TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Dakin da aka sauke Amarya nan kawayenta suke gaba daya Nafisa ce da Hawwa suka shiga wurin Fatima suna mata tsiya saiga Suby ta shigo ita da Nadiya kallon kallo sukayi da Hawwa kodis bataji komi ba game da Suwaiba saboda ta riga tayi mata wuri amma saboda jan fada irin na Hawwa tashi tayi ta koma kusa da Suby tace mata”kin biyoni kenan amma fa kisani na warning dina dake na karshe shine Yusuf ba sa’arki bane kuma Yusuf nawane ni kadai bazaki samu komi wurinsa ba sai wahala amatsayinki na wayayyar mace maintance ur self agarinku ban raga maki ba to agarinmu ma bazakiji da kyau ba muddin kikayi kuskuren shiga hurumin mijina don haka becarefull kama hannunta tayi kamar wata maganar arzuki sukayi tace zo mu zauna kusa da Amarya tana murmushin mugunta ita ko yau Suby taga yarinya karama makira munafuka wato dama akwai irin wadannan yaran haka amma gaskiya ba’ataba raina mata hankali ba irin na yau.bata gama tunaninta ba taji Hawwa tace”Aunty Teema wannan kawar taki tanada kirki murmushin yake Suby tayi itama ita ko Fatima sanin wacece Hawwa tayi shiyasa batace komi ba fatanta dai kada tasan itace wadda ke son Yaya Yusuf.hhhhh bata san aikin gama ya gama ba Hawwa tasan komi shiyasa take barazana da kalamai masu zafin sauraro
Anshirya dinner tagani ta fada ta kuma bugawa ajarida amma fa fir Hawwa bata bada kofa ba wurin mijinta haka akayi aka gama akai Amare gidansu ita kuma dama gida suka wuce sukayi kwanciyarsu Jamila ko gidan mummy ta wuce ta kwana don bata son ta hadu da Yusuf ya kama yi mata wannan wa’azin nasa.washegari akayi komi aka gama tare da walima kowa ya kama gabansa amma Suby tayi nadamar zuwanta katsina amma ta kullaci Hawwa itama sai ta nemi hanyar ramawa itako Nadiya Allah ya taimaketa tasamu abokinsj Yusuf dan gidan wani Ambassador ne kuma da alama da gaske yakeyi don shima bashi da mata kuma bazama yakeyi ba sosai a Nigeria ya tafi da alkawarin zai dawo gareta insh Allahu.Umar kam gida yayi komi masha Allah haka ya hada matansa yayi masu nasiha tare da fatan zamansh lafiya duk da yake yasan kowace da tarbiyyarta mai kyau atare da ita.sai muce Umar Asha Amarci lafiya kada ka ragama kowa cikinsu don sun maka shiri mai kyau hhhhhh……
Yusuf bafa zakaje da Hawwa Egypt ba saboda haka kama bar wannan maganar gaskiya nan zata haihu agabanmu.”wallahi Umma kinga canfa Akwai kulawa sosai kuma yaranta zasu samu ingantaciyar kula tunda dai ance twins ne.koda Baba Asabe sai mu tafi in wani abu kikeji.don Allah Umma.”hmm ai kawai kabar maganar nan tashi Hawwa tayi da kyar tamike ta zun buri baki ta fita dakin binta sukayi da kallo gaba daya tabe baki Ummah tayi tace”ba inda zaki ke mai miji kuna abu ba tunani sai ku kwashi jiji ku tafi wata uwa duniya ace can za’a haihu ko ina ne ba Allah keyi ba.”Hjy da kin barsu ai banga wani abun tashin hankaliba idan hakan yake so abarshi mana.”Ammi Yusuf ya rude fa akan wannan cikin komi yana yinshi na wauta yanzu kema kinsan idan Hjyar Kankiya taji ai ni zata rufe da fada tace komk yara ke so shi mukeyi don haka ya hakura kawai idan shi zai tafi ya tafi ban hana ba amma banda ita gaskiya.”gaskiya ne amma dai yanzu abar maganar nan tukunna kai Yusuf tashi kaje wurinta zamu nemeka.”to Ammi nagode tashi yayi yafita yana zuwa parlo yasameta zaune da uban ciki tanata cika tana batsewa tana ganinshi ta fashe da kuka cikin sauri ya isa wurinta tare da rungumota jikinsa jin ihunta yasa Ammi da Umma suka yo waje ita kuma Mami da Asabe daga kitchen suma suka yo waje hankali tashe gaba daya turus sukayi ganinshi rungume da ita Mami kuwa jitayi kamarta nutse kasa don kunya Ammi ce tayi saurin isa wurinsu don jin me ya faru ita ko Mami komawa tayi tana mamakin sakarci irin na Hawwa.”walhi nibazan yarda ka tafi ba saidai ka fasa tafiyar gaba daya wayyo Ammi kice ma Umma da Mami su hanashi tafiya tsugunnawa Ammi tayi tana bata hakuri su Umma kuma kamar status akayi dasu don mamakin Hawwa. “Keeee!!!!!mara kunya Mamice ta dawo don jin furucin Hawwa don Hawwa ta fara kaita karshe wajen rashin kawaicinta.hhhhhhh nagaji nima da shirmenta zan da huta mu hadu next page insha Allahu don jin yazata kayane???
Masha Allah ina ma kowa fatan Alkairi alla fans ina jin dadin vote dinku don haka nima bazan gajiya ba da sanbado maku TUN INA KARAMA ba.
Takuce Sa’ar Mataaa ????????????????????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????
©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
By Sa’adatu Bello
Saadatu99gmail.com!
PAGE 46
…………….Karasowa Mami tayi wurin da suke, kallon Yusuf tayi tace”maza katashi kabar wurin nan tun kafin ranku ya baci kawai yarinya tana neman zautar dakai kana yin abu kamar wani karamin yaro idan ita mahaukaciyace kai ai kanada hankali don me zaka zama sakarai akan mace duk wata lalata datakeyi ina sane to saboda haka nagaji da wannan sakarcin nata kaikuma kana biyemata mu da muka haifeku anan kasar wani abu yasameku??komu wani abu yasamemu kawai don ansa maku ido sai kuyitayin abunda kukaga dama to wallahi kamar yadda yayata tafada bazakuje ko ina ba nan zata haihu kaje ka shirya tafiyarka kaikadai Allah ya dawo dakai lafiya.”gaskiya ne Umma tace wannan maganar haka take kaje kayi shirinka ita kuma kabar mana ita nan Asabe zataje ta kwaso mata duk abunda take so agidan na yarda ta zauna nan damu har Allah ya sauketa lafiya.”hakan yayi daidai inji Ammi Hawwa ko ina kikaje Haihuwa guda dayace babu mai iya amsar maki ita kedin dai zakiyi abunki mu nan duk son da muke maki tsakaninmu dake Addu’a don haka kuyi hakuri kuba xuciyoyinku magana kibarshi yaji ya dawo kilama kafin ya dawo kin haihu.gaba daya yaji maganganun su tashi yayi ya fita batare da yace komi ba ita kuma fadawa tayi jikin Ammi ta sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya kowa wurin ya tausaya mata amma dole su kauda kai su lallasheta ta zauna gabansu ta haihu don gaba daya ita da mijinta wauta ke dibansu.Mami barin wurin tayi itama Umma binta tayi sai Ammi da Asabe aka bari wurinta suna faman lallashinta.
Koda Yusuf yafita rai bace ya nufi office yana zuwa ya shiga office dinsa su kansu ma’ikatan sun gane baya cikin haiyyacinsa don ba haka yakeyi ba indai lafiya lafiya.yana shiga ya daga waya yakira Umar yace yasamesa office “ok sir yafada masa cikin zolaya don daga jin muryarsa yasan wata rigimarce shida Hawwa bai bata lokaci ba ya isa office din Yusuf knocking yayi sanin cewar Umar din ne yasa yace” yes come in budewa yayi ya shiga da sallama ya mika masa hannu sukayi musabaha zama yayi tare da cewa”lafiya na ganka so cool??ko dai maman yanbiyuce ta taba mana kai ya karashe magana cikin zolaya”hmm plss counsellings this countarct pappers din ya tura masa gabansa.cikin razana ya mike tsaye yace What!!!Yusuf are u serious??”yes i’m serious Umar”why??zakaja mana asara acompany why??cikin zafi yake magana don yaga abun na Yusuf din da gaske yakeyi.”saboda baza’a barni in tafi da matata ba .dariya yaba Umar aikuwa ya kwashe da dariya hhhhh.lallai Romio to wallahi baka isa ba sai anyi wannan contract din tunda sun zabemu kuma dole muyi don haka komi is Done.sake kallonsa Yusuf yayi yaga da gaske yakeyi yasan waye Umar.”haba don Allah ya kuke so inyi da rayuwata saboda me kowa zai kasa fahimtata kuma ciki ma harda kai Umar why!!why!!!ya karashe magana cikin rauni.dan uwa da dan uwa sai Allah nan da nan Umar yaji tausayin dan uwan nasa yakama shi.shima cikin tausasa murya yace “bros bawai ban fahimceka bane ina hango mana nasarar da zamu samu ne a company nnan ne yanzu ace mun soke kwangilar nan ai bamuyi ma kanmu adalci ba damace tasamemu don haka sai muyi amfani da ita plss bros ka kwantar da hankalinka only 2weeks nefa zaka dawo kasamu sister lafiya kila ma lokacin ta haihu kazama daddy ita kanta zaifi mata kyau ta haihu agabansu Umma kadai san Hawwa yar gatace dole ka danne zuciyarka kayi hakuri kayi mata fatan Alkairi ka lallashi matarka ta kwantar da hankalinta.tabbas kalamain Umar sun dan tausasa zuciyarsa amma taya zai samu natsuwa ya bata cikin wannan condition din anya zai iya kuwa??murmushin takaici yayi yace” to yanzu kana nufin in barta in tafi?”yes shine abunda ya dace bros “hmmm to shikenan na barma Allah komi” yauwa bross kagama magana yanzu kaje kasamu Hawwa ka kwantar mata da hankali”uhum wai fa tana gidan Umma kuma ma ayanda naji daga nan kayanta za’a kaimata har sai ta haihu”hhh ok to wannan ashi ake kira goyon ciki zakace mani ta tafi ayya gaskiya ba ‘a duba maka ba frnd amma bakomi zan raka ku koma tsohon part dinka domin kuyi ban kwana mai kyau ya karashe magana cikin tsokana.nan dai basu bar company ba saida Umar ya tabbatar daya kwantar ma da Yusuf hankali kuma sun magance komi.