HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Jamila na shiga ciki ta sa key a kofar tace ai walhi bana tsayawa ka bugi banza.shiga tayi ta dauko wayarta ta kira wata no banji me tace ba saidai naji tace ok ina zuwa yanzu….

Masha Allah kuyi hkr da wannan insha Allahu kullum zaku jini Takuce sa’ar mataaaa

Ku biyo ni next page my all fans????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

http://global-4-lvs-hopper.opera-mini.net/ha23-10-07/36652/0/-1/global-4-lvs-hopper.opera-mini.net/501d18a8bf0fbe3e10d3df628a6eeec7325a0140/snap.webp

By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!

PAGE 37

…………….Koda Yusuf ya fita bai zame ko ina ba sai wani katon mall inda ya shiga ya kwaso ma Hawwa kayan kwalama kala-kala haka ya ciko leda biyu da kaya na ciye-ciye don baya son ta nemi komi, yana gamawa ya biya ya fito aka kawo mashi kayan amota.koda ya fito juyawa yayi domin ya dawo gida da wuri tunda Hawwa ma bata san fita yayi ba.cikin sauri yake tuki don baya son har ta nemesa bata ganshi ba, yasan halin rigimarta bare yanzu abu kadan sai tayi fushi dashi haka yake tuki yana zancen zuci baima san lkcn da murmushi ya kufce masa ba.girgiza kai yayi dai-dai lkcn da zai shiga kwanar gidansa dai-dai nan ita kuma Jamila zata fita kallo daya yayi mata ya kauda kai tare dayin tsaki mtsss ahankali ya furta mahaukaciyar banza.ita ko koda ta ganshi bata saurari komi ba kara taka motarta tayi ta fice layin nasau da gudu kamar zata bar gari.Allah ya kyauta ya sake furtawa tunda yana hangenta ta mirrow.yana isa get din gidansa mai gadi ya wangale masa ya shiga.

Wurin parking ya karasa yayi parking sannan ya fito ya bude bayan motarsa ya kwaso ledojin dake ciki ya kulle motarsa ya nufi cikin gida kai tsaye part din Hawwa ya nufa da sallama ya tura kofar ya shiga amsawa sukayi gaba daya tare da kallon kofar ganin shi sukayi da kaya niki-niki saurin mikewa Hawwa tayi ta tare shi shi kuma ajiye kayan yayi akasa yana kokarin riketa kaucewa tayi tana nuna masa Asabe kashe mata ido daya yayi ya wayance da cewa”Baba sannuku da gida”yauwa Alh Karami brk da zuwa ta amsa masa.tashi Asabe tayi tana cewa “uwar dakina bari inje inyi wanka kafin ki gama shan fatenki.dariya Hawwa tayi tare da cewa” afito lfy fita Baba Asabe tayi itama tana dariya don ta fuskanci masoyan suna son kebewa da juna tana fita ta rufo masu kofar ajiyar zuciya Yusuf ya sauke tare da jawo Hawwa jikinsa ya rungume ta tsam…..

Ita kuma kara shigewa tayi cikin jikinsa”wai ina ka shigane Hubby nah??baice komi ba kama hannunta yayi suka isa wurin ledojin daya ajiye zaunar da ita yayi sannan shima ya zauna ya jawo ledar ya fara budewa wata sweet Hawwa tagani taji kawai tana son shanta hannu ta mika ta dauko ta shima hannu yasa ya amsheta daga hannunta barewa yayi ya jefata abakinsa itama saurin kai bakinta tayi acikin nasa don tasan abunda yake nufi kenan tunda yayi hakan , hakan ta cigaba da tsotsar sweet din abakinsa tana shanyewa shi kuma yana bata cikin hikima da soyayyar junansu.tana gama sha tace “don Allah kabani plate din abinci na gashi can mikewa yayi ya nufi wurin data nuna masa yana zuwa yaga faten tsakine daya sha yakuwa har zaiyi magana ganin tsamin yakuwar sai kuma ya tuna kashedin umma sai ya fasa yasa hannu ya dauki plate din ya kaimata yana ajiye mata tasa hannu ta cigaba da shan abunta.shiko kallon mamaki kawai yakeyi mata sbd yasan abaya bata damu da abinci ba amma yanzu gashi wanda bai kamata ba ma take ci tsakaninta da Allah.

……..Jamila na isa gidan hjy Lami qawar mummy tayi parking ta fita ta shiga gidan da sallama apalo ta sameta zaune cikin fara’a ta amsa mata tare da nuna mata kujerar dake kusa da ita zama tayi cikin jin dadi Jamila ta gaisheta bayan sun gama gaisawane, Hjy Lami ta gyara zama sosai ta tura ma Jamila ruwan dake gabanta da da kofi amsa tayi ta tsiyaya tana sha “kinsan dalilin dayasa na kiraki Jamila???” A’a Hjy.”hmmm to so nakeyi in canza maki boka sbd naga wannan ba zai mana abunda muke so ba tunda har yanzu babu abunda ya canza tsakaninki da Yusuf ko kuma akwai ta tmby Jamila cikin hikima???”walhi Hjy yanzu haka saida ya wulakanta ni kafin ki kirani in baro gidan har kusan bugu na yayi don na gudu na rufe kofa yanzu ma abunda yasa na fito ganin baya gidan ne amma kuma lkcn da zan fito naga ya dawo ashe ba nisa yayi ba, ni takaicina kwata-kwata ya daina kulani bare ma in samu inyi amfani da maganina da aka bani kuma duk wata kissa da kisisina inayi masa don dai in yaudaresa amma a banza ko romancing dina babu abunda ke shiga tsakanina dashi sai ya tabbatar ya kaini karshe sai ya kyaleni iya ka yayi mani abunda zanyi satisfy dina shikenan amma baya yarda ya shigeni ni tunanina ko ya fahimci wani abu ne oho??amma ai yana like ma wannan shedaniyar yarinyar nikuma dana mashi magana saiyace wai shi sex bai dame shi ba amma daka ganta ai kasan namiji na taba ta yanda jikinta ke kara budewa.nisawa Hjy Lami tayi sannan tace”dama abunda yasa nace kizo kenan tunda mariya bata kasa tana Dubai kinga ke sai kisa lkc mu tafi tunda yanzu dole dake zamuje sbd can gaban kano ne kauyen yake inda zamu ga Bokan.”badamuwa zuwa weekend sai inshirya mana tafiyar zance ma Yusuf zani bikin kawata a kano ????????????

Masha Allah ku biyoni next page don jin ya tafiyar zata kasance

Ina mika gdy gareku all fans TUN INA KARAMA Allah ya bar zumunci Takuce Sa’ar Mataaaaaa????????????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

*May Allah bless yours brothers and sisters , May Allah brighter his grave Dad And Mom*

By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!

 

PAGE 38

…………Yusuf baiyi mamakin ganin Jamila har takai karfe 8:30 bata dawo ba sbd yasan yanzu haka tana gidansu wurin mummyn tah sbd shi bai ma san mummy bata kasa ba.shigowar motarta ya tabbatar masa da dawowarta hankali kwance ta shigo gidan tayi parking motarta ta fito direct ta shiga gidan bada tunanin komi ba ganin shi apalon yasa tayi turus ita batayi gaba ba ita kuma bata koma baya ba, shahada tayi ta shigo taraba zata wuce part dinta kallonta yayi cikin tsana da takaici yace”ai da kin sani da kwana kikayi tunda ke baki da control.bata ce masa komi ba ta wuce ta shige aranta tana cewa kakusa zama nama a hannuna kajira lkc mal.shima kyaleta yayi don shi walhi shedancin Jamila ya fara bashi tsoro don gaba daya ita duniya bata shakkar kowa Allah ya kyauta.tashi yayi shima ya rufe kofar ya shige part dinsa da takaicin Jamila aransa.

Akwana atashi asarar mai rai yau ne tafiyar Jamila da Hjy Lami don haka tasamu Yusuf ta fada masa amma yace bazata ko ina ba asalima shi bai san wata kawarta akano ba don haka babu inda zataje haka suka sha rigima adaren.washegari yana tashi bayan ya dawo sallah Asuba lkcn ma bata da alamar tashi bare tayi tunanin yin sallah do ba damuwarta bane ganin haka yasa shima yashiga ya dauko key din wata motarsa wadda bai cika hawanta ba yaje parking lot ya fito da ita daidai inda tayi parking yayi blocking dinta yanda babu yanda zatayi ta fita da motarta.murmushin mugunta yayi ya koma cikin gida ya shiga part din Hawwa bayan sun gaisa yake ce mata zai shiga yadan kwanta ya huta “ok yau baccin safe za’ayi kenan to a Fito lfy cikin zolaya ta ke masa mgn”dariya yayi yace ” amma in kinjj shiru ki tasheni “ok dear fita yayi ya nufi part dinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button