TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

“Stupid ke kullum bazaki yima kanki fada ba baki da aiki sai yawo da son zuciya to ni zanyi maganinki kada ki fasa sakarai kawai.shi kade yake fadansa don ita har ta shige part dinta dama babu inda zata abunda taso yi ne kuma ba nasara kiran Mummy tayi ta fada mata ita kuma Mummy ce mata tayi tabari zata san abunyi karta damu.
Bayan Yusuf yayi wanka ya shirya ya fito amma yayi mamakin rashin ganin Hawwa tazo part din shi tun safiyar yau kulle ko ina yayi ya fito sai kamshi yakeyi ya nufi part din Hawwa yana zuwa ya bude ya shiga tare da sallama amma jin shiru ya wuce direct bedroom dinta kwance yasameta peacefull tana bacinta daga ita sai wata karamar riga tasanya wando shotnick ga cinyoyinta nan sanbala sanbala gwanin sha’awa karasaw yayi wurin gadonta yayi kissing din hancinta kamar a mafarki taji kamshin turarensa da kyar ta bude runannun idanuwanta suka sauka anasa murmushi yayi yace” sleeping girl shine kika manta da mijinki kikazo kina bacci hankalinki kwance ko?itama murmushin tayi tace walhi bacci ne ya kamani sosai hubbynah am so sorry”naji dadi tunda hutawa kikayi dear tashi tayi ta shiga bathroom shi kuma kawai gyara mata gadon ya shiga yi cikin minti kadan ta fito shi yatsaya saida yaga ya taimaka mata ta shirya ta fito cikin kananan kayan daya zabar mata ta sanya tayi kyau sosai kamar ka saceta ka ruga hhhh….
Haka suka isa har daininig suka ja kujera suka zauna dama kafin ta kwanta ta gama komi ta shirya sannan ta kwanta coffee ta tashi tana hada mashi tare da farfesun kaza datayi ga kuma cheep’s data soya da kwai komi na cikin warm haka ta zuba mashi abunda yake so itama ta zuba nata saida suka koshi kyat sannan sukayi hamdala tashi yayi yace “zanje in gaishe da Umma daga na in wuce wurin Ammi itama mu gaisa turo baki tayi cikin shagwaba tace ” shine kaki cewa in shirya mu tafi.burge shi tayi sosai dariya ya yi mata yana cewa”ina zani dake kice ma Umma kwana zakiyi haka kawai in jawo ma kaina fitina?ki zauna bazan dade ba zan dawo.shikenan tace masa sai ka dawo ka gaishe mani dasu amma Allah next weekend sai naje na wuni can alright Allah ya kaimu”haka ya fita ya tafi.
Umar ya shirya mana tafiya kankiya zamuje mu gaishe da hjy kaka sbd mu mun samu hutu a skul kuma ga bikin Umar yanata masowa harda Nabila zamuje haka muka shirya muka nufi kankiya kwatsam hjy kaka ta ganmu tayi murna sosai tare da zolayarmu haka aka cika man gaba da abinci kala kala kowa nacin abunda yake so Nabila ce tace”gafa abunda kikeso Hawwa turo mani tayi gabana ina budewa naga farfesun kayan ciki ne ai ji nayi kaina ya sara kamar ana juyani gaba daya zuciyata ta tashi amai ya taho mani da sauri na tashi da gudu nayi bathroom ina toshe bakina ina shiga aiko amai ya fara shatatowa kamar zan amayar da yan hanjina.da gudu gaba daya suka yo kaina hjy kakace da Nabila suka shiga suka riketa Umar kowa da Yusuf suna bakin bathroom din kowa na tunanin to me yasameta?saida ta gama sannan suka sanya mata ruwa ta wanke fuskarta daga gani ta galabaita Umar ne yayi karfin halin cewa to ko Asibiti zamuje kaka?ya tambaya kamata sukayi suka dawo falon sunata yi mata sannu ita ko Nabila mamaki ne ya rufeta tasan Hawwa nasan kayan ciki amma meyasa haka ta faru?tambayar da bata san amsarta ba.hjy kaka ce tace Umaru ba sai anje Asibiti ba bari in kira wata likita nan makwabciyata ta duba mani ita.to suka amsa da shi ita kuma ta fita da sauri.kallonta Yusuf yakeyi shima cike da mamaki kada fa zargina ya zama gasky don kwanan nan Hawwa ta cika bacci ga cin abincin da abaya bata yinsa daya tambayeta sai tace masa tana ganin ulcer dinta ce takeyi mata haka sbd ita kanta bata kawo ma kanta komi ba haka ya cigaba da tunani har Kaka ta dawo tare da likitan gasheta sukayi gaba daya ta amsa masu cikin sakin fuska sannan ta kalli Hawwa wadda ke kwance tace “sannu diyata ya jikin?da sauki ta amsa kakace ta kalli Yusuf da Umar tace to ku kuma ai sai ku jiramu a waje ko?kunyi wani zuru zuru da ku kamar ku za’a duba Nabilace ta fara tashi tana dariya tabi hanyar fita suma sun san halin Kaka tashi sukayi suka fice kafin ta ce wani abu kuma.
Suna fita ta fara duba Hawwa tare da gwaji fitsari sosai ta dubata sbd kwararar likitace itama nan ta tabbatar da Hawwa nada ciki na sati uku ta sheda ma Kaka.Alhamdulillah Alhamdulillah Kaka take fada tana ta dariya ita ko Hawwa gabanta ne ya fadi don bata zata ba ga kuma kunyar Kaka da taji kamar ta nutse kasa ita ko bata ma san tana yiba.haka likitan ta rubuta mata magani da zata samu dan relief kuma tace ta rinka samun hutu sosai komi zaiyi daidai insha Allahu.Kaka tace hjy kinga wannan mai kama da jan kosai to shine mijinta bari i amso maki Albishir dinki.A’a hjy ai nima diyatace kuma walhi kinga tun da nashigo naga suna kama da mariganya Amina don har saida gabana ya fadi Allah sarki Aminatu mutuniyar kirki Allah ya jikanki da Rahama Amin muka amsa nikaina sai naji hankalina ya kwanta da matar kuma na tausaya mata.sannan tace akira mata su Yusuf haka suka shigo Kaka nayi mashi tsiya hjy Rabi kallon Yusuf tayi tace mashi congrat yarona very soon will be a father insha Allah tana magana tana dariya……..
Masha Allah masoyan Tun Ina Karama ina maku fatan Alkairi aduk inda kuke.kuma bazan taba mantawa da Malamata ba kuma Aunty nah ASEEY BEAUTY…….FATAN ALKAIRI GAREKI…..ALLAH YAKARA DAUKAKA….
Ku biyoni next page Taku ce Sa’ar mataaaaaa.????????????????????????????
TUN INA KARAMA????????????????????????????????
©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
By Sa’adatu Bello Saadatu99gmail.com!
PAGE 34
…………Gaba dayan su bakinsu yaki rufuwa sbd murna.akunyace Yusuf ya furta thank u Ma” sbd yadda matar tayi masa kwarjini.Umar ma cewa yayi mata sun gode da taimakon datayi masu haka Granny ma gdy kawai takeyi mata, ita ko Nabila tunaninsu daya da Umar akan abunda suka sani Jamila da Mummy suna kullawa amma kuma gashi Allah yafisu kowa kawar da abun yayi azuciyarsa yaci gaba da nuna farin cikinsa tunda dama ita Hawwa bata sa abun acikin rayuwarta ba tun lkcn da ta dukufa gayama Allah kukanta akan ya tsareta daga sharrin su Jamila.
Hjy Rabi ce ta dawo da hankalinsu gareta “Yusuf akula sosai wurin bata kulawa sbd kasan duk macen datake cikin wannan hali tana bukatar kulawa sosai da hutu kodan abunda ke cikinta, charaf Granny ta amshe maganar ” ai ina ganin ma Hjy nan zasu bar mani ita kafin tasamu kwarin jikinta kara bata rai Kaka tayi tace bazan bari asamu matsala ba irin wancan gara ta zauna gabana in kula da ita.cikin mamaki Hjy Rabi tace “Hjy ya zakice zaki rike mashi mata daga zuwa ziyara??ki barshi ya tafi da matarsa ai kinga yana kula da ita sosai.” Walhi Rabi wata mata gare shi shedaniya wancan cikin haka tayi mata Allura ta zubar mata dashi da sunan taimako kuma baki san wani abuba ni na haifi uwarta kanwar su Baban wadan nan yarane ta nuna Yusuf da Umar, to kinga ai duk zumunci ne gaba daya ita ko wannan yarinyar da kike gani ta nuna Hawwa amanace a wurinmu tunda batasan mahaifinta ba sai mamar wannan Isuhun da mahaifinsa tunda aka yayeta uwar Isuhu ta amsheta kuma Tun Tana Karama Allah ya hada Aurensu sbd dama shi Isuhu TUN TANA KARAMA yake kaunarta har Allah ya kaddara lkc yayi muka sheda.ita ko Jamila Yayar wannan yarinyarce Nabila amma gaba daya ita ta fita daban cikinsu shiyasa khadija uwar Isuhu ta dauketa tamkar ita ta haifeta kuma ita ma ga wanda zata aura nan Umaru to kinga yanzu idan takara sanin tana da ciki ai bamu san abunda zai faru ba Rabi??Kowa sauraren Kaka yakeyi har ta gama magana.nisawa Hjy Rabi tayi sbd ta fuskanci tashin hankali atare da Yusuf na maganar da Kaka tayi, cikin kwantar da hankali ta fara magana “awane Asibiti matarka take Aiki?tambayar data jefo ma Yusuf kenan, dagowa yayi suka hada ido da ita yace mata” FEDERAL MEDICAL CENTAR”ya sunanta yaji takara tambayarsa?”Jamila Muktar Sabo.”Alright ba matsala.kowa hankalinsa ya maido gurinta.