TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Hawwa dake kwance ta dago kanta don jin an taba motar ganin mace tsaye yasa ta tashi sosai don gane ma idonta tabbas mace ce kuma magana takeyi da Yusuf yasa ta bude murfin motar jin budewar motar yasa itama Suwaiba dawo da hankalinta wurin ganin Hawwa ya tabbatar mata da itace ga kamarsu nan kamar yadda ta ganta a pics ita ko Hawwa mamaki takeyi wacece wannan shikam Yusuf mutuwar tsaye yayi ganin Hawwa ta bude motar shikenan yau kuma ta faru ta kare ya fada acikin ransa.haka nan ya tattaru jarumtarsa yace”madam koma ciki mu tafi “wacece wannan yaji Hawwa tace mashi ” Suwaiba ce taji yabata amsa.”ok Hjy Suwaiba nice meet u gaba daya jikinsu ne yayi sanyi daga shi har Suwaiba din dama zaune take kafafuwanta awaje kara kallon Suwaiba tayi da kyau ta fahimci yar barikice murmusawa tayi tace”Hubbynah dazaka zagayo ta nan da munyi magana.baice komi ba ya zagaya ya yazo kusa da ita ya tsaya ta sake cewa “wash kafata Hubby kalla ka gani yanda ta kumbura tsugunnawa yayi yana kallon kafar tata da tashi xanen lalle yafara dandanna mata kwantawa tayi abayansa tana lumshe idanuwa itako Suwaiba mutuwar tsaye tayi dagowa Hawwa tayi tace baiwar Allah da zakiyi hakuri ki kyale mani mijina ki nemi naki da zaifi maki kyau.kekinsan tsakanin miji da mata sai Allah don haka kada kiyi ganganci da zakiyi dana sani.wani irin kallo Suwaiba tayi ma Hawwa cikin isa tace mata ” yarinya baki da ikon karkatar da zuciyata akan abunda take so don haka kijira zuwan nawa turn din juyawa tayi afusace tabar wurin zciyarta na zafi dariya kawai Hawwa takeyi shikam koda wasa baisan Hawwa tana da wadannan kalamai haka ba ganin Suwaiba ta bar wurin yace mata “to madam mu wuce ko??” Hhhh wasa farin girki
Masha Allah babu nepa kuyi hakuri da wannan sai Allah yakaimu gobe zakujini
Ina maku fatan Alkairi all fans Tun Ina KaramaTukuce sa’ar mataaa????????????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????
©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
By Sa’adatu Bello
Saadatu99gmail.com!
PAGE 45
……………Tada motarsa yayi yabar wurin cike da mamakin matarsa, ashe Hawwa haka ta iya magana? wonderfull!!wallahi Nadiya bazan bar yarinyar nan ba shiko wane irin so yakeyi mata ne? hmm ke nifa danaji tarihin soyayyarsu shiyasa nake baki shawarar janyewa kinga dai irin abunda yafaru yanzu agabansa don Allah ke bakiji komi ba??ki kyaleshi kawai ki nemi wani daidai dake amma wallahi Yusuf bazai iya kula kowace mace ba indai wannan yarinya tana raye kina ganin daya matarsa ma ba abakin komi take ba kuma wayewa da bariki tafiki tunda itama cewa akayi tare da Yusuf a india amma takasa samun soyayyarsa kema kinsa wahala kawai zakiyi.” Hmm haka dai kika gani ni wannan labarin naki bazai dameni ba yazama dole in samu mafita”tab! ashe isaka tana wahalar da mai kayan kara ni kinga ga gawanda zan bi can don nima nayi new catch kinganshi yana kirana wallahi abokaninsu duk sun hadu ki daure kisamu wani ki makale masa mana amma ki kyale wadan can masoyan asali takara she maganar cikin zolaya da dariya tare da kama hannunta zuwa wajen saurayinta saboda an fara fitowa don har ansanya Amarya amotar Ango don yace shi zaikai Amaryarsa.
Basu iso katsina ba sai karfe 4:20 direct gidan Ammi ya wuce ya ajiye Hawwa duk cikin takune don idan ya maidata gidan Umma zata gane tare suke koda ya wuce yace mata idan sauran sun iso zaizo sai ya maida ita gidan Umma ahaka suka rabu batare da kowa yasan shine ya kawota ba don bai shiga ba don yàsan Granny ma tana gidan suna jiran isowar Amarya.kiran Nabila tayi ta fada mata ta dawo domin Nabilama tasan tana tare da Yusuf don haka bata nemeta ba.Granny kuwa na ganinta ta tasa ta gaba da tsegumi wai duk sun tare gidan Umma ba wanda ya shigo nan harda su Aunty Zainab da Aunty Rabi’a maimakon wasu su taho nan dariya takeyi yanda taga Granny ta dage da fada”to wai ni bagani nazoba suma ai suna nan zuwa ke kin cika damuwa ai Amaryar ma bata iso ba ko.haka daia sukaita hirarsu ai fada ai dadi Ammi dai dariya kawai takeyi masu kiran Umma tayi tace ita tana gidan Ammi can ta wuce daga gida Aunty Zainab ko dake kusa da Umma taji Hawwa nata sharota ai tasahi tayi ta fita tana dariya sun gama mamura Ummansu hhhhh.
Basu iso ba sai karfe 5:30 sannan jerin gwanon motocin Amarya suka fara shigowa cikin layin gidansu Alh Bello don nan dama za’a kaita kafin dare yayi awuce da ita gidanta Granny najin ance ga Amarya nan tayo waje tana murna haka mutane keta fitowa anata shiga cikin gidansu Ammi sufa su Suby da akace masu gidansu Umar ne sakin baki sukayi don ganin irin daular dake gidan lallai su Fatima sun dace to ina ga gidanta nanfa suka zama yan kallo gaskiy daga ganin family din nan ba karya akwai kudi dole suke wulakancin mace sai sun zaba amma gaskiya bazan barka ba Yusuf dole nima inshigo in hau daular nan adama dani.
Koda Yusuf ya isa gida yasamu motar Jamila amma sai yayi tunannin ko da motar gidansu take amfani bai kawo komi ba ya shiga cikin gidan don ya gaji so yake ya dan huta kafin anjima kadan ya fita shiyasa ma ya kashe wayoyinsa don baya son takura yana bude parlon yaga ba kowa amma da alama part din Jamilar bude yake har zai shige sai kuma ya dawo da baya ya nufi part din yana taba kofar yajita abude turawa yayi ya shiga atsorace ta juyo tana kallon maia shigowa ganin shine yasa jinkinta ya dauki rawa shiko hayakin da ya turnuke wurin ne yake korewa matsawa yayi kusa da ita yace”Jamila kina da hankali kuwa saboda me kike son maida rayuwarki mara amfanin yanzu wannan abun shine daidai kina so ko kigama da duniya lafiya ina zaki kai wannan shedancin naki???agaskiya baki da hali ko kadan yau fa bikin kanwarki akeyi uwa daya uba dayay amma baki wurin kina nan kina shaye shaye wace irin rayuwace wannan???mai family dinmu sukayi maki kikeso dole sai tozarta su a idon duniya kince sai kin aureni na yarda na aureki amma kin kasa zaman lafiya kullum cikin masifar rayuwa kike kin kasa kwantar da hankalinki ki zauna lafiya nakasa fahimtar menene matsalarki arayuwa?kallonshi tayi da idanuwanta na mashaya tace”kaine matsalata koda na aureka ka taba sona?”taya zan soki baki da abun burgewa bare har aga abun dubawa daga gareki dama nasan wannan sauyin nak ba na Allah da Annabi bane ba tashi tayi kamar zatayi magana sai tayi taga taga zata fadi sauri yayi ya riketa ya zaunar kallonta yayi cikin jin haushi da tausayinta wai ita wace irin mutum ce arayuwa kunsan jini haka kawai yaji yana tausayinta akaro na farko sannan kuma yaji kamar yayi mata kuka saboda halin data shiga irin wannan abun shishar ya kalla ya harbar da shi sannan yajuyo yaga har bacci ya dauketa akan kujerar da ya zaunar da ita baisan lokacin da hawaye suka zubo mashi ba abunka da dan uwa kuma duk zafinsa shi yanada tausayi gaskiya ba kamar Umar ba.matsawa yayi kusa da ita ya kamata ya gyra mata kwanciyar sosai sannan ya bude windows din dakin don hayakin yabfita daga gani ta dade tanaa shan abun sake kallonta yayi ya girgiza kai ya fita ya jawo mata kofar zuciyarsa cike da tausayinta ina ma kana canza ma naka rayuwa mai kyau shikam daya canza Jamila tazama tagari Allah ya shiryeta yasa ta gane gaskiya…