi agidan nan.kuma ina so daga yau ki daina zubda hawayenki akan yusuf, ki daure ki cire shi aranki.duk dana san abun mai wahalane agareki amma yakamata kiyi tunani akai, ina fatan kin fahimceni.cikin dauriya amsa mata da insha Allahu ummatah.ina kallonta ta fita ta jamani kofar.ajiyar zuciya na sauke a hankali na furta ki gafarceni ummatah amma bazan iya cire yaya yusuf azuciyata ba.kamar yadda nasan shima bazai iyaba.zandai kiyaye dokokinki amma yaya yusuf jinin jikina ne.

 

 

Na share hawayen da suka zubo mani.”abangaren yusuf tuki ya keyi yana jin wani zafi a zuciyarsa, har ya isa office ranshi ba dadi, yana isa wani katon wuri dana ga an rubutu kamar haka Y.B. DISTRIBUTION COMPANY LIMITED… Ahankali naga ya isa bakin get din wurin yayi horn , cikin sauri naga an wangale get din wurin.ya tura hancin motarsa yana shiga ya nufi wurin yin parking ya park motar shi tare da budewa ya dauko breif case din shi da lapton din shi sai wayoyinsa.cikin hanzari naga wani mutum ya nufe shi yana fara’a yana cewa ranka shi dade barka da zuwa, yana kokarin amsar kayan dake hannunsa.cikin dan sakin fuska da babu walwala acikinta ya amsa masa tare da mika masa kayan dake hannunsa ya shige gaba shi kuma yana biye shi.har suka kai bakin office din mutane na gaishe shi saida suka isa yasa key yabude office din mal iro ya shiga ya ajiye mashi yakayan ya fito yana cewa atashi lfy yallabai.ya masa kofar.

 

 

Babu alamar wani datti a office din ko ina fes ga wani irin kamshi mai dadi dake tashi cikin office din.sbd gsky yusuf akwai tsafta ga son gayu gashi dama Allah ya bashi kira mai kyau kowace mace ta kalle shi to zata so ta mallake shi a matsayin mijin aurenta.in takaice maku dai yusuf handsome ne na bugawa ajarida ???? idan yayi murmushi wushiryarsa ta bayyana dimpul din shi ya lotsa ai kawai kamar ya dauwama ahaka.

 

 

Zama naga yayi akujerarsa ya fiddo wayarsa naga ya nemo wata no yana kira yana karawa akunnensa naji yace na iso ina office kasameni, banji mai akce ba saidai kawai naji yace ok sai kazo ya ajiye wayar ya fara duba file din dake ajiye kan table din sa, ba don yana jin dadin aikin ba sbd damuwace fal azuciyarsa.

 

 

…..jamila ta gama shirinta tsab na zuwa hospital wurin aikinta, saida tagama ta fito ta wuce sashen maigidan amma abun mamaki rufe ta ganshi hanyar fita tayi tafito daga cikin gidan tayi harabar gidan wajan parking amma bata ga motar shi ba.tsaki tayi tace to koma dai baya kwana gidan ne?ta dage kafadarta alamar ko oho” tace nasan yana wurin mayyar nan amma zanyi maganin shi mts yana can kamar wani rakumi yana bibiyarta.kwaf tayi ta nufi wurin motar ta ta sa key ta bude ta shiga tayi rivos ta nufi get mal isah na ganinta ta wangale mata get tazo daidai fita ta sauke gils, “mal yace barka da fitowa hjy ” cikin isa da jiji dakai tace barka dai yaushe mai gidan nan yafita ta jefo mashi tmbyr?”yace ai hjy zaikai awa biyu da fita batace komi ba ta rufe gilas din ta ja motarta ta fice rai bace, tunani takeyi yau sati guda kenan abunda yakeyi mata kenan, kuma in ya dawo baya yarda su hadu cikin yanayin damuwa ta furta:yusuf Bashir kankiya ka tabka babban kuskure!!!

 

 

Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? takuce sa’ar mataaaa ????

TUN INA KARAMA ????????????????????????????????

 

 

By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!

 

 

Page 6

 

 

…….Tunda umma ta daga dakina na tashi na shiga toleit na kara wanke fuskata na fito na tsaya gaban mirrow na dan gyara fuskata wadda dama bawani make up nakeyi mata ba.sbd dai dai gwargwado ni farace kuma ina da kyauna daidai missali Allah yayi mani hallita mai kyau sbd haka kullum nake kallon kaina ina gode ma Allah Alhmdulillah.

 

 

Ban canza shigata ba amma na dauki hijabi na sanya a maimakon gyalen dana sanya.sbd dama gaskiya idan zanyi driving to bana sanya gyale saidai hijabi dama don tare dashine nake wannan shigar, duk da shima baya son inayi don yusuf yanada kishi ba tun yanzu ba nasan hakan.tun kafin muyi aure yana hanani ire_iren wannan shigar.

 

 

Ina da lucture karfe 2:00 shiyasa nayi kokarin fita in shiga skul kafin lkcn ko don in dan rage ma kaina damuwar dake zuciyata.bude jakata nayi na dauko key din motata na rike ahannu na, nafito na rufe dakina na nufi dakin umma don banganta a falo ba, ina zuwa na murda kofar dakin tare da sallama na shiga.tana zaune tana waya na shiga sai naji tace ina zuwa mami zan kiraki bari in sallami diyata.kawai naga ta kashe wayar tare da amsa sallamata”tace hawwa har kin shirya tafiya zakiyi?na amsa da eh ummatah.ta sake kallona tace wai yauma kina azumin ne?nace inayi tace to yaushe zaki dawo?nace ummatah sai karfe 5:00 tace to Allah yabada sa’a adawo lfy.don Allah a kula nace insha Allahu.na juyo zan fita ta taso ta biyoni a baya tana cewa wace motar zaki hau?ina murmushi nace ummah tawa zan hau, tace to shikenan Allah ya tsare na amsa da Ameen, sai da ta rakoni

 

 

….har bakin motata na shiga da Addu’a abakina na waigo nace umma bye itama ta daga mani hannu tace bye bye adawo lfy, haka nayi ma motata key a lkcn har baba mai gadi ya bude mani get na isa bakin get din zan fita na sauke gilas dina na gaishe shi, shikuma yana yi mani Allah ya kiyaye haka na fita gidanmu na dauki hanyar skul ina tafiya cikin natsuwa da taka tsan tsan a hanya na kunna kira ar Ahamed suleman ina saurare ina jin wata natuwa na zo mani.kuma ina tunanin maganganun ummatah wanda sune fal araina.ina neman mafita awurin Allah.sbd ban san kowa ba sai yusuf babu wanda na saba da shi acikin dangi kamar shi haka awaje ma babu shi kadaine abun alfaharina kuma tamkar jinin jikina.wasu hawaye masu zafi suka zubo mani, ummatah idan kika rabani da shi wazan jawo arayuwatah TUN INA KARAMA.nake son shi tun ban san menene so ba tunanina yan uwanta ka ne ashe kaunace mai tsanani tsakaninmu dawannan tunanin na isa skul daidai get din skul din mu na UMARU MUSA YAR’ADU’A UNIVERSITY dake cikin garin katsina haka nasa sighnal din motata na shiga cikin skul din na nemi wurin da mukeyin parking na parka motata na fito na kulle na wuce block din class din mu inada nasa zamuyi lucture.

 

 

…..yusuf bai gama duba file din dake gabansa ba aka buga kofar office din shi batare daya daga kansa ba yace yes come in, umar ne ya bude kofar tare da sallama ya isa inda yusuf yake zaune ya mika mashi hannu suka gaisa.sannan ya nemi wuri ya zauna yace wlhi compaming din kayan nan ne tsaya yi amma komi normal in sha Allahu.yusuf yace ba ok ba damuwa umar yasake kallon yusuf yace frnd naga kamar you not feeling okey?yusuf ya dan ya mutsa fuska cike da damuwa .yace walhi umar umma bazata taba yarda dani ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button