HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Bayan ta gama baccinta ta tashi tayi wanka ta shirya tsab ta fito zata tafi bata ma sake bi ta kansa ba tana fita taga anyi blocking dinta kuma motar Yusuf ce wadda ma baya hawanta cikin mamaki ta isa wurin don ta tabbatar tana isa taga tabbas blocking dinta yayi cikn bacin rai da jin haushi a fusace ta wuce part dinsa ba bacci yakeyi ba shiga tayi ko sallama babu shi kansa yasan haka za’ayi cikn zafi tace ” wai meyasa Yusuf bazaka kyaleni agidan nan ba inyi rayuwata mai dadi kaidai ba mata ka daukeni ba amma gaba daya ka takura mani tafiyace sai nayi ko ka yarda ko kada ka yarda.dariyar rainin hankali yayi mata yace”kin gama??to idan kin gama sai ki fitar mani daga daki domin ni ba sakarai bane dazan barki da aure na kina gantaliba tafiyace nace bazakiyi ba to sai me kuma???nunata yayi da yatsa yace Jamila ki kiyayeni walhi nafa gajiya da iskancinki don haka babu inda zaki fita ki bani wuri !!!cikin tsawa yake maganar “ai walhi na sai naje kuma ai kasan akwai motoci agianmu ko??to don haka zanje in dauki wadda nake so in tafi da ita juyawa tayi fuuuu!!! ta fita tsaki yayi mtsss yabi bayanta da kallo ga mace har mace amma ba hali.tana fita yanda mai gadi ya ganta yasan ba lfy bude karamar kofa tayi ta fita tabe baki yayi yace” yau ba kanta kenan su Hjy Babba.adaidaita tasamu ta kaita gidansu nan ma mai gadin gidansu saida yayi mamakin ganinta ahaka shiga kawai tayi cikin gidan sanin inda komi yake yasa ta nufi inda tasan zataga keys din motocin ta dauki daya ta fito tazo wurin motocin ta hau ta bata wuta ta fito daga gidan ta nufi gidan Hjy Lami koda ta isa dama ta gama shiryawa kawai tafiya sukayi sai muce gamu nan muna bibiyarku.

Duk abunda ya faru tsakanin Jamila da Yusuf Hawwa taji su amma tana mamakin yadda Yusuf zai cigaba da biye mata suna saida hali kullum amma tayi alkawarin yi masa mgn cikin hikima yanda zai daina kulata idan tana neman rigimarta.koda suka gama komi suka gada break fast ganin yaki fitowa tace ma Baba Asabe bari ta shiga ta kira Yusuf.tana shiga zaune ta samesa yana danna lapton dinshi da sallama ta shiga gani yayi tayi masa wani irin kyau ga wani haske yana baiyyana ajikinta masha Allah ya furta karasowa tayi kusa dashi ta zagaya ta bayansa ya dora hannuwanta a kafadunsa ta dan rankwafa daidai fuskarsa tace “hubby nah yakamata ka huta ka rufe lapton din nan haka nan weekend ai namu ne na iyali bana office ba.zagayo da ita yayi ta gabansa sbd wani irin kamshi da yake ziyartar hancinsa kara jawota yayi ajikinsa yana sunsuna wuyanta can cikin husky voice dinsa taji yace” ba wanj aiki nakeyi ba dama yanzu zan fito inyi break.murmushi tayi itama tace “to tashi kayi wanka mu fita ok yace mata tare da mikewa tsaye binshi tayi hara bathroom din ta hada masa ruwan wanka zata fito ya riketa saurin kwacewa tayi ta ruga ta rufe masa bathroom din tana fitowa bata tsaya komi ba ta hau gyara masa dakin nan da nan ta gyara komi ta kuna kamshi ko ina sannan ta dauko mashi kayan da zai sanya bada jimawa ba ya fito ta tai maka masa ya shirya suka fito tare suka nufi dianing suka zauna suka fara ciyar da junansu.

Tafiya sukeyi sosai sbd gudun da jamila keyi har sun shiga kano daga nan suka dauki hanyar kwankwaso inda daga nan zasu shiga kauyen dazasu haka kuwa akayi sun shiga kauyen basu sha wahala ba wurin gane gidan bokan sbd ya fice sosai koda sukayi parking akofar gidan da mota samu sukayi wani yayi masu iso suna shiga gidan abun mamaki kamar ba kauye ba komi na alatu akwai shi cikin gidan dakin da aka kaisu shikan shi abun kallo ne mamaki ne ya ciki Jamila tab azuciya bata sha mamaki ba saida taga ya shigo cikin dakin don bakace mashi boka ne fes-fes dashi ga shiga ta alfarma jikinsa ga kamshi na tashi abunda bata sani ba shi da yan siyasa yake harka duk wani tsibbu na siyasa ya sanshi haka suke masa layi kuma abun duniya suna mashi sosai shiyasa komi na shi sukeyi masa.” Barkanku da zuwa taji yace gaba daya suka amsa da yauwa barka dai kafin wani lkc an cika masu gabansu da kayan ciye-ciye da sha, bayan sun gama gaisawa ne ya dauko wani abun tsibbun shi yace “Jamila kina so mijinki yazama ke dai ce aransa kina so ki kauda hankalinsa akan matarsa kuma kina so ki mallaki komi na shi ciki harda uwar data haife shi koba abunda ya kawo ku kenan ba???cikin tsoro da gaba dayan su yanda sukaji ya ambaci sunan Jamila yabasu mamaki cikin sauri baki na rawa ta amsa masa da ” haka ne bukatata kenan Yusuf yazama nawa ni kadai kuma in juya shi yanda nake so.”wannab ba matsala bane indai zakiyi yanda ya kamata anyi an gama “zanyi kuma ko nawa ne zan biya ayi komi boka dariya yayi yace baki da matsala Hjy to yanzu abunda zakiyi shine ina so ki kaurace ma mijinki har sai mun kammala akinmu don yadda ranar da kuka hadu magana ta kare ko mgn zaiyi da uwarshi saida izininki ” haka muke so boka inji Hjy Lami.”to yanzu ke Jamila zaki iya dawowa nan da kwana hudu mu fara aiki?cikin sauri ta amsa da sosai ma kuwa zan iya dawowa mana.”to kizo ke kadai akwai abubuwan dazaki karba wanda ba’a so kowa ya gani daga ni sai ke.”to ba damuwa da ce masa cikin sauri kaji kidahuma!!!Allah ya tsare mana Imaninmu Ameen ya hayyu ya qayyum…haka suka shirya komi akan zata dawo nan da kwana hudu ta dauki kudi masu yawa ta bashi ya sallamesu suka kama hanyar gida.

Kwance suke tayi pillow da cinyarsa yana shafa mata maganin ciwon da kafarta keyi mata wajan karfe 10:40 na dare sukaji tsayuwar motarta tabbas sun san itace parking tayi ta fito ganin har yanzu motarta a blocking take yasa ta ja tsaki mtsss akin banza.jin zata shigo yasa Yusuf ya hade fuskarsa data Hawwa ya kuma sanya bakin shi cikin nata ya fara tsotsa kamar lolipop budewar da zatayi idanuwanta suka sauka akan su wata irin kara!!!!tayi wadda hakan bai sanya Yusuf ya cire bakinsa daga na Hawwa ba hot kiss kawai yake bata…hhhhhhh muje zuwa

Masha Allah ku biyo ni next page insha Allahu don jin ya zata kaya???

Iluv u All fans Tun Ina Karama naji korafinku insha Allahu zaku rinka samu dogon typing har mu gama amma dai kun san typing wahala????????????

Takuce sa’ar mataaaa????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!

PAGE 39

……..Yusuf bai fasa abunda yakeyi ba.ita ko Hauwa kokarin tureshi takeyi, jitayi babu dadi kuma ita bata son yana biye mata sunayin wannan abun don bai kamata ba gaskiya ita a tsorace takema’ dan ihun da
Jamila tayi,cikin zafin nama ta iso wurinsu kama Yusuf tayi tana kokarin janye shi daga jikin Hauwa wata irin tsawa ya daka mata wadda har saida palon ya amsa “keeeeeeee!!!!kada kisake ki yunkurin shiga hurumin da bana kiba!!ki tsaya matsayinki kin dawo gantalinki shine zaki shigo mani da ihu cikin gida kamar kin kama kwarto ina jin dadina da matata ke kuma kin dawo zaki takura ma rayuwarmu wai meye haka ne Jamila????” Ai dai yau girki na ne sbd me zakazo ka makale mata kuna abunda kuke so?”hmmmm Alhamdulillah ashe kin san girkin ki ne shine kika fita bada izinina ba kuma kika dawo alkcn da kika ga dama duban agogo yayi yace karfe nawa yanzu ace macen kirki na waje sbd tasamu freedom yau me kika bani naci tunda girkinki ne??bayan haka ko ruwan zafi kin bani nasha?amma kinzo kina haukan girkin ki ne anci amanarki sai kawai ki
katse mani jin dadina da matata “wai ni ba matarka bace da zaka kama kiran matarka ai mata biyu gareka yakamata ka rinka jam’i.murmushin mugunta yayi ya kalleta da kyau yace” amma ke kike fadin haka da kanki bayan ni banida banbanci da mai mata daya ?maganganusa sun fara bata mata rai sosai juyawa tayi a fusace ta shige part dinta tana huci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button