HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Saida ya tabbatar dacewa ta hakura kuma ta saki ranta sannan ya fita ya bar gidan domin zuwa wurin Umar bayan ya fitane sannan Asabe ta shiga wurinta tana zuwa ta sameta zaune da sallama ta shiga amsawa Hawwa tayi murmushi tace”Baba Asabe ki shigo mana karasawa tayi cikin bedroom din zama tayi kusa da ita kallonta tayi daga gani kasan damuwarta ta ragu cikin zolaya tace”uwar dakina angama rigimar ai wallahi bansan kishinki ya kai haka ba don naga bakiyi data gidanki sai wadda bata shigo ba.rufe fuskarta tayi tace”kai Baba ai ni ba kishi nakeyi ba kawai dai haka nan nayi hakan.dariya sukayi gaba daya, Asabe tace”Hawwa ki rinka yima mijinki uzuri kinga dai komi yana yi maki iyakar kokarinsa baya son abunda zai taba rayuwarki amma kuma kina so har ki kureshi kisa yayi abunda baiyi niyya ba akanki babu dadi ai ba masifa yakamata kiyi ba koda kingani ko kinji kauda kai yana daga cikin biyayya ga miji bakomi zakiyi magana ba domin shi kawaici yana sa namiji yaga kimarki da darajarki kuma shima dole ya raga maki amma namiji ya fada ke ki fada babu kyau ga macen kirki kuma ke ba tarbiyyarki bace don haka bana son in kara jin irin wannan tsakaninku.itama sunkuyar da kanta kasa tayi ta amsa da “insha Allahu ba za’a sake ba ” to haka nake sonji Allah yayi maku Albarka”Amin ya Allah

Koda Yusuf ya fada ma Umar abunda ya faru shima dariya yayi ma Yusuf sosai yana tsokanarsa daga karshe dai yace ya yarda shi zaije don kada ya jawo mashi magana kada yana so yaci amarcinsa amma kuma ya jawo masa magana don da tsautsayi yasa ka dora hannunka akan Hawwa ai da wallahi kasan Umma bazata ragamana ba daga ni har kai to don Allah kayi hakuri nima in shiga daga ciki inj abunda kukeji kashewa sukayi suna dariya.koda Nabila taji abunda ya faru itama tayi dariya sosai tana jinjina rigimar kawartata.

Komi na tafiya yanda ya kamata domin Umar dai na kaduna shi kuma Yusuf yana nan tare da cingum dinsa ko ina yayi tana binsa ita ko Jamila ai sai ta koma yar kallo saboda Hawwa ta tare ko ina hakan ba karamin dadi yayima su Aunty zainab ba domin dama ita ba wanda take shiri dashi acikinsu haka ma mummy Aunty Rabi’ace kawai ta wajansu shiyasa komi nasu gwanin ban sha’awa.

Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya yau asabar akeyin daurin auren Umar Bashir Rano da amarensa guda biyu saida aka fara daura na Nabila karfe goma na safe akan sadaki dubu hamsin sanan suka wuce kaduna inda za’a daura na Fatima.Yusuf yazo yasamu Hawwa tana cikin dakin Umma lokacin tana sanya kayanta amma tana ta mita wai dikin ya matseta sosai yana shigowa ta kwabe fuska kamar zatayu kuka.shikuma fahimtar kayan nata dayaga sun matseta yasa yace”to madam tunda kin zama giwa ai sai ki hakura da sanya kayan haka nan don bana son hancin yarana yazama kin nane mani su.kara bubbuga kafa tayi sauri yayi ya isa gabanta”haba maman yara don Allah karkisa yarana su fito basu gama girma ba.”to su fito mana ai ni dama na kosa su fito in huta komi bana yinsa irin na mutane dariya yayi mata sannan ya kamata ya zaunar da ita bakin gado sannan yace “bari in canza maki kayan don kaduna zamu tafi yanzu ” wayyo hubbynah da gaske dani zakaje tare da fadawa jikinsa “kara riketa yayi sosai yace shiyasa fa kikaga nayi amfani da motar nan mai tintec saboda in gudu da matata kada ma wani yaganki dama Umar ne zaisa mani ido to sun riga sunyi gaba Aunty zainab ce kawai tasan shirina don haka ta kofar baya zamu fita don itace dama tace mani in sameki nan don Umma tana dakin baki” tooooo dama shiyasa tace in maza in shirya zakazo to amma nagode mata tana dariya shikuma yana kokarin sanya mata rigar daya fiddo “to amma da sharadi ko mami bazata san kinzo ba fa” eh na yarda ni dama burina mu kasance tare to amma idan Umma ta neme ni fa “nabar komi wurin Aunty zainab karki damu kwalliya tayi sosai sannan suka shige ta baya inda ya ajiye motar shiga sukayi suka bar gidan batare da kowa yasan fitarsu ba.

Koda suka shiga kaduna ya kira Umar yace masa ya amma zai danje wani wuri sannan ya iso bai zame ko ina ba sai hotel can yaje yakama daki shifa dama da biyu ya taho da matarsa saboda gaskiya abukace yake kuma yau wurin kwana hudu tana kwana gidan Umma itama tana bukatar mijinta amma biki ya dauke mata hankali koda taga sun wuce hotel bataji komi ba haka suka shiga yayi yanda yake so da matarsa daga gani kasan sunyi missing din juna.saida suka ji zam-zam sannan sukayi wanka suka fito zuwa gidan mami mintoci kadan suka rage a daura auren ya iso yati parking nesa da gidan mami ya barta a mota ya kulle ko ina ita kwantar da sit ma tayi ta kama baccinta abunda bai sani ba parking dinshi da fitowarsa akan idon Suwaiba ba don taga zuwan Umar amma babu shi tana nan tana jiransa don tasan dole yazo sai kuma gashi ya iso ajiyar zuciya ta sauke tace” yau tarkona zai kama kurciya by all means shi zai kaini katsina babu wadda zan bari ta shiga motar nan Yusuf dole yau ka saurareni kuma ka karbi soyayyata don ni kadai kazo wurin nan don haka bazan bar wannan damar tawa ta kubuce mani ba.hhhhhh kaji wai wata sabuwa inji yan caca.mutum na tare da matarsa amma ke kina nan kina karanta banza banza wasikar jaki hhhhhhhh….

*****************
Masha Allah sai mun hadu next page insha Allahu don jin ina za’a bar Hjy Suwaiba ko kuma zata samu nasarar bin Yusuf????

Ina mika godiyata gareku all fans Tun Ina Karama wannan page din din na sadukar dashi ga duk wanda yake grp din Tun Ina Karama abu na gida ne kuji dadinku…Allah ya bar zumunci………….

Takuce Sa’ar mataaaaa????????????????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

By Sa’adatu Bello

Saadatu99gmail.com!

PAGE 44

……………Gaskiya Yusuf abun so ne, namiji ne da kowace mace zatayi fatan samunsa amma ya like ma wannan yarinyar tana juyasa son ranta.kallonta Nadiya tayi tace”ai kema Suby kwace goroba ahannun kuturu ai ba aiki bane ke kinsan wayewa da gogewa kinfita amma ki tsaya kina bata ma kanki lokaci ai wallahi danice da yanzu angama.”gaskiya ne amma ai nesa tazo kusa kawata.koda ya shiga anata gaisawa da mutane yan uwa da abokan arziki wurinsu Abba yaje da Daddyn kd ya kwashi gaisuwa suna tambayarsa ina ya tsaya bai iso da wuri ba sosa keya yakeyi yana dariya kawai daga gani kasan akwai magana fauzewa kawai sukayi don sun san yaran zamani hidimarsu sai su.koda ya wuce wurin dasu Umar suke tare da abokansa suna gaisawa Umara kuwa kallon tuhuma kawai yakeyi masa yana son gano wani abu don yasan waye Yusuf amma shima sharewa kawai yayi.

An daura auren Umar da Fatima akan sadaki dubu hamsin itama kamar na Nabila to masha Allah sai muce Umar Allah yabada zaman hakuri da juna.wuri kam ya hada manyan mutane iri iri da yan siyasa manya abundai sai gdy Allah haka aketa hidimar arziki Yusuf da Umar sun shiga wurin mami sun gaisa Yusuf tsab kin bin su umar yayi wurin yin resption samun wuri yayi ya zauna inda yake hangen motarsa da matarsa amma fa ya kunna Umar to wai me yake shirin akatawa ne don dazun yaganshi da shedaniyar yarinyar nan Suwaiba suna magana amma ko idan har ya kula yarinyar nan zan mugun bashi mamaki don ni zan kunna mashi wutar da bazai iya kasheta ba.hankalinta na wurinsa ganinsa zaune shi kadai yana latsa wayarsa tayi mamakin da shi bai je wurin resption din ba koda yake daga ganinsa shi ba mai son hayaniya bane ba.hhhh bata san gadin matarsa yakeyi ba don ita baccinta kawai takeyi hankali kwance don shi kansa Yusuf yasan ya gajiyar da ita.sallamar da yajine ya dago kai ya kalleta cikin yaudara ta zauna kusa dashi baidaice ce mata komi ba “uhumm yallabai kada kace na dameka don Allah ina son idan za’a tafi da Amarya in bika.cikin sauri ya dago ya kalleta ” what!!! Kinga nayi kama da irin yan daukar yanmatan Amarya??? Look ki fita harkata i’m family man, yes inada iyali kuma yanxu haka ina tare da matata saboda haka go back ur business!! Jitayi kamar ya caka mata wuka azuciyarta bata sake magana ba barin wurin tayi binta yayi da kallo yana tunanin wannan zamani abun tsoro ne kana zamanka mace ta haye maka ba gaira babu dalili Allah ya kyauta.shi ya kosa ma abada Amaryar su wuce ko yaje ya huta tare da matarsa don shi baya tunanin zasuje wannan dinner din.koda Suwaiba ta juya aranta tana tunanin wai shi wane irin mutum ne haka?to ta ina zata fara gaskiya akwai aiki gabanta saboda Yusuf ya cika taurin kai ya ya isa yanzu ya fahimceta duk text din datakeyi masa tunda in ta kira baya dagawa amma ace yakasa gane irin kaunar da takeyi masa kuma wai da iyalinsa yazo to ai ita bataga kowa ba ko matan dataga sunzo biko ai bataga alamar matarshi ba tunda tana da pic dinta amma wai kaji shi zai tsarani amma baru in samu Nadiya tayi ma Fatima magana cikin hikima in da matarshi zanji ai inko babu ita dolene mu tafi tare mal bazan barka ba.koda ta samu Nadiya tayi mata bayanin komi sai tace mata karta damj zata nemo mata labarin komi aikuwa tana zuwa wurin Fatima cikin hikima da bariki irin nasu na yan duniya ta tambayeta ita kuma ta tabbatar mata babu matan Yusuf ko daya ai dama su bazasu zoba.dadi taji sosai nasamun labarin da Nadiya ta kawo mata tayi kuma ta shirya yanda xatayi bari dai atashi tafiyar xaigani.gaba dayama shi Yusuf ya manta da alamarinta tashi yayi yaje yasamu Hawwa wurin motarsa sakamakon text din datayi masa tana son shan wani abu shikuma ya manta da ledar drinks din tana bayan boot din motar koda yaje ya bude boot din ya dauko ledar ya bude motar yasameta sai turo baki takeyi ita tagaji da xama murmushi yayi mata yace”sorry my sweet heart ina ta jirane abada Amarya muma mu wuce don munyi waya da Aunty Zainab tace Umma ta tambayeki tace mata kinyi baki kina gida dasu “hmm wallahi umma jinku kawai tayi amma nasan don dai tazama busy ne.kwan kwasa masa gilas yaji anayi kara kwantawa tayi asite din motar tayi shi kuma ya sauke gilas din ganin Umar ne tsaye yasa shi murmushi ” wai bros mekake boyewa ne?murmushi yayi yace “kanwarka ce bude motar yayi don ya tabbatar masa da itace din ita kuma rufe fuskarta tayi da gyalenta tana dariya shikam Umar mamakine ya hanashi magana.kamar daga sama yaji muryarta tana gasheshi kauda tunaninsa yayi ya amsa mata.” Lallai bros abun naku sai kallo babu mai iya maku sai Allah.kama hannunsa yayi suka bar wurin motar sannan suka tsaya bai boye masa komi ba ya sanar dashi.dariya yayi sosai sannan yace”ashe kace yau kun shammaci Umma da Granny lallai to yanzu ya za’ayi ne wucewa zakuyi ko don nasan dai bazaka dauki kowaba?”gaskiya kam amma kasan wannan yarinyar ta zo wai ni zata bi “hhhh kai haba mai mata to ku sauke mani sister ni intafi da ita ” kai amma kai ka iya kiran ruwa “haba akwai wanda yakaika kiran ruwa nida kafin matan nan su fara fitowa bari in wuce ok to nima bari inje wurin daddy din inji yanda ake ciki ” ok to sai kun taho juyawa yayi zai shiga mota shikuma Umar ya tafi kafin ya isa wurin motar yaji an kirashi yana yuyawa yayi batare da ya amsa ba ganin tana tahowa yasa ya fasa bude motar ya tsaya yana kallon mayya irinta koda ta isa bata tsaya inda yake ba saita zagaya site din din da Hawwa take tana kokarin budewa cikin tsawa yace mata”keeee!!!mahaukaciyar inace da kike kokarin bude mani mota???

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button