TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

…….ajiyar zuciya umar ya sauke tare da jinjina kai alamar gamsuwa “to amma yusuf taya ita hawwa zata tabbatar ba sonta kake ba?” Yes ina so hawwa ta kwaci kanta wurin jamila tacire tsoron da takeyi mata arai kamar yadda nabila ta bata shawara kuma naga ta dau hanyar yin hakan, kuma ina so ita jamila tasan hawwa ita kadaice macen da nake so a zuciyata duk da ta kasa gane hakan har yanzu zan bita akan asirinta na ta siri har sai nakai inada zamu fara game din daga nan zata fadi kasa warwars daga ita har uwarta.”to shikenan amma u have very careful about her “insha Allahu frnd.” Amma ba yau ba kaje ka lallashi littel.”hmm walhi umar tunda ta kulle daki bazata saurareni yanzu ba “to yanzu kasan ya zamuyi?” Ban sani ba umar.”nabila zan kira tace mata zata zo yanzu na tabbatar bazata cigaba da fushin ba har kasamu ka fahimtar da ita komi cikin hikima.”gud idea frnd.
Koda umar ya kira nabila ya fadi mata ga abunda yake so tayi ta amsa da to kuma bata kawo komi aranta ba sannan yace mata bai so abarta ita kadaine tunda zasu fita da yusuf ne, koda nabila ta fada ma umma sakon umar na zuwanta gidan hawwa bata hanata ba don itama tasan hawwa tana bukatar wani kusa da ita tunda jiya ta koma.umma tace ma nabila idan kin shirya ki tafi a motar hawwa sbd abar mata abunta can nasan ai kun kusa komawa skul?”haka ne umma zan tafi da ita dama key din yana hannuna.”to shikenan agaisheta amma kada kiyi dare umar ya maido ki gida “to umma ngd.kiran hawwa tayi kamar yadda umar yace ta sanar mata zuwanta hawwa tana da son boye tsakaninta da yusuf shiyasa koda nabila ta kirata bata daga ba saida ta saita kanta sosai sannan ta kirata kuma ita kanta nabila bata fahimci komi ba.
Suna gama samun mafita umar yace su fita kada ma tasame su haka suka fito shi yusuf ga plistar agoshi gidan su umar suka wuce direct suka nufi sashin umar batare da sun yarda Ammi ta gansu ba bare ta tmby me yasamu yusuf din.
Ita ko jamila tana gida gabanta na faduwa tana tunanin ya zatayi idan kuma an samu wata matsala tsakaninsu amma tayi mamakin yanda har yanzu bataji wani feed back ba kuma tayi tunanin ko hawwa zata fadi ma umar komi kuma shima tasan daya sani da yanzu yazo yayi mata hauka amma bari takara sauraren su iyaka kawai tace masu bada niyya tayi ba tsautsayine kawai tana wannan tunanin ne mummy ta shigo dakin suka ci gaba da kullawa suna kwance wa.
……….nabila data zo wurin hawwa bata fahimci komi ba don bata son daga dawowarta tace ga matsala tana so ta fahimci abunda yusuf yake nufi da zaman su, haka suka sha firarsu kamar bata da wata damuwa koda nabila ta tmby ta aunty jamila cewa tayi ta fita hospital tunda ta na tunanin kamar afternoon takeyi haka suka bar mgnr batare da tunanin komi ba azuciyar nabila.
……….su umar basu dawo ba sai karfe 4:30 suna zuwa suka iske hawwa kamar ba abunda ya faru tsakaninsu koda nabila ta tmbyai hawwa me yasamu yaya a goshi cewa tayi koface ta buge shi yayi rauni Allah ma ya kiyaye.umar najin yanda hawwa take kare mijinta azuciyarsa yace lallai yusuf Allah ya baka yar aljannar mata haka nabila ta jajanta masu sukayi sallama suka rako su har bakin mota suka tafi wurin motar ta ta wuce inda nabila tayi mata parking.binta yayi da kallo don ita ko sake kallonshi batayi ba tunda su nabila suka fita budewa tayi ta dauki abunda zata dauka ta rufe bata saurare shi ba ta nufi hanyar shiga cikin gidan binta yayi abaya tana shiga tayi hanyar part dinta cikin sauri ya isa gareta ya rike mata hannu juyowa tayi kafin yayi mgn ta daga masa hannu dakata yusuf !!!!!!cikin razana ya bita da kallo don ko da wasa bai taba jin ta kira shi agaban shi ba kai tsaye ????
Haka ya tsaya yana kallonta ????????????????????ran mata ya baci ????to yusuf ya ake ciki????
Masha Allah ina maku ftn Alkairi masoyan Tun ina karama ngd da kauna da kulawarku.
Ku biyoni next page takuce sa’ar mataaaaa ????????????????????????
TUN INA KARAMA????????????????????????????????
©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
Page 28
……….mamaki ne ya hana yusuf magana sbd yanda yaga tashin hankali a fuskar hawwa karara, juyawa tayi ta barshi wurin yana tsaye haka ya ganta ta shige part dinta ta rufe.murmushi yayi cikin ransa yace hawwa a hankali zaki fahimceni zakuma ki san ke kadaice araina.azahiri kuma girgiza kai kawai yayi ya shige part din shi shima batare da ya kara binta ba.
Hawwa na shiga daki fashewa tayi da kuka tana cewa meyasa nayi sabo da soyayyarsa dama abunda umma ke gani kenan taso rabamu?gsky bazan iya ganin wannan rashin hankalin ba ace wai mace ta so hallaka ka amma kana cewa zakaje ka dawo da ita alhali ita ko bin ta kanka batayi ba anya akwai adalci cikin wannan rayuwa kuma kace wai kada afada ma kowa, to me kake nufi ne?haka tai tayin tunaninta wanda babu amsa cikinsa hardai ta tashi tayi wanka tayi sallah.bata iya cin komi shiyasa ta dan sha tea kawai ta kwanta shima sakamakon tana da ulcer kada ta samu matsala yasa ta sha.
A bangaren yusuf kuma shima hakan take saida ya gama komi zai kwanta ya tuna da umar cewa yayi bazasu je gidan su jamila ba yadai kirata awaya yace ta dawo.haka ya dauki waya bayan ya gama komi ya kira jamila, zaune take tana chatting awaya kiran shi ya shigo wayarta cikin tsoro da fargaba take kallon kiran har ya katse.tsaki yayi ya kara kira har ta kusa katsewa ta daga cikin karfin hali,”hello tace kafin ta kara mgn yace”come back ur home right now!kafin ta sake mgn taji dif ya kashe wayarsa, cikin mamaki da jin dadi tayi ihu wanda har saida mummy tayo dakin da gudu tana fadin “lfy jamila???
…….” Mummy yusuf ne ya kirani wai in dawo gidan yanzu ta fada tare da rungume mummy cikin jin dadi mummy tace “amma fa ya shammace mu amma ba komi tunda dama mun gama komi kawai ki maza ki shirya ki tafi kinsan ance da zafizafi akan bugi karfe ” gsky ne mummy bari kawai in tashi to yi sauri kinga 8:30 tayi kije can ki kara shiryawa kinde ji bayanin danayi maki ko?”eh mummy naji amma kinsan nayi mamakin da abunda nayi masa kuma banji ya fada mani komi ba harda wannan dan kazagin nashi banji komi ba.hhh ke wai an gaya maki mu na wasa ne har yanzu ke yarinya ce ai an riga angama komi ke dai tashi dama inata tunanin munyi waya da daddy dinki yace gobe zai dawo dama kada ya dawo ya sameki kuma ya fara fada amma naji dadi tunda anyi haka kuma koda kinje ki kwantar da hankalinki ki bashi hkr kinga dai alamar yana sonki ko?”gsky ne mummy bari ki gani”tasahi tayi ta shiga cikin bathroom ita kuma mummy ta fita don ta fiddo mata komi cikin sauri ta gama komi ta fito ta shiga part din mummy haka suka fito mummy tayi mata rakiya har gaban motarta tare da fada mata yanda ya kamata tayi komi haka ta tashi motarta mai gadi naganin haka yace”ga matsiyaciyar nan bari in bude kafin tayi mani rashin mutunci haka ya wangale mata get.ita kuma dari da tamanin ta fita gidan batare da tunanin komi ba.