HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Fatima ce itada kawayenta daya daga cikin kawartace ta amshi wayar Fatima tana duba pics Suwaiba kallon Fatima tayi tace”wai wannan shine yaya Yusuf?kallon pic din Fatima tayi tace”eh shine bakiga pics dinshi da yaya Umar ba kuma gashi nan ma da matarsa Auny Hawwa rike baki Suwaiba tayi tace”nifa ma dauka kanwarsa walhi amma dai sunyi kama sosai”eh ai dole suyi kama tunda yan uwane kuma kanwarsace itama”kice ku gidanku auren zumunci kawai kukeyi??”A’a kawai dai Allah yasa duk yan uwane mazajen namu dariya sukayi gaba daya can kasan zuciyar Suwaiba tana saka abubuwa da yawa akan Yusuf haka cikin hikima ta tura pics dinsa awayarta don gaskiya taji yayi mata arayuwa kuma irin mijin datake so don haka ita ma zata gwada sa’arta babu ruwanta dawani zumuncinsu kuma kawancesu da Fatimar ma ba kallonsa zatayi ba hankali kwance zatayi komi.

Kamar yadda suka tsara washegari sukaje wurin masu decoration sukayi setting din komi nan Fatima batare da wani tunaniba taba Suwaiba No Yaya Yusuf don su gama magana amsa tayi tare da samun nasarar bukatarta lokacin data kirasa yana daidai danja a an tsaida su yana kokarin dagawa danja ta basu hannu sai kaiwa ya ajiye wayar ya wuce kallon Fatima tayi tace bai dauka ba kodon bakuwar number ce”gskiya saidai idan baya kusa amma idan yaga miss call zai kira nasani.tabe baki tayi tace”ai shikenan inya kira nayi masa bayani “to hakan ma yayi komi kenan saiki fada masa.maji yanda kukayi.farin ciki ne baibaye da zuciyarta koba komi dama ta farko tafara samuwa dama shine babbar matsala rashin number sa amma yanzu komi mai saukine haka suka bar magana.shikam Yusuf baima sake bi takan kiran da akayi masa ba saboda shi yama manta hidindimu shn masa yawa kasancewar yanzu duk wani aikin company Umar ya sakar masa yasa abun yayi masa yawa bashi da lokacin kansa sosai

Jamila da Hawwa kuma Yusuf dubu dari biyar yaba ko wacen su na hidimar biki kuma yace idan akwai wata mai bukatar wani abu tayi magana sai abata Hawwa dai cewa tayi” babu ita ko Jamila koba komi bazata barshi haka nan ba saita kara amsar wani abu tunda yaushe rabon data amshi kudinsa don bata son raini wai acewarta hhhhh

Kwance suke adaki shida ita yana fadi mata yanda tsare tsaren company ya canza tana dubawa tana yaba kakarin mijin nata wajan karfe 11:15 suka ji wayar Yusuf na kara cikin mamaki yace “kira kuma yanzu wayene batare da komi ba Hawwa ta mika masa wayar tana cewa number ce ma ba suna bai kawo komi aransa ba ya karbi wayar ya daga muryar mace sukaji tace Assalamu alaikum.bai amsa sallamar ba ya zaro ido cike da tsoro itama Hawwa bude baki tayi ta bisa da ido cikin tuhuma hhhhhhh muje gatan gatanan ku fans???

Masha Allah kuyi hakuri da wannan matsalar nepa ce insha Allah sai mun hadu next page

Iluv u too much all fans TUN INA KARAMA Takuce Sa’ar mataaaa????????????????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

*By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!*

PAGE 42

………………Kallonshi takeyi sosai, shikuma yana amsa wayar Suwaiba adabarce yake magana don gaba daya hankalinsa ya tashi ita kanta Suwaiba tasan baya cikin hayyacinsa daga jin yanda yake magana kasan babu natsuwa’ dariyar mugunta tayi ta kashe wayarta dora wayar akan kirjinta tayi ta rungume tana jin dadin muryar Yusuf akunneta koda ba wata magana sukayi ba amma ita taji dadin hakan har cikin zuciyarta.Hawwa na kallon ya ajiye wayar ta tashi zata bar dakin shima saurin tashi yayi zai rikota juyowa tayi afusace tace”kada kayi wani yunkurin tabani amma inaso kasani koma wacece wannan kanada alaka da ita mai kyau tunda har ta iya kiranka awannan daren saidai wani abu daka manta kasanar mata cewa kana da iyali don haka tasan lokacin kiranka tana fadin haka ta bude kafa ta fita dakin binta yayi da kallo don shi abun ma ya daure masa kai amma ita ma wannan yarinyar ai tayi hauka gashi yanzu ta hada mashi fitinar da baisan ta ina zai kare kansa ba don yanzu Hawwa bata cika bashi uzuri ba.zama yayi yana tunanin ta ina zaifara kare kansa.ita ko tana fita dakinta ta shige tasa key zama tayi itama tana ganin yaushe Yusuf ya canza da mata zasu fara kiransa cikin dare haka amma gaskiya ya bata mamaki amma ba mamaki namiji ne shima zai iya aikata komi hmm amma Yusuf ka tafka babban kuskuren yaudarata don ba Hawwa daka sani abaya bace zan iya daukar komi amma banda cin amana wato dama maza da yawa suna fakewa da biki ahadu da yanmata kala kala ko don fashion to bazan ba kowace wannan damar ba daga yanzu nasanya maka ido.

Yusuf na tashi da safe ya nufi sashen Hawwa do ganin ko ta tashi ganinta kan cafet yayi tana sallah murmushi yayi ya juya ya rufe mata kofar saboda dama yasan Hawwa bata wasa da ibada shiyasa yarinyar take kara shiga ransa.tabbas taji shigowarsa amma me zaiyi mata don yanzu haushinsa takeji koda ya dawo masallaci shima bai koma ta wurinta ba komawa yayi dakinsa wayarsa ya dauka ya kira number Fatima bugu biyu ta dauka cikin ladabi tayi sallama sannan ta gaishe shi bayan sun gaisa ne yace”wai Fatima wata ba number sa ta kirashi tsakar dare har tasanya Hawwa tana fushi dashi, cikin mamaki Fatima tace “Suwaiba ce Yaya amma gaskiya bamuyi da ita ba zata kiraka da tsakar dare ni tunda ma ta kira lokacin muna tare baka dauka ba nace ta bari zaka kirata amma kayi hakuri zan mata magana” ok zan turo maku kudin ai ta fada mani amma ki kira Hawwa kiyi mata bayanin komi kafin ta rikice mani”insha Allahu yaya zan kirata ahaka sukayi sallama yace ta gisheda mutanen gidan.

Tashi yayi don ya koma wurin Hawwa yana shiga yaga bata parlon sai ya nufi bedroom yana shiga yaga bai ganta kwance ba motsin ruwa yaji a bathroom isa yayi bakin kofar ya bude zaune ya sameta tana wankin panties dinta cikin hanzari ya isa wurinta ya amshi wanda ke hannunta kallonshi tayi shima kallonta yayi bude baki tayi zatayi magana taji yace”nasan baki jin maganata amma ai ni ke wanke maki tunda gaba daya an hanaki komi daga bacci sai sallah sai kici abinci amma kwata-kwata yanzu kin canza Hawwa ai inace ko kowa zaiyi fushi dani amma banda ke kuma ni ya isa kiyi shedata akan mace kinga dai bansan yarinyar nan ba kuma kawar Fatima ce banda wani masaniya atare da ita nasan dai ni nace idan sungama komi su kirani sai in tura masu kudin amma bansan akwai wadda zata kirani ba tabbas ta kirani lokacin ina hanyar dawowa gida amma ni na manta cewar wani ya kirani ma shine tayi mani wannan kiran amma wallahi bansan komi game da ita ba plsss Hawwa ki yarda da dani ya karashe magana yana hade hannuwansa alamar rokonta yakeyi.tabbas ta yarda da maganarsa amma duk da haka zatayi taka tsantsan dama ko wacece acikin kawayen Fatima zakuma ta bincika kallon shi tayi fuskarta ba yabo ba fallasa tace”ya wuce, miko mani kayana in karasa wankewa makale kafada yayi alamar bai yardaba yace”haba madam kibarni inyi aikina mana kodai ba’a daina fushin dani ba??sakar masa kayan tayi don bata son wata doguwar magana tsakaninsu haka suka gama suka fito harda yi mata wanka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button