HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Jamila saida taci kukanta mai isarta sannan ta tashi ta nufi part dinta tare da sarkesarke azuciyarta inda zata samu mafita dama kuma wannan matar ta Asibiti tasa mata ido kuma ta bata dama ta karshe akan aikinta wadda bata ma san ya akayi issue din ya fita ba daga cikin family dinsu ai ko baka ce ba Yusuf bazanyi kokarin zubda cikin nan ba sbd na rabu da wancan bokan saidai koda ta haihu bazan barta ta zauna lafiya ba don nice yakamata ace nafara ajiye maka yara ba wannan yarinyar ba nasan yanda kake son yara ida har na haihu dakai dole in amshi wannan soyayyar taka amma ba komi muje zuwa.

Bikin su Nabila saura sati uku don haka ita kanta Hawwa taki zama ta huta don duk wani shiri da akeyi da ita akeyi shiyasa suka zama busy gaba dayansu hankalinsu nakan bikin don yadda suka shirya shan shagali hhhhh ai Umar dangata ne mata biyu alokaci daya ai sai namijin duniya shi kanshi Yusuf baya kaduna baya katsina yana tayin abunda ya kamata.mummy taso adawo da komi gidanta na dangane da bikin Nabila amma daddyn su yace ai wadda ta riki diya ita keda biki don haka yazama dole tabar wannan maganar kuma yana so ta shiga cikin hidimar ayi komi da ita baya son akawo mashi wani korafinta don haka ta kula sosai.haka ta hakura ta fara shiga cikinsu amma ba ranta naso ba amma itama tafara ganin yanda mijin nata ya fara canza mata amma zatayi maganin abun don tasan asiri sukayi masa amma zata bisu har agama komi.haka ta kira Jamila ta fada mata kada ta nuna komi su bisu kafin agama bikin sannan asusan abunyi harda maganar cikin Hawwa ahaka suka bar maganar suka wayance aka cigaba da hidima dasu amma kowa na mamakin canzawarsu ciki ko harda Yusuf yanda yaga Jamila na hidima sosai yayi mamaki.

Ita ko Ammi cema Umma tayi ta kula sosao don Hjy Mariya shu’umace kada ta sakar mata komi.abangaren mamk kuma itama hidima takeyi tsakaninta da Allah don idanma baka sani ba bazakace ba itace mahaifiyar Fatima ba su kansu yan uwan mahaifiyar Fatima suna yaba mata sosai da kokarinta, Abba kuwa cewa yayi baya son Daddy yayima Nabila komi saboda shi zaiyi mata don Nabila diyace saboda karamcinta Umma kuwa tayi kokari sosai wurin inganta ma Nabila rayuwa kuma tayi rawar gani haka komi ke tafiya cikin tsari.

Umar ne yace ma yusuf wai yaga matarshi ta canza kodai komi ya daidaita ne??murmushi yayi irinnasa yace”nima haka nagani Umar Allah dai yasa da gaske ne har zuciyarta don walhi Jamila abun tsoroce daga ita har mummy dariya yayi shima yace”Ameen wai ya kuka kare dasu Fatima ne??”eh yanzu dai nace masu komi sukayi da masu decoration din sai su sanar mani amma dai har yanzu basuce komi ba.”to shikenan ai sai mu sauraresu “haka ne yanzu ni inason zuwa in dauko Hawwa mu wuce gida don idan nabarta bazata dawo yanzu ba sai tagama wahalar da jikinta sannan ta dawo gida ta hanani sakat.dariya Umar yayi sosai yace” ai naga yanzu Hawwa tana maka gashin gyada a hannunka kai mashi bugu yayi shima yace”ai sauran kiris kaima agasa maka gyadar dariya sukayi hhhhh gaba daya sannan suka kashe sukayi sallama sai sun hadu goben.koda Yusuf yaje gidan Umma yasamu Granny ta iso tana tare da Hawwa tanata zolayarta wai wannan cikin nata daga gani yan biyu ne ita kuma Hawwa nacewa asheko zan baki dayan don ni ina zan iya renon yan biyu dariya sukeyi gaba dayansu sallamar Yusuf ce ta katsesu amsawa sukayi gaba dayansu suna kallon kofar Granny ce tace”ashe Isuhu ne shigo to kaji abunda raguwar matarka ke fadi”haba Granny sai kace ke ai nasan ni matata ba raguwa bace zama yayi kusa da Granny yace ashe kin iso tun yau zaki wani kama kizo kai mai bugu tayi tace”kaji mani yaro da shiga sharo ba shanu to nida kai wafi mukami agidan nan??dariya sukeyi sosai”to naji masu gida nima dai ai dadin abun inada gidan da kuma iyalina gama daya nan gabanki kina kallonta “yauwa to wai ina dayar matar taka mai kama da basamudiya??” Haba Granny ai ni matana duk yan daidai ne banida katowa ko wannan da kikagani cikine ke kara sata girma amma zata dawo daidai bari ta dai ta haihu.”hhhhhh naji to amma banga Jamila ba”kuma fitarta kenan kika iso Hawwa tace mata ina ganinma gidan mummy taje “ooho ai ina zaton tana nan tana nuna mugun halinta don bata bar kowa ba
ba wanda yasake magana tashi Yusuf yayi zai fita don yasan ma ko yace ma Hawwa ta taso su tafi wannan tsohuwar ba bari zatayi ba.kallon shi Hawwa tayi tace” Yayanah ina zuwa kuma??”kisameni wurin mota fita zanyi bai yujoba yaji Granny nacewa ooni Hauwa’u kinji zamani ita tace ina zaka shikuma yace ki sameni wurin mota ko kunyar wannan abun dake gabanta bata ji zata bi miji haka.kafin ma ta gama korafinta Hawwa ta kai kofar tana dariya hhhhhh…….????????????
Sa ido irin na Granny tashi tayi itama tabisu tana cewa bari in biku inga ida zaku…….

Masha Allah ko ko ni Granny da bani da aiki sai binsu ina kawo rahoto to yau na tsaya miji da mata sai Allah
ban ciki shiga tsakaninsu ba????????sai Granny yar rigima????????

Ku biyo ni next page masoyan Tun Ina Karama fatan Alkairi aduk inda kuke Iluv u too much my all fans

Takuce Sa’ar mataaaa????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

TUN INA http://saadatu99gmail.com!
TUN INA KARAMA????????????????????????????????

*By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!*

PAGE 41

……………..Koda Hawwa ta isa bakin motar shikuma har shiga ya zauna, dafe murfin motar tayi ta tsaya gabansa. kallonta yayi sosai ta yanda cikin nata ke kara girma tana kara barkewa “ai nasan tunda kika hadu da tsohuwar can konace kizo yanzu mu wuce gida bazata barki ba.murmushi tayi tace” ai yanzu haka ma tana baya na inaga wani ya tsaidata shiyasa bata fito ba”nasani ai amma ai kema baki kyauta ba cewa nayi fa ki jirani inzo in kawoki amma shine kika taho abunki bayan ina fada maki yanzu bana son kina tuki amma naga alamar kema yanzu kin fara yimani abunda kikaga yar uwarki nayi mani kin fara kin jin maganata ko??ya karashe maganar cikin daure fuska.”Ayya hubbynah walhi kakace datace mani ta iso kuma ninaga kamar bazaka shigo da wuri bane shiyasa nace ma Baba Asabe mu taho kasamemu amma nayi laifi afuwan ni banyi don bata maka raiba kuma ni taya zan ki jin maganar mijina takarashe magana cikin shagwaba data zame mata jiki.sake kallonta yayai yace”to yanzu ina zakuje da Nabila in ta dawo??”wurin matar nan zamuje mu karbi dinki sannan mu shiga kasuwa don akwai sauran abunda zamu saya nida Nafisa.”kai wai su basu kyaleki basa ganin halin da kike ciki nidama indai kun hadu ku ukun nan baku sauraren komi amma ba komi ni nafi kowa kosawa ayi bikin nan ko kin samu natsuwa haka nan idan kowa tana gidan mijinta ai naga yanda zakuyi wannan shiriritar, to walhi zan fada maki kada ki hau motarki kuma bana son tukinki zan kira Nabila na fada mata kuma da anyi magrib zanzo mu tafi gida kibar Asabe nan ta zauna har agama hidimar nan.”Ranka shi dade angama baisan lokacin da dariya ta kubuce masa ba gaba dayansu dariyar sukeyi daidai lokacin motar Jamila ta kunnu kai cikin get din gidan dariyarsu kawai take gani abun burgewa wani irin abu ne ya bugar mata zuciya haka nan ta danne don maganar mummyn ta kawai take bi wuri tasamu tayi parking ta fito kamar zata wuce ta shige sai kuma ta fasa ta isa wurinsu jin tahowarta yasa Hawwa cikin kissa ta juyo tana cemata “Aunty Jamila sannu da dawowa yake tayi tace ” yauwa Hawwa Nabila bata dawo bane??”eh walhi amma ta kusa fitowa lecture din.ok tace kallonshi tayi wanda shi tunda suka fara magana kallonsu kawai yakeyi kamar daga sama yaji tace” barka yallabai cikin mamaki ya amsa da “yauwa kin dawo kenan?” Eh na dawo dama gidan mummy naje.”good yace daga haka tace ma Hawwa sai kin shigo “ok to tace mata atakaice.koda Granny ta ga Jamila zata shigo falon saita koma kan kujera tana murmushin jin dadi don tunda ta tsaya akan window nan ba abunda bata ganiba tsakaninsu tunda ta biyo Hawwa nan ta tsaya kasancewar babu kowa a falon Jamila na shiga tayi sallama ganin Granny a falon taji faduwar gaba don tasan karawarsu ba dadi amsa sallamarta tayi cikin karfin halin Jamila tace” Granny ashe kin iso ita kanta Granny saida tayi mamakin canjin Jamila bata gama mamaki ba saida taga Jamila tazo wurinta ta zauna tana gasheta itama barin mamakin tayi tana amsa mata cikin jin dadi don dama duk cikin jikokinta ita kadaice ta banbanta amma kuma ai ba mamaki idan Allah yasa ta canza itama zatayi farin ciki sosai to amma fa Granny bata da barin bakinta shiru kamar daga sama taji Granny nacewa “ke ya akayi kika shigo kika bar mijin naku waje?kamar an soketa taji maganar Granny azuciyarta aranta tace wannan tsohuwar nason tarwatsani yanzu ai zama da wadancan cingum din fitina ne cikin karfin hali tace” ai Granny tare nazo nagansu kuma sai in zauna ai bansan sirrin da sukeyi ba mata da miji”hmm ke Allah na tuba ma yawonki ma ya barki ki kula da miji ai saidai kiga anayi tunda ke baki gaji zama ba gidan miji sai gantali awaje uhum’ nidai nafada maki kina ji kina gani yarinya karama zata kwace miji ahannunki ke kuma gaki nan ganda memiya baki san komi ba yo Allah na tuba ni Hawa’u ai isuhu inda ke kadai gareshi da yanzu rayuwarsa ta shiga garari don ke baki san wata soyayya ba sai son zuciya.tabe baki tayi tana jin maganganu Granny har cikin ranta amma ya ta iya dole tayi hakuri har lokacinta yayi ta tabbatar da kowa sai ya gane kurensa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button