TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Kullum cikin tada mani hankali take wai dole saina sakar mata diya kumani umar walhi bana iya daukar hannuna in yi saki kokuma in furta da bakina wai in saki hawwa tare da nuna kanshi ya girgizawa kamar zaiyi kuka yace frnd ican’t umar zuciyata zafi take duk ranar da ummah tayi ikirarin rabani da hawwa.
Tunda ya fara magana yaji abokin nashi ya bashi tausayi, karo na farko kenan tunda matsala ta faru tsakanin shi da hawwa ya tausaya masa.sbd shi kanshi haushin shi yakeji sbd bai kyauta ba duk da yasan ba laifinsa bane to amma sbd me bazai dauki tsatsauran mataki ba yana gani ana cutar dashi amma ya kasa magana.umar ya nisa yace agky frnd bazan boye maka ba dolene ummah tayi maka haka sbd kayi kuskuren da sai munyi da gske zamu gyara shi, kuma walhi kada kasake ayi nasarar rabaka da hawwa kayi duk abunda zakayi ka tabbatar hawwa ta dawo gareka.shine abunda zamuyi, “yusuf yasake runtse idanuwan shi ya kara tura kujera baya ya kwanta yayi blance yace umar ita kanta hawwa ta canza mani maganar ummah ita take amfani da ita yau karara na hango tsanata a idanuwanta.
….cikin damuwa umar ya taso ya dafa kafadarsa yace kayi hkr frnd insha Allahu komi zaiyi daidai kuma hawwa zata dawo gareke da yardar Allah karka damu.umar ya koma ya zauna yace frnd kasan wani abu?cikin yanayin damuwa ya girgiza masa kai alamar a’a ya cigaba da cewa to dazun jamila tazo wurina cikin tashin hankali ya dago kanshi ya kalli abokin nasahi ido cikin ido yace what?jamila!
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? takuce sa’ar mataaaa????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 7
ASALIN LABARIN:
…….waye yusuf Bashir mado kankiya?Alh Bashir mado kankiya haifafan cikin garin kankiya ne dake jahar katsina Alh bashir su hudu ne wurin mahaifinsu.Alh bashir shine babba a cikin su da shi da kanin sa Alh bello sai kanwar su hjy mariya dakuma autar su rabi atu.sun taso cikin jin dadi da walwala ta rayuwa, sakamakon mahaifinsu yana da ilimi na addini dana zamani yasa yazama wayayye kuma gashi yana amfani da iliminsa wurin iya mu amula da mutane.sannan ga tarin dukiya Allah ya hore masa, yana kasuwancin shi cikin ilimi da gogewa ta rayuwa.matar shi daya hjy hauwa’u wadda itace mahaifiyar su Alh bashir.sunyi auren soyayya da Alh mado itama yar cikin garin kankiya ce.sunyi zama na soyayya da Alh mado wanda har Allah ya azurta su da haihuwar yara guda hudu, shima Alh bashir koda yake dan boko to ya biyo baban shi wurin son business sosai don tunda ya taso ya gama karatunsa na degree akan business ne yayi karatu har master’s din shi.
Shi kuma Alh bello gsky yafi karfi a govment sbd yanzu haka shine commissioner na manoma watau agric.ita kuma hjy mariya sakamakon mijinta mai haline yana da tarin dukiya sosai shiyasa ita bata aiki sai kawai ta fada harkar kasuwanci, tana fita dubai tana kawo kaya sosai.sai Rabi’atu wadda itama tayi aure amma tana aiki da ma’ikatar lfy ta kano.gaba dayansu kowa yana da rufin asiri daidai gwargwado sbd Alh moda koda yake da kudi bai yarda ya bar yaranshi ba babu ilimin addini dana zamani ba.bayan rasuwar maifinsu ne Alh mado Alh bashir ya koma katsina da zama a inada ya auri diyar aminin babansu Alh garba mai dala.wadda dama suna soyayya dashi wadda hakan yasa iyayensu sukayi masu alkawarin auren junan su kuma Allah ya kaddara.shikuma Alh bashir dalilin dayasa ya koma katsina da zama sbd duk harkokin mahaifin shi suna can to koda y rasu sai ya tattara gaba daya ya koma da zama.yaso ya tafi da mahaifiyasu amma ta nuna mashi tafi son zamanta anan kankiya cikin danginta haka nan ya hakura badon ranshi yaso ba.amma duk satin dunya yana zuwa ya kwana biyu wurin mahaifiyarsa saidai idan baya kasar.kuma yana zuwa da matarsa hjy khadija wadda mace ce mai karamci da nuna kulawa ga yan uwan mijinta shiyasa ta shiga ran kowa na family dinsu Alh bashir .ita kanta hjy hauwa’u tana kaunar sirikar tata sosai bata son taji ance ga laifinta.shikuma Alh bashir ganin yanda take kula da mahaifiyarsa da yan uwansa yasa yake kara ganin darajarta da kimarta.
Kuma yake kyautata mata, itama haka zamansu yake cikin mutunci da girmama juna.to amma duk da haka basa shiri da hjy mariya sbd ita gsky halinta ya sha banban yan uwanta, ita mace ce wadda tasa duniya gaba bata tunanin komi sai son zuciya, sbd tana fita kasashe tana haduwa da kawaye sun zugata tana ganin kowa ma bai isa ba.sbd haka ne basa shiri da Alh bashir yayanta shikam duk harkar wani shashanci baya cikinta.kuma shi mijin nata sbd son dayake yi mata baya iya magana duk yanda take so to haka za ayi Allah ya kyauta.itama mijinta dan katsina ne nan suke zaune a le out.shima Alh bello yana katsina tare da iyalinsa, sai hjy rabi’atu dake aure a kano ita mijinta dan kano ne a nan kundila suke da zama anan take aikinta a ma’katar lfy dake jaha.
Allah ya Albarkaci Alh bashir da haihuwar yara uku aunty zainab ce babba sai yusuf sai kuma Nafisa wadda itace auta.rayuwar farin ciki da kaunar junan su haka rayuwa take tafiya.hjy khadija su uku ne wurin mahaifinsu Alh suleman shine babba sai ita umma sai kuma babana wanda shine kaninta Alh mansir shine mahaifina Allah yayi masa rasuwa ne a sakamakon hadarin mota.daga kaduna zuwa katsina, Allah ya gafarta ma iyayenmu yasa Aljannace makoma Ameen ya hayyu ya qayyum.
To lkcn mahaifina shi yana kaduna ne zaune tunda can yake aiki tare da mahaifiyata wadda dama it yar kaduna ce anan ya aureta alkcn daya rasu an haife ni amma shekareta daya lkcn.sbd haka iyakar zaman danayi da mahaifiyata kenan ana yayeni hjy khadija tace lallai sai an badani haka dai mamana tayi kawai ci sbd karamcin yayar mijin nata ta hakura ta bada ni haka na tashi ina ganin umma itace mahaifiyata tunda koda wasa bansan umma da Abba ba basune iyayena ba tunda ko yaransu ban taba ji abakinsu ba kowa yana sona.nasan dai akwai mamin kaduna tunda haka naji suna ce ma mamana.kuma sai inji suna ce mata mamin yusuf naga kuma yawancin zaman shi acan wurinta ne .na tmby umma sai tace mani ai ita mami itace mamanshi dana dameta da tmby sai tace tashi kibani wuri harga Allah ban kawo komi araina ba.mami tayi aure ta auri wani aminin dad dina wanda shima matarsa wurin haihuwa ta rasu shima mutumin kirkine .amma mami da kyar ta amince da auren shi dayake kuma Allah ya kaddara haka ta auri Alh isma’il shima dan zaria ne amma enginer ne yanzu haka yana Abuja can yake aiki amma nan yabar mami a kaduna sbd tace tafi son zaman kata anan tare da yaranta saidai yarinka zuwa weekend ko kuma wani lkc suje su danyi hutu su dawo
Diyarshi wadda matarshi tabari itace babba wurin mami sai wadanda ta haifa guda uku yaran shi hudu amma baka cewa mami ta haifi ummi ba sai Abdul da khalid da halimatu sune yaran mami
Hjy mariya yaranta biyu jamilace babba sai kanwarta nabila sakamakon tsada haihuwa datayi wai ita bata son ta tara yara kuma su tsaida mata harkokinta nabila ba halinsu daya ba da jamila shiyasa gaba daya basa shiri shiyasa koda yaushe tana gidan umma muna tare ita kuma hjy mariya ta tsani hakan shiyasa ko hidima akaje ta rinka yima umma habaici kenan ita kuma bata kulata.