HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Hjy Lami ta kira ta shedamata komi cewa tayi kawai su shirya su koma wurin bokan wannan ba abun abari bane gara su koma koma mi za’ayi ayi shi kawai.

Koda nagama lectures sallama mukayi da nabila tare da bani kwarin gwiwar kada inji tsoronta nima gida nane.Nabila har ta dau hanyar gida sai kuma wata zuciyar tace mata taje gidansu ta gani ko daddy ya dawo haka ta karkata motarta don zuwa gidan, koda ta shiga ba wanda ya sani don bata shiga da mota ba bakin get ta ajiye ta haka suka gaisa da mai gadi ta shiga ta bayan lambun gidan ta shiga amma abunda kunnenta suka jiyemata ne mummy na fada ma Aunty jamila yasa takasa gaba ta kasa baya sbd razana datayi……

Masha Allah ku biyo ni next page Insha Allahu don jin mekefaruwa?Ina ma kowa ftn Alkairi Masoyan TUN INA KARAMA????

 

Takuce sa’ar mataaaaa ????????????????????????????????

TUN INA KARAMA ????????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

By Sa’adatu Bello Saadatu99gmail.com!

PAGE 32

………..Nabila jikinta rawa yakeyi sbd tsoro da fargabar abunda taji Mummy na fada ma Aunty Jamila.cikin sauri ta fasa shiga cikin lambun ta juya baya da gudu gudu take tafiya tana waiwayen bayanta haka ta karaso bakin get din gidan su ta fito ta karamar kofa ta nufi motarta dama mai gadi ya zagaya don haka tashin motarta kawai yaji.

Tafiya take tana tunanin anya Mummy tana cikin hankalinta amma ita ko Aunty Jamila me take nema da take kokarin lalata rayuwar Hawwa sbd namiji?kaicho!!!hawayene masu zafi suke zubar mata tuki takeyi da haka har ta isa gidan Hawwa dake Barhin, hon tayi mai gadi ya bude mata ta shiga wurin parking ta nufa tayi dai lkcn mai gadin ya iso yana gaisheta cikin karfin hali take amsawa ganin motar Yaya Yusuf yasa tasan Hawwa ta iso gidan direct kofar gidan ta isa tare da taba bell din Hawwa har zata shiga wanka taji an taba bell cikin mamaki tace “to waye kuma window dakinta ta nufa ta bude labulen hango motar Nabila tayi cikin sauri ta saki labulan ta juya ta dauki hijabinta ta sanya ta fito waje ta isa bakin kofar ta bude kallon Nabila tayi da mamaki xatayi magana Nabila ta kama hannunta suka shiga ciki binta kawai take da kallo don takasa cewa komi, koda suka isa falon Hawwa zama sukayi kan kujera sannan Nabila tace” Hawwa daga gidan Mummy nake “to lfy Hawwa ta tmbye ta?” Babu lfy Hawwa Mummy da Aunty Jamila zasu cutar dake “akan me Nabila zakice haka?” Walhi Hawwa gsky ne arayuwata ban taba jin ance wai za’a dauke ma mutum mahaifaba sai yau wurin Mummy sbd kada ki haihu wacan an zubda maki ciki yanzu kuma ance anyi asirin da za’a sanya Ajani ya sace maki mahaifa ta karashe magana cikin kuka.”bazan yi maki gardama ba sbd tsafi gaskyr mai shine amma ina so ki kwantar da hankalinki Nabila babu abunda zai sameni saida izinin Allah Nabila su basu isa su sauya abunda Allah ya hukunta ba don haka ina so kibar maganar nan kawai Nabila kema ki tayani rokon Allah Allah shi ya iya komi don haka kwantar da hankalinki kibar komi ahannun Allah.zare hannunta tayi daga na Hawwa kallon ta takeyi tana hango tsantsan imani da dogaro da Allah irin na Hawwa.tashi tayi ta ce”Hawwa wannan maganar dole Umma taji ta don tasan abunyi walhi banyi alkawarin yin shiruba sbda ke baki fahimtar irin illar da abun zai haifar ba don haka ni na wuce yakamata ki kiyaye cikin sauri ta bude kofar dakin ta fito Hawwa ta biyota tana kira amma taki saurarenta har ta fice daga gidan ta shiga motarta ta fice aguje shi kanshi mai gadin ya tabbatar ba lfy ba.

Hawwa dawowa tayi don ita kanta abun ya girgizata amma bata son ta nuna ma Nabila afili amma duk da haka bata tsira ba don dama tana tsoron Umma taji maganar ta tashi hankalinta amma tunda Nabila taki saurarenta ya zatayi wani irin kukane yazo mata ta durkushe wurin tanayi aranta tana cewa nikuma irin tawa kaddarar kenan ya Allah ka kawo mani dauki don girman zatinka don tsarkin mulkinka ya Rabbi.

Koda Nabila ta koma gida haka tasamu Umma ta sanar mata komi bata boye mata ba Umma tayi mamkin rashin imani irin na hjy Mariya amma cewa tayi ba komi akwai Allah Nabila kuma zan fada Umar wannan mgnr koda zai iya daukar mataki don nasan indai Umar yasanar ma Yusuf komi zasu san abunyi, mu kuma mu cigaba da taya ta Addu’a insha Allahu yazamu samu masalaha Allah ya kyauta tashi kije kiyi abunda zakiyi ki zo kici abinci.”to Umma amma kina ganin bazamu nuna masu mun san komi ba?”A’a Nabila idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kamaka don haka bana son jin kin kara fadar wannan maganar mu barta kawai.

Koda Jamila taba gidan Mummy hankalinta kwance tana tunanin duk wata matsala tazo mata karshe badai so ya ke matar shi ta haihu ba to ai saida mahaifa ake haihuwa kuma ba ita cireta ma za’ayi gaba daya hhhhhh haba yarinya dani kike magana naso ma ace ya daina kusantarta amma shima wai bokan yace dolene ya rinka kusantar ta ai da dole su gaji su rabu amma ba komi wannan ma is okey for me….haka ta cigaba da sambatunta har ta isa gida.

Yusuf koda yusuf ya kira Hawwa bata bashi lbrn komi ba haka suka rabu cikin so da kaunar junan su tana tmbyrsa su mami yace mata mami tace zatazo kafin bikin Umar dadi taji sosai, ya kuma tmbyeta Jamila tana gida?tace masa ita bata sani ba ba matar shi bace ya kirata ya tmbyta mana.koda jin haka yasan cewa kishine haushi taji dariya yayi yace hakane kuma cikin zolaya.

Koda Yusuf ya dawo yasamu Jamila ta canza masa gaba daya ta fita harkarsa shida matarsa koda ranar girkinta ne bata damuwa dashi ta daina shiga hidimarsa abun yana bashi mamaki sbd Umar bai sanar masa komi ba yana so sai ya gama shirinsa don koda Umma ta fada masa cewa yayi ta kwantar da hankalinta ba abunda zai faru insha Allahu.ita kuma Hawwa ta kasa fadi ma Yusuf komi amma shi ya fahimci kamar akwai abunda ke damunta.amma sbd yanda yaga tana tashi tana tsayuwar dare yasa ji koma menene damuwarta zata samu waraka.

Yau takama weekend ne kowa na gida.akwai wata laya da aka bata ace ta sanya ma Yusuf a mota to tarasa yanda zatayi tunda ita dai ba shiga motarsa takeyi ba kuma daukarta yakeyi ba.amma yau tunda taga yana gida dabara tazo mata murmushi tayi nasamun nasara tashi tayi ta shirya tsab tayi kwalliyarta ta nufi part dinsa……hhhhhh muje zuwa.

Masha Allah ku biyoni next page don jin ya zata kaya tsakanin miji da matarsa zatayi nasara ko kuwa?

Taku ce sa’ar mataaaaa????????????????????????????????

TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

https://chat.whatsapp.com/JQ7XP7WslctGxTdw5G7OQw

By Sa’adatu Bello Saadatu99gmail.com!

PAGE 33

……..Tana shiga part din Yusuf da sallama bakinta ta tura kofar ta shiga, dago kai yayi yana mamakin yau Jamilace tashigo mashi daki da sallama?amsawa yayi tare da tashi daga kwanciyar da yake yana latsa wayarsa.karasowa tayi fuskarta cike da murmushi ta zauna daf dashi tace “barka da warhaka shima kallonta yayi yace” yauwa ya gidan?lfy klau ta amsa masa cigaba yayi da kallon yanayinta yana mata fassara da dama azuciyarsa.katse masa tunani tayi da cewa “wata alfarma nake so kayi mani.Ina saurarenki yace mata, cikin jin dadi tace’” motarka zaka bani aro tawa tasamu matsala kuma so nakeyi inje funtua dubiya ta karashe magana tana kara shigewa jikinsa kallonta yayi sosai ya hango tsabar yaudara atare da ita cikin hikima ya dan raba jikinsa danata yace “amma gsky bazan iya baki motata ba akira bakanike ya duba maki taki mana ai zaifi ko yakara she mgn yana mata kallon tsab.” Haba Yusuf yanzu don na nemi abu wurinka shine bazaka iya yi mani ba?cikin bacin rai tayi maganar.”wai ke wakika gani ina ba motata ne kodai neman magana ne?shin wai ma Jamila wa kika tmby zaki tafi dubiya har funtua?ko don kin dauke ni sakarai ne?sai kin shirya zaki tafi sannan zakice wai zaki tafi aida tafiyarki kikayi tunda baki san darajar aurenki ba kina yin abunda kika dama wai ke Jamila yaushe ne zaki natsu ki kama Allah?itama tashi tayi tace cikin bacin rai “dakata mal ba wa’azi naxo kayi mani ba abu na nema wurinka tunda kuma baka iya yi mani ai ba sai ka tsaya kana yi mani fada ba nima ina da yancina, wai dakata ma da anyi magana kace aura kai zakayi iko akaina sai na tambaye in zani wuri to ni ka dauke ni matarka ne da zaka kafa mani doka in bita?Yusuf baka isa ba!ai dakace wai ba mai hawa motarka ita waccen yar gwal din daka bata fa kwanaki fina tayi dazaka bata mota ni ka hanani idan har nima ka dauke ni mata ai sai kabani in hau mana.” Yes na bata mota amma ai ba yawo taje da ita ba office ta kaini ta wuce skul ko ance maki taje wani wuri da ita ne?”ni ina zan sani tunda ba binta nayi ba nasani”ai walhi data je data fadi mani taje tunda ita ba irinki bace nidai bazan baki motata ba amma idan canjin mota kike to zansa akawo maki sai ki fadi irin wadda kike so amma ba motata ba sbd ban san inda zaki shiga da ita ba.”ai kasan inada kudin sayan mota ko wace iri nake so amma basai na tsaya maula wurinka ba Yusuf kuma ai da waccan ka canza mawa da yafi maka itace nasan tana nema a wurinka ba Jamila ba wadda kowa yasan tana danata arzikin.murmushi yayi mai kayatarwa yace”walhi ita ba mota bace matsalarta nuna mata kansa yayi yace ni nine matsalarta ba komi ba in ma baki sani ba ki sani daga yau.cikin tsawa yace nagaji da surutun ki plss out!!!yana magana yana nuna mata hanyar kofa tashi tayi tace”daina yi mani ihu fita zanyi, fita tayi rai bace don gsky ya yarfata da yawa dolene ta dauki mataki kan Yusuf don kullum abun nashi kara gaba yakeyi wai me ke faruwa ne?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button