HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Jamila yau take son zuwa wurin malaminta don tana da bukatarsa saboda yayi mata asirin idan har tana da bukatar namiji to saidai ta sameshi yabiya mata bukatarta to gaskiya tana son ganinshi ga kuma hidima agidansu ga tsohuwar nan idan bata ganta ba ta damu da tambayar tana ina ne tana wannan tunanin yanda zatayi ta bar gari sai dabara tazo mata tsalle tayi tace yauwa shikenan shikenan bari kawai in shirya mummy kadai zancema zanje in karbo magani.tashi tayi ta shirya cikin sauri tagama komi fitowa tayi part din Yusuf din ta nufa tana isa da sallam ta shiga tasamesu zaune ita kuma Hawwa tana shan kunun gyada ahannunta don yanzu tafi sonsa fiye da komi Jamila jitayi kamar ta shaketa saboda yanda tagata shishigema Yusuf daurewa tayi ta zauna kusa da Yusuf itama cikin yaudara da kisisina tace “barkanku da safiya murmushi Hawwa tayi tace ” barka dai Aunty Jamila nayi tunanin baki tashi bane ba.”A’a na tashi kallon Yusuf tayi tace yallabai ina son zuwa workshop ne kano shine nazo in fada maka ba Yusuf ba hatta Hawwa abun ya daure mata kai wai Jamila ce da tambayar zuwa wani wuri kuma ma harkar aikinta lallai duniya juyi juyi ce kwado ya fada ruwan zafi ita kanta Jamila ta tsargu amma sai ta faske kawai.”Yusuf cewa yayi adawo lfy kawai daga nan bai kara magana ba ya tashi ya shige cikin bedroom dinsa ita kuma ganin haka yasa saboda tsabar yaudara ta matsa kusa da Hawwa jawo flask din kunun ta tsiyaya tasha sannan tayi sallama da Hawwa ta fita tana jin dadin yanda bata samu wata matsala ba.

Koda ta isa wurin malamin yayi murnar ganinta don shima akame yake haka suna ganin junan suka makalema juna suka shiga badalarsu ya gurjeta son ransa haka suka wuni suna abu daya saboda ta isa da wuri sannan kuma bata biya gidan mummy ba itama a waya ta fadi mata komi kafin ta wuce.koda Hawwa taje gida Umma tace ma Granny Jamila taje aikine.Fatima kuwa ta kira Hawwa tace tayi hakuri kashedi tayi mata tace kada takara ba kowa number mijinta.

Yusuf ya fadama Umar abunda ya faru tsakaninsa da Suwaiba don ya fahimci yarinyar bata da kunya Umar kam dariya yayi sosai yace “bros kayi kasuwafa tun yanzu don haka ni bana cikin wannan rigimar hhhhhh” kaifa dan iskane to wallahi zance ma Hawwa kai ka hadani da ita hhh”kaji matsoraci to kafada mana.

Malamin Jamila ya tabbatar mata da cewa shifa gaskiya bazai rabuda ita ba don yanzu ma ya fara jin dadinta kuma baya son wata alaka ta kara shiga tsakaninta da mijinta har lokacin daya bata damar hakan.ita kuma dayake sokuwace ta amince da hakan Allah ya tsare mana imaninmu Ameen ya hayyu ya qayyum.

Akwana atashi asarar mai rai yau saura kwana biyar bikinsu Nabila amare kam sun hadu don gaskya Umar zakaji jiki wurin amaren nan naka hankali kwance akeyin komi dole Yusuf yasa ma Hawwa ido
amma kullum sai yayi mata korafin tana wahalar masa da yara ita bata jin komi hidimarta kawai takeyi dole in angama bikin nan duba mashi lafiyarta Yusuf yana so yaje kaduna wurin partyn dasu Fatima suka shirya shikuma Umar ya tsaya wurin Nabila amma rigima ta kaure tsakaninsa da Hawwa ita ko Fatima tasamu Suwaiba tayi mata warning sosai akan Yusuf amma ko daya bataji ba tayi aniyar samunsa ako wane hali.

Shigowa yayi ya iske ta jawo akwati tana shirya kayanta kallonta yayi da kyau ya hango tsabar fitina a idanuwanta.daure fuska yayi cikin masifa yace “kimaida kayan nan ko ranki yayi mugun baci!!!” Bazan maida ba wallahi sai naje kaduna kuma bazan tsaya wurin program din Nabila ba wanda zaka shi zani idan gaskiya ne me zai hana shi Yaya Umar din ya tafi kaduna kai kai katsaya nan amma sai kai ka tafi saboda kana budurwa acan ni kabarni nan cikin tsiwa itama take magana daga hannu yayi zai sharara mata mari!gam yaji an rike masa hannu juyowa yayi yayi masifa wanda yaga ni ne yasa ya sunkuyar da kansa kasa………

***************
Masha Allah gaskiya yau Yusuf baka kyauta mani ba amma ba komi zamu hadune????????????Ina ma kowa ftn Alkairi all fans Tun Ina Karama!!!

Kakus kai duk meenah din dake cikin fans din Tun Ina Karama ga page nan naku ne kuyi yanda kuke so dashi sai mun hadu a next page.

Takuce Sa’ar mataaaa????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

By Sa’adatu Bello
Saadatu99gmail.com!

 

PAGE 43

………….Baba Asabe ce tarike masa hannu batare datace masa komi ba ta nufi hanyar fita rike da hannusa, binta yayi shima kamar wani karamin yaro ganin haka yasa Hawwa itama ta fada kan gado ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.Asabe bata zame dashi ko ina ba sai part dinsa aparlo ta zaunar dashi` sannan ta isa wurin fridge ta bude ta dauko robar ruwa hade da kofi tazo gabansa ta tsiyaya masa ta mika masa’ amsa yayi batare da musu ba ya kafa kai ya shanye ruwan ya ajiye kofin ajiyar zuciya ya sauke! ganin zuciyarsa ta fara sanyi yasa Asabe ta matsa kusa dashi cikin sanyi murya tace “Alhaji karami meyasa zaka biyema mata??har kana kokarin kai hannunka gareta? haba don Allah kadaina wannan halin idan kasaba kai hannunka jikin mace to bazaka bari ba, kuma raini zai shiga tsakaninka dasu ko Jamila dakake bugu ba daidai bane ita kuma wannan dole kayi mata uzuri tunda kana ganin halin datake ciki ko wane ciki da irinsa don haka karinka hakuri da ita kada ka dauki wannan halin` kaga dai wannan abun ba halin gidanku bane tunda kake da Abbanku ka taba ganin suna sa’insa bare har kaga wani rashin mutunci a tsakaninsu? to wallahi kadaina wannan abun kai kasan idan har Ummanku taji wannan to ranka zai baci sosai don haka kaje ka lallashi matarka ku zauna lafiya komi tayi maka kayi hakuri don Allah kabar maganar bana son in kara jin wani abu tsakaninku,nisawa yayi yace” nayi kuskure amma zan kiyaye insha Allahu` Baba kiyi hakuri kema hakika Hawwa ta tunzurani amma nima banyi tunani ba dana biye mata amma zan gyara ayi hakuri ya karashe maganar yana sunkuyar dakai alamar jin kunya, murmushin jin dadi tayi tace “masha Allah tashi tayi ta fita`ita ko Hawwa tunda suka fita data fada kan gado kuka kawai takeyi mai tsuma zuciya bayan fitar Asabe tashi yayi shima ya nufi part din Hawwa yana shiga tun daga parlo ya ke jin kukanta mai tsuma zuciya har cikin ranshi yake jin kukanta cikin sauri ya shiga bedroom din ya isa inda take, kwance birkito ta yayi ya rungumeta ajikinsa yana bubbuga mata bayanta kamar wata karamar yarinya shima jin shi yakeyi kamar ya fashe da kukan.” Hawwa don Allah kiyi hakuri ki daina wannan kukan bana jin dadi kuma ki kwantar da hankalinki ke kin san bani da wata matsala game da mace kin san bata su nakeyi ba amma haka kawai kike tada hankalinki kinsan ni naki ne har abada saboda banida lokacinsu don haka ki natsu ki mu fuskanci juna don Allah.”cikin kuka tace wallahi Yaya baka sona yau kaine harda daga hannunka zaka bugeni.sauri yayi ya rufe mata baki yace”ki bar maganar nan nima nasan nayi kuskure amma tuba nakeyi kuma maganar zuwa kaduna nima na barta zan nemi Umar muyi magana kada ki kara maganar komi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button