HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Umma kallon Yusuf tayi tace”ka biyoni zamuyi magana tashi yayu batare da yasake magana ba amma yana mamakin yanda za’ace mutum yana shan wannan yajin a cikinsa kuma ance ba komi lallai kam akwai drama.koda suka shiga samun wuri yayi ya zauna domin dai shi yau ji yayi ma yana kunyar Umma gaba daya don yasan tasan komi ita kanta ta gane hakan.kallon shi tayi sosai tace”Yusuf!Yusuf!!Yusuf!!!sau nawa na kiraka???gyara zama yayi yace”sau uku Umma….”Gud to ina so ka saurareni da kyau don kada wani abu yaje ya dawo agidanka, ni kuma wannan karan bazan yafe maka ba walhi anyi na farko anyi na karshe koda yake yanzu ai zata hadu da daidai ita tunda Nabila ta fadi mani komi harda matakin da Asibitin zasu dauka akanta to nima naji dadin haka ai dama ita gsky dayace daga kinta kuma sai bata Allah shi kyauta.Yusuf ka kula da amanar matarka kasan cewa Allah bazai barka ba in har ya kasance kana da hannu wurin cutar da ita sbd haka koda matarka tasan Hawwa nada ciki babu ruwanta da ita amma idan tace zatayi gangancin da zata sake zubda mata ciki to gsky abun bazaiyi kyau ba, tabari idan tasamu nata tunda su turawane komi nasu suke tsarawa to tana iya zubdawa idan bata shirya haihuwar ba amma ba ruwanta da diyata kaji abunda na fada maka ko???”naji Umma kuma zan kiyaye Insha Allahu.”masha Allah kuma yanzu haka mun yanke shawara da Abbanku Asabe zata koma gidanka da zama don ta kular mani da diyata da kyau har Allah yarabata d abunda ke cikinta sbd ai Umar ya fadi maka komi game da sharrin da suka so su bita dashi amma Allah ya fara nuna masu iyakarsu to na tabbatar basu hkr ba don haka idan da babba kusa da ita komk zaizo da sauki In Allah yaso.”hakane Umma mun gode sosai Allah ya kara girma.”Amin yaushe zaku wuce ne?”wai in ta gama yanzu sai mu tafi “To bana son kuma ace kana hanata cin abunda ranta ke so ko baku dashi ka fadi mani sai anemo mata dama shi ciki kala kala ne wannan naga nata da alama mai tarkace ne dariya shima yayi.” Gsky ne don yanzu haka bakiga abunda Kaka ta bata ba wai na kwadayi ne suna mota “eh ai lkc ne yana girma tana canzawa karka damu tashi muje ku tafi gida ku tafi gida ku huta Allah yayi Albarka.” Amin Amin Ummatah.

Koda Umma tazo tasamu Hawwa rigima sosai wai ita saidai ya barsu su taho gobe ba yau ba da kyar Umma ta lallabata don ta lura cikin ma rigima da fada yasata ga saurin fushi haka dai tace mata su tafi itama zata zo jibi ita da Nabila ko kwana ne sai suyi mata dariya tayi ta rungume Umma tana jin dadi itako Nabila gwalo takeyi mata an mata wayo….

Koda suka isa gida haka suka fito mai gadi na gashe su haka ya ba mai gadin key yace ya shigo masu da kayansu ganin motar Jamila aparking space yasan tana gida suna shiga main palo da sallam abakinsu gaba daya juyowa sukayi ita da Samira ne zaune suna shan shisharsu wurin duk ya turnuke da hayaki babu wanda ya tanka masu don ko sallama basu amsa masu ba haka suka wuce suna dode hancinsu babu kamar Hawwa data kejin kamar jiri na dibanta haka ta isa part dinta Baba Asabe na biye da ita shima Yusuf din kallo daya yayi masu ya shige ciki cike da takaicin Jamila aransa.Samira ce tace ma Jamila”ke ni wucewa zanyu tunda masu gidan sun dawo “wai ke banza ce ina ruwan mu dasu ” ke ni kinsan wancan mijin naki yana iya zuwa yayi manj rashin mutunci gara na bar masa gida tashi tayi tana daukar gyalenta da jakarta “jirani Jamila tace mata tashi tayi tashiga part dinta bata jima ba ta fito da kudi ahannunta ta mikama Samira tace” gashi nan kiyi amfani dasu “thank u besty tashi sukayi ta rakota har bakin get din sannan ta tafi mai gadi kuwa dadin dawowar mai gidan yaji ko ba komi zai huta da wulakancinta.

Kasa jurewa Yusuf yayi fitowa yayi don ya ci masu mutunci sbd Jamila ta kaishi karshe yasan tana shan shisharta amma ai ba a main palo yakamata tayi ba part dinta duk tsiyarda zatayi tayi ita tasani yana fitowa daga part din shi yaga tana kokarin shigowa daga waje.tana gani ya nufota tayi kokarin shigewa part dinta amma sakamakon wata irin tsawa da yayi mata wadda ta karde palon yasa ta tsaya cak keee!!!!!!!Jamila!!!!…..

Masha Allah Ina ma Allah gdy daya bani ikon yin wannan page din wanda shine zan ajiye Alkalamina sai kuma Allah mai kowa mai komi ya Kaimu Bayan Sallah lfy, Insha Allahu zan kammala wannan littafin mai suna TUN INA KARAMA:Kuma in shiga sabon littafina mai suna NA AMINTA DAKAI!!!!wanda shima soyayyace kuma sannan labarine mai taba zuciya.saidai kunji ni.Ina ina makowa ftn Alkairi Allah ya karbi Ibadunmu ya bamu falalar watan Ramadan mai Albarka yasa mu Dace Amin ya Hayyu ya Qayyum….

Ina mika gdy ta gareku yan uwana loverly sister’s dina Aseey Beauty, Magirat Musa…Allah ya kara daukaka.

My all fans Allah ya hadamu da Alkairi Ina neman Afuwar kowa duk wanda nayi ma ba daidai ba a yafe mani Takuce sis FATINAH…..

Real Sa’adatu Bello.Saadatu99gmail.com!✋????????????????????
????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

By sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah….duk kan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa kuma mai komi cikin yardarsa gashi ya sake dawo dani lokacin da zan karkare maku wannan littafin nawa TUN INA KARAMA…Ina godiya ga yan kungiyata Al’umma writer’s Association.Allah ya kara hada kanmu tare da kaunar juna Ameeeen.dftn anyi sallah lfy Allah ya karbi ibadun mu badon halinmu ba.Ameen ya hayyu ya Qayyum.

Mum sultan, mum Adnan, Shugaba, fatima, ummi Aunty Aseey sister jamila All the best my loverly sister’s i’am back insha Allahu..

Reader’s fatan Alheri gareku aduk inda kuke dftn anyi sallah lfy Allah ya karbi ibadunmu.Ameen…kuyi hkr damu muma muyi hkr daku inda kukaga kuskuren mu kuyi mana gyara inda shawara ku bamu mai amfani ta haka zamu karu da juna insha Allahu…

PAGE 36
………….Jikinta rawa kawai yakeyi har cikin hantarta takejin yana kadawa, jingina tayi da kofar part dinta don ji tayi kafafuwanta basa iya daukarta.cike da jarumta yake takowa gareta fuskar nan tashi babu alamar wasa ya koma mata wani zaki a haka har ya isa dab da ita har suna jin numfashin junansu.kallonta yayi cikin tsare gida yace”wai ke Jamila me kikeso ki zamane a rayuwarki???wato bazaki taba canzawa ba ko??yanzu iskancin naki ya kai har ki zauna main palon kina shaye shaye agidana ko??ciza leben shi na kasa cikin takaici da jin zafinta aranshi ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan yaci gaba da magana”hakika Jamila ko namiji ne yake da irin halayarki to abun dubawane bare ke a matsayin na matar aure amma kin kasa natsuwa kullum kina cikin badala da kara tarwatsa rayuwarki wadda nan gaba zakiyi nadamar abunda kika aikata,to wannan shine last warning dina dake na karshe saboda na fara gajiya da mugayen halin nan naki ke kullum cikin rashin mutunci kike tunda kinsa kanki masifa ki rinka zama part dinki idan ma wuta zaki sha ke kika sani matsalarki ce bani da damuwa amma ba ko ina ba agidana kuma na fada maki bana son kina tara mani yan iska agida don haka wannan shedaniyar kawar taki nasake ganin kafarta agidan zakiga abunda zai faru.juyawa yayi zai bar gurin yaji muryarta tana cewa”sannu mai gida ai ban san ka ka iya goriba sai yau amma dai kasan nima inada arzikin sayen wannan gidan naka don hak basai ka wulakanta ni ba kuma kasan nima na mallaki abunda kake takama dashi.afusace ya juyo yayo kanta da gudu ta shige part dinta ta banko kofar ta rufe.kwaf yayi yace”dakin tsaya karamar mara kunya.duk abunda ke faruwa Asabe na kallonsu ganin Jamila ta shige shikuma ya bi hanyar fita yabar gidan.yasa itama ta juya part din Hawwa tana dariya da sallama ta shiga tasamu Hawwa kwance a palo bayan ta amsa sallamar Asabe ganin tana dariya yasa Hawwa tace”Baba Asabe naga kina dariya lfy?”ai uwar dakina ina can ina kallon drama tsakanin Alh karami da matarsa.murmushi Hawwa tayi tace”indai kina gidan nan zaki sha kallo don kusan kullum sai sunyi basama gajiya shi kuma ya biye mata.”uhum ai yau da ta tsaya data daku don guduwa tayi ta shige sashenta ta rufe kofa kuma ya fada mata kada ta kara sha mashi wannan abu agida har tana cewa ita ma tana da kudin sayen gida kinji karfin hali fa.dariya sukayi gaba daya Hawwa tace Allah ya kyauta to shi yana ina Hawwa ta tmby Asabe??”nadai ga ya fita ya bar gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button