HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Ita ko Hawwa kamar wata status ta zama sbd gaba daya ita lamarin nasu mamaki yake bata kullum cikin fada kara janyota jikinsa yayi daukarta yayi cak bai direta ko ina ba sai cikin bedroom dinta akan gado dariya kawai takeyi don ita yanzu kwata-kwata bata ma sanya Jamila aranta bare ma ta dameta.ita kuma Baba Asabe ta dade da shigewa part dinta ta kwanta tunda dai tasan Yusuf yana gida wurin Hawwa bai bar dakinba saida ya tabbatar da Hawwa tayi bacci sannan ya shafeta da Addu’a sannan ya kashe mata komi na sashenta ya jawo mata kofar sannan ya kulle mata part din ya fita tare da kewar matarsa aransa da soyayyar ta aranshi. Ita ko Jamila tana shiga ta jefar da jakarta da wayart ta shige bathroom don wanka take bukata.

Shiko Boka tunda Jamila ta bar gidan shi yake tunaninta wanda har yana ganin kwana hudu tayi mashi nisa don gsky Jamila tayi masa irin macen daya ke so ne kuma daga gani zai moreta da yawa don gsky zai huta dayawa gsky mijinta ya bar banza duk da
bai san waccen matar tasa ba amma ai ita ma wannan tayi dole ya bibiyeta ya more sosai haka dai yayi ta saka sharrinsa a zuciyarsa.

Kwanci tashi ba wuya wurin Allah lkn komawar Jamila yayi haka ta dauki hanya ita kadai don cika burinta daga wurin aikinta ta wuce batare da ta sanar ma mijinta zataje wani wuri ba Hjy Lami ce kadai tasan da tafiyarta daidai zata shiga kano sukayi clashing da Umar shi kuma zai fita tabbas itace to amma ina zata haka??dage kafada yayi alamar bai damu ba ya wuce yayi tafiyarsa don shima wani uzurinsa ne yakaisa kano.itama ta gan shi amma ko ajikinta do ayadda take ji ko Yusuf ne ta gani bazata tsaya ba bare wani Umar, haka ta isa har gidan Boka tana zuwa yayi mata kyakyawar tarba haka ya gama shirya mata karya da yaudara ya bata maganin da zai gusar mata da hankali yace shine zata fara sha kafin taje gida haka ta shanye tana jin dadi dariyar mugunta yayi mata mintoci kadan maganin ya fara dibarta dagan ta fara ganin ba dai-dai ba haka ya tsaya yana kallonta har takai karshe baiji komi ba ya dauketa cak ya shige da ita cikin bathroom haka ya cire mata komi na jikinta ya fara wulakanta mata rayuwa A uzubillahi Allah ka tsare mana imaninmu agasky Jamila kin halaka da yawa Allah shi kyauta.

Tabbas yasamu abunda yaso kuma gsky bazai barta haka ba dole ya mallaketa ya maidata wurin hutawarsa koda ta dawo hayyacinta gaba daya taga jikinta ya canza cikin rikicewa tayi hankalinta tashe take duba jikinta lkcn da ya shigo kallonta yayi cikin shauki yace”hakika aiki zaiyi kyau don aljanu suka tafi dake sukayi aiki akanki don haka ki tashi ki shiga kiyi wankan tsarki don sun tabbatar mani sun sanya maki duk wani maganin acikin jikinki tashi tayi jiji ba kwari ta shige batare da tace komi ba.
Shikuma wani smile yayi na jin dadi don ya ma fahimci ta yarda dashi don haka zai kara mata mallakar ta sosai koda ta fito ta kintsa kanta cike da mamaki haka ya bata magani duk na mallakarta bawai wanda taje nema ba tuni komi ya canza haka ta tafi jikinta duk asanyaye ta tafi kuma yace mata idan ta kara samun lkc ta dawo kudin data bashi bai amsa ba yace ta bari tukunna haka ta tafi bata shiga katsina sai wajen karfe 6:30 sannan ta isa gida agajiye.

Umar koda wasa bai fadi ma Yusuf ya hadu da Jamila akano ba domin ya tabbatar bai san da tafiyarta ba don haka shima baice komi ba taje can tayi ta sakarcinta.
Akwana atashi asarar mai rai bikin Umar dasu Nabila da Fatima yana ta matsowa don gaba daya gidajen nasu ya fara zama busy ga ita kuma cikin Hawwa ya kai wajan wata hudu gaba daya ta canja amma har yanzu ita Jamila tunaninta kibace kawai tunda ba yawan haduwa sukeyi ba sai in takama kuma Hawwa na samun kulawa sosai ta ko ina don Hjy Kaka kullum sai sunyi waya taji lfyrta haka umma duk da Asabe tana wurinta amma hankalinta na wurinta.
Zaune suke alambun gidan suna duba wani abu a lapton dinshi shi da ita dariya kawai Hawwa takeyi.ita kuma yau tana gida bata fita ta zagayo cikin lambu zata zauna taji dariyar Hawwa a hankali ta dawo baya don jin meke faruwa karaf kunnenta yajiyo mata Yusuf nacewa nifa dasu Umma zasu yarda da bazaki Haihu anan kasar ba sbd cikjn nan najikinki ina jin shi har cikin raina.”ai walhi ni nafi sha’awar kasata bana son yarana su zama bakin haure dariya suka sanya gaba daya yana ja mata hanci` faduwar cup din dake hannun Jamila ya dawo dasu kallon wurin da sukaji karar, cikin sauri ya tashi don yaga meke faruwa?lokacin da yaje yaga shigewar Jamila cikin gidan……..

Masha Allah mu hadu next page insha Allahu ina gdy all fans din Tun Ina Karama ina yinku sosai walhi ????????????
Takuce sa’ar mataaaa????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

TUN INA https://chat.whatsapp.com/JQ7XP7WslctGxTdw5G7OQw
TUN INA KARAMA????????????????????????????????

*By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com*

PAGE 40

……………Yusuf sauri yayi ya bi bayanta’ itama cikin sauri da gudu gudu ta shige main kichen din dake gidan, shima binta yayi `rufe kofar zatayi yayi sauri ya tokare kofar da kafarsa yana shiga shima rufe kofar yayi binta yayi tana ja da baya har saida ta tokare da bango sanna shima ya isa ya zagaye ta da hannuwansa daf da daf suke sai nishi takeyi saboda gudun datayi “Jamila me kika labe kikaji??bata daga kanta ba tace” ban saniba amma komi ke faruwa naji wallahi kuma duk munafurcinku najishi don haka Yusuf babu wata barazana dazakayi mani ayanzu dai takarashe magana cikin rashin kunya.”tabbas kinji kuma banyi mamaki ba don kin labe kinji amma inaso kisani wallahi billahi idan har kika karayin gangancin zubda ma yarinyar nan ciki to zakiyi nadamar da har ki mutu bazaki manta ba don walhi Jamila zan iyayin komi akan cikin yarinyar nan kada kiga wancan an kyaleki to walhi wannan karon bazan yarda da iskancinki ba zan dauki tsatsauran mataki akanki don haka daga yau kinsan Hawwa nada ciki dama ba’a boye maki ba sai don mugun halinki to yau kinji kuma dole idon kuwa ya koma kanki.daga nan ya cire hannuwansa ya juya ya bude kofar ya fita.durkushewa tayi wurin ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba.

Koda ya koma wurin Hawwa ita sanyin wurinma har yasa ta kwantar da kanta akan kujerar ta fara bacci don yanzu bata da wuyar bacci.motsin shi dataji yasa ta bude idanuwanta da kyar hannu ya mikamata alamar tataso mika mashi nata hannun tayi ta mike tattara abunda ke wurin yayi ya dauka ya kamata suka barwurin koda suka shiga part dinshi zaunar daita yayi ya ajiye lapton dinshi da ruwan dake hannunsa shima zama yayi daf da ita ya kama hannuwanta yace”ke daga bari in dawo har kin fara baccinki.murmushi tayi tace”yauwa wai me kaganine najika shiru kamar ma cikin gid kashiga??kallonta yayi cike da tausayinta da kaunarta yace”Hawwa , u have very carefull about wannan cikin don Jamila yanzu tasan kinada ciki itace tazo dazun kuma taji duk maganar da mukeyi dake”cikin fargaba da tsoro tace “what!!?kana nufin labewa tayi??yanzu u know everthing about me?tab ai walhi gidan umma zan koma.da sauri ya dago kansa yace” walhi Hawwa ba inda zakije ko wancan cikin dakikaga tayi nasarar zubda shu Allah yasa bazai taka kasa bane don haka bani so kikara wannan maganar, to inkince haka menene amfanin Baba Asabe badon ta kular mani dake ba??to menene damuwarki kedai kawai mu cigaba da rokon Allah kariya daga duk wani shedanci nasu.nisawa tayi tabbas maganarsa gaskiya ce amma bakomi kamar yadda yace Allah to Allah shine kawai zai bamu kariya.kallonsa tayi sosai tace”babu komi Allah ya shige mana gaba “Ameen ya amsa mata daga nan kuma suka shiga wani babin suka saki wannan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button