TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

………ganin ya kashe wayar ne tayi sauri ta zira jallabiya da hijabi ta shiga bathroom ta wanke jinin da ya bata mata jiki ta fito da sauri rike da wayarta da tashi daidai shigowar umar shima nufarsa yayi inda yake kwance cikin jini don ya bugu sosai ca kumarsa yayi bai damu da jinin jikinsa ba yana girgiza shi yana cewa “bros walhi idan har wani abu ya sameka bazan bar jamila ba haka ya sungumi dan uwansa hankali tashe ya fito dashi zuwa mota itama hawwa ganin haka yasa ta bishi da gudu ta shiga motar gudu umar yakeyi har ya kawo Alheri hospital wanda dama shine asibitin families dinsu haka ya isa cikin tashin hankali dama yayi waya da doctor din yana isa suka nufi kansa suka dauke shi sai emagency nan da nan likitan yashiga duba shi tare sauran nurse din hakayayi nasarar cire masa kwalbar da tashige masa a goshi tare dayi masa dinki sbd ta huda shi wurin har yayi rami.
Haka dai aka gama mashi komi aka kaishi dakin hutu.likitan na fita su umar suka tashi suka nufo shi ” umar yace yaya doctor?murmushi yayi ya dafa kafadarsa yace” babu damuwa umar muje office haka suka bi doctor har office suna shiga ya nuna masu wurin zama suka zauna sannan doctor yace”bakomi umar yayi sa’a wuri dayane kwalbar ta shige sosai kuma an cireta anyi masa diki wanda dole ne yasamu hutu na wani lkc koda na sallameku kuma akwai magungunan da za’a nema zan rubuta maka su yanzu kuma idan yayi 3days zan kwance masa dinkin ana dressing din wurin, amma wai umar sister dinku kuwa she is very stupid tayaya zakiyi ma mijinki haka yanzu da da tsautsayi fa ta fasa mas kai ya mutu fa?umar ji yayi kar zuciyarsa zata fashe sbd takaici amma walhi idan zai ganta yanzu sai ya canza mata kamanni.murmushin yake yayi yace”nidai fatana kada wani abu yasamu bros.”ba komi insha Allahu amma u better ku dauki mataki don ba’a san abunda gaba zatayi ba, Allah ya kyauta Amin umar yace.ita ko hawwa banda tunanin irin hali irin na jamila babu abunda takeyi.haka likitan yace su bari sai nan da 1hrs zai sallame su daga nan ya rubuta maganin yace umar yaje y nemo su haka suka tafi da hawwa tare da kwantar mata da hankali.
Bayan sun gama komi doctor ya sallamesu tare cewa nan da kwana uku su dawo, haka sukayi masa gdy suka tafi.gaba daya motar babu mai magana sbd kowa da irin tunaninsa akan jamila haka suka isa gida mai gadi ya bude masu kofa tare dayi ma maigidan nasa Allah ya kyauta don yaji komi kuma shima yayi tir da halin jamila.
Suna yin parking hawwa ta fito ta bude masu gidan shi kuma umar ya kama yusuf suka shiga ciki yakai shi har part din hawwa sannan ya nuna ma hawwa yanda maganin yake sannan yace shi zai koma sai da safe dare yayi sosai “yusuf yace bros ngd Allah yabar zumunci.” ba komi umar yace Allah ya baka lfy sai na dawo da safen haka sukayi ban kwana hawwa ta biyo shi ta rufe gidan shi kuma ya shiga mota ya nufi gida cike da takaici aransa.
…….jamila ko na fita bata zame ko ina ba sai gidansu tana shiga tayi parking ta fito ta shiga cikin gidan bata zame ko ina ba sai part din hjy mariya tana shiga ta sameta sai hada mata magungunan takeyi cikin tashin hankali tace mummy na fasa masa kai.cikin tsoro tace”garin yaya jamila!zakiyi wannan danyen aikin?walhi mummy hanani fitowa yayi shine nima na aikata hakan, “kash!amma ke banza ce to yanzu ai kin lalata komi sai ki zauna mu nemi mafita zuwa safe, ” ai dole mummy daddy dai bashi nan ko?don shima yanzu naga kamar ya fara bin bayansu Abban yusuf.”ke don Allah kyale shi can da munafurcin su kije ki kwanta bashi gari “to mum ngd.
Hawwa na dawowa wurin yusuf ta zauna tace” yaya bari in hada maka tea kasha kafin kasha magani ko, ta tmbye shi cikin damuwa tausayinta nae fal aranshi yarinya karama amma ana sanya mata damuwa da yawa why ya tmby a zuciyarsa, azahiri kuma murmushi yayi yace”duk yanda kike so sweet heat zanyi, murmushi tayi tace to hak ya kamata tashi tayi ta wuce kitchen ta sanya mashi ruwan zafi tare da warming din kazar da suka zo dashi don su duka babu wanda yaci komi in banda cinye juna da sukayi wanda yasa har jamila tayi masu wannan rashin mutunci.
Haka tayi komi ta dawo ta zauna kusa dashi tana bashi tea din yana sha ita kuma tana ci kadan don ita kanta komi ya fita aranta amma bata so taga yanada damuwa aransa ita dai fatan ta Allah ya bashi lfy kafin tace komi.bayan ta gama ne ta taimaka mashi ya shiga bathroom yayi wanka tare suka gama komi suka fito haka ta shirya shi cikin kayan baccinsa saida ta tabbatar ya kwanta sannan itama ta hau bisa gadon ta kwanta tare da rungume shi ta baya juyowa yayi yana mamakin yanda ta canza duk wannan kunyar ta ta ta cireta shima murmushin jin dadi yayi ya kara rungume abinsa ko ba komi ya samu natsuwa aransa.sai muce Asuba ta gari masoyan juna????
……washegari da safe bayan sun gama komi ta bashi magani suna zaune a falo tayi pillow da cinyarsa shi kuma yana wasa da kalabar dake kanta shi kansa wani dadi yakeji aransa yanda yaga bata damu da abunda ya faru ba bare ta tmbye sa me ya faru tsakaninsa da matarsa.ba zato taji yace”littel amma ina ftn babu wanda yasan me ya faru ina nufin su umma.dariya tayi tace”babu wanda yasani, “gud house wife haka ake so mace ta rinka rike sirrin cikin gidanta kuma kada ki damu da abinda jamila takeyi with time kinji ko?” Naji yayana kuma insha Allahu zanyi yanda kace”Allah yayi maki Albarka “Amin dear ta amsa masa tare da kara shigewa jikinsa.
Basu dade ba umar ya shigo duba shi hawwa bayan sun gaisa ne ta tashi taje ta kawo ma shi lemu da ruwa.yusuf ne yace” frnd ina so ka rakani in maido da jamila.cikin razana umar ya mike tsaye yana nuna shi d ya tsa zaiyi mgn sukaji faduwar tiren da hawwa ta dauko da lemu da glass cup din data dauko suka fadi kasa suka fashe sbd jin furucin da hawwa taji yusuf yayi na zuwa dawo da jamila.gaba daya suka juya tare da ganin hawwa bata tsaya ba sauraren komi ba ta juya da gudu tana kuka!!!????
Masha Allah kuyi hkr na rashin jina kwana biyu walhi na zama busy ne amma duk da haka zaku rinka jina akai kai iluv u fans ????
Din Tun Ina Karama ina maku ftn Alkairi irin sosai din nan ????????????
Mu hadu a next page takuce sa’ar mataaaa????????????????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 27
……..tana shiga daki tasa key ta fada kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yusuf binta yayi a kidime yana kiran sunanta amma yana isa kofar yaji ta sanya key, komawa yayi wurin umar wanda tunda yazama kamar an dasa shi sbd mamaki yazama kamar status.
“Kaga irin abunda nake nuna maka yusuf, yanzu ace kai bazaka iya hkr da jamila ba sbd sun gama dakai sun maida ka wani wawa sbd da Allah kanayi ma yarinyar nan adalci kuwa?gsky yusuf zan fidda hannuna akan wannan badakala taku don bazai yiwu ba kullum problem’s yaki karewa tsakaninku kai kuma kullum kalmarka bata wuce revenge zakayi taking ba kuma har yanzu kaki gamawa da al’amarin ba.” Umar kasan bazan boye maka komi ba arayuwata ba to walhi ban taba son jamila koda da second daya ne idan ba don asiri ba kuma gaba daya mun san haka to jamila tayi mani abubuwa da yawa arayuwa infact ma ince maka ban taba samun mutumin da ya musguna mani ba arayuwa irin jamila idan har na rabu da jamila salun alun to gsky banyi abunda ya dace ba amma ina so in nuna ma jamila ita bata isa ba arayuwa duk abunda take takama da shi ina so in raba ta dashi in nuna mata ita bata isa ba kuma bazata iya samun digo araina ba na soyayyarta kuma ina so duniya tayi mata kunci, ina so in azabtar da rayuwarta har sai ta wulakanta sannan inyi mata mai gaba daya zan dasa mata ciwo a zuciyarta wanda har ta mutu bazata daina jin sa ba.amma hakan bazata samu ba har sai mun zama clothenings da ita don haka ina so ku bani lkc ku fahimce ni babu komi araina intentionally nayi mgnr nan dama ina so hawwa taji don inga reaction dinta kuma nagani zanyi handle din komi ya kara she mgn yana kallon umar sosai.