HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Ammi da Asabe basu kyale Hawwa ba saida suka kwantar mata da hankalin da nuna mata faidar zamanta gida haka dai suka shawo kanta harta saki ranta ita ko Umma fa Mami suna can suna tattauna yanda zasu bulloma alamarin nasu Mami ce ke magana agaskiya Yayata bana son yanda Hawwa takeyi ma mijinta yakamata tazama mace ta gari amma ya daina bin abunda take so dole saboda gaba akeji ni gaskiya bazan yarda ta maida mani yaro sakarai ba ya tare a wurin mace na juya shi gaskiya Hawwa ta gyara halinta shagwabarta tayi yawa yayata.”uhum kada ki damu Hawwa harda cikin nan ya canzata amma muyi mata uzuri zata gyara muyi hakuri lokaci kadan ne Allah dai ya rabasu lafiya”Amin Amin Mami tace.

Tashi sukayi suka koma parlon samun su Ammi sukayi sunata hira kamar wani abu bai faru ba suma isa wurin sukayi da fara’arsu suna yimata dariya wai tagama borin rufe fuskarta tayi tana dariya zama sukayi suka sanyata tsakiya.”wai yanzu Hawwa har Yusuf ya kwace mani ke har kina borin sai kin bishi lallai na yarda dadin Aure kesa ace ma miji Baba gaba daya suka kwashe da dariya ita kuma Hawwa wata irin kunya ce ta rufeta don kwata kwata ma ita abunda tayi mamakin abunda tayi nan dai sukaita zolayarta har ta warware sannan Ammi “tace ina zaki zauna wurin Umma ko part din mijinki?rufe fuska tayi tace” Ammi part din shi “hhhhh kingani ko Ammi haba Hawwa bata sona yanzu mijinta kawai don haka nima nafi son zamanki acan don kada ki takura mani nida tsohon mijina tunda kowa kansa yasani haka dai suka tashi anata dariya da farin cikin samun kan diyar tasu itadai Mami bata cewa komi don ita akwai kawaici.

 

Yusuf gida ya koma bai wuce gidan Umma ba don sai daga baya yaji kunyar Mami sosai abunda yayi shiyasa bai kara tunanin komawa ba sai zuwa ko darene ya lallaba yaje yaga matarsa don ya nemi wayarta akashe yasan fushi takeyi kwance yake yana jin wni feeling aransa sha’awa takama shi sosai domin yana tausayin Hawwa yanzu baya matsa mata amma fa yau abun naso yafi karfinsa ya fara jin mararsa na mashi ciwo sosai yana cikin wannan halin ne yaji dawowar Jamila daga wurin aiki ajiyar zuciya ya sauke.ita kuma ganin motarsa tasan yana gida tabe baki tayi aranta tace nasan yana can wurin yar gwal dinsa tunda ita bata ma san bata gidan ba. Bayan yan mintoci da dawowarta ne ya tashi da kyar yanufi part din Jamila yana zuwa ya shiga tare da sallama amsawa tayi cikin mamaki gashi ta gansa dafe da mararsa cikin sauri ta iso garesa tana fadin ” lafiya Yusuf?atake ya nuna mata bukatarsa don shi rabonshi da ita yakai wata goma aiko Jamila tana ganin haka tayi murmushin mugunta tace yaune yasan da cewa ita ma matarsa ce.hhhhhhh

Masha Allah ku biyoni next page don jin yaya Yusuf zai fada tarko kokuma zai tsallake ina maku fatan Alkairi masoyan Tun Ina Karama Iluv u too much all fans.

Takuce Sa’ar mataaa????????????????????????????????????????©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

TUN INA KARAMA????????????????????????????????

By Sa’adatu Bello

Saadatu99gmail.com.

PAGE 47-48

……………..Hmmm Yusuf kenan, to ni yanzu me zan maka??kallonta yayi da kyau yana tunanin sau uku kenan tanayi mashi haka shikuma bawai don yana ra’ayinta bane yake nemanta don dai kawai kada ya cuta mata da yawa amma kwata kwata ba sha’awarta yakeyi ba.”yanzu Jamila ni zaki wulakanta don na nemi jikinki??kuma kina matsayin matata?sau uku kenan kina yimani haka saboda ina kulaki.”nima ai idan na matsa maka ai cewa kakeyi kai sex bai dameka ba amma ai kana kwanciya da matar da kakeso gashi nan har kayi mata ciki sau biyu nifa?”ok to yanzu dai yauma bazaki duba halin danake ciki ba ki kwantar mani da hankali sai kin ja mani rai haba Jamila komi nayi maki ki daure ki cire mani wannan damuwar.”dakata Yusuf!!katashi ka fitar mani daki tun ina gayamaka magana mai dadi dama ai ku maza haka kuke idan kuna son abu wurin mace kun iya kwantar dakai ku raina mata wayo to ni bazaka samu ba kaje ka nemi magani kasha har lokacin da matarka zata haihu sai ku cigaba daga inda kuka tsaya amma ni Jamila kabarni da jarabata idan ta taso mani inada mafita shiyasa kaga ban damu da damuwarka ba kaima kaje kasha magani ai akwaisu kala-kala kakuma sansu u are parmacy don haka plss out don yanzu na dawo inada bukatar hutawa.tab!lallai Jamila kin wuce duk inda na ajiyeki aransa yake magana don mamakinta ya hana shi magana bai sake cemata komi ba tashi yayi ya fita don yafara jin ma sauki yana fita ta rufe kofar garm!juyowa yayi ya girgiza kai kawai ya shige part din Hawwa da alkawarin yagama nemanta zata gane kurenta.nikuma Sa’adatu nace Yusuf nayi maka murna kayi freee hhhh.Allah yasa mu dace.

********************
Ita ko Jamila dariya tayi sosai ai ban taba ganin ka rude haka ba Yusuf hhh niga sakarai sai kawai kuma in bude masa cinya saboda ina tsoronsa ai ni yanzu gaba dayama ka fita raina tunda nasamu dai dai dani kuma ni shikadai nake jin dadi ko tabani yayi ina gamsuwa badai kawai ina labewa da aurenka bane amma gaskiya ka fitar mani arai Yusuf. gaskiyane Jamila tunda angama dake da Asiri ai kinyi ma kanki.

Yusuf yana shiga dakin Hawwa akwati ya dauka yafara zuba mata kayan da yasan zata nema saida yagama sannan ya fito da akwatin ya nufi part dinsa saida ya tabbatar ya kulle mata ko ina sannan wanka yayi ya shirya kawai dai karfin hali yakeyi amma har yanzu yana tare da feeling dinsa haka ya fito yasanya kayan amotarsa bai wuce ba saida yayi sallah magrib sannan ya wuce yana zuwa kamar yadda yayi tsammani haka yasamu parlon ba kowa sai Asabe dake jera abinci akan table da sallama ya shiga amsawa Asabe tayi tare da yi masa sannu da zuwa cikin fara’a ya amsa tare da gaisheta ajiye kwanokan hannunta tayi ta nufe shi domin amsar kayan hannunsa kujera ya nufa zai zauna sai yaji Asabe” tace ai Alh Karami uwar dakina tana sashenka can tace zata zauna murmushin jin dadi yayi sannan yabi bayanta suna shiga zaune suka sameta tana sallah don yanzu bata iya sallah atsaye saboda kafafuwanta duk a kumbure suke da sallama suka shiga Asabe ta wuce cikin bedroom din ta ajiye mata akwatin ta fito ta fita shikuma ya nemi wuri ya zauna saida ta idar da sallah sannan ta juyo ta kallesa kwance kan kujera ya daga kansa sama ko mi yake tunani oho.”lafiya hubby nah?saurin tashi yayi ya iso wurinta ya zauna kamar yadda ta zauna suna fuskantar juna murmushi yayi mata yace”sannu ya jikinki itama maida mashi tayi bata amsa ba sai ta sunkuyar da kanta kasa.”me yasa kika kashe wayarki tundazun bayan kinsan dole in nemeki??”kayi hakuri namanta akashe take.me yasa kika zabi zama nan sashen?”saboda akwai abubuwan da zasu debe mani kewa ko baka nan.”uhum to amma kin hakura in tafi din?”na hakura ina maka fatan Alkairi.”na gode dakika fahimci komi Allah ya saukeki lafiya.”Amin ya Allah. Mamakin natsuwarta yakeyi da canjinta to me yafaru ta zama so cool haka??bai gama tunani ba yaji tace “bari in kawo maka abinci tana kokarin mikewa riketa yayi ya zaunar da ita yace” zauna ba yanzu ba.kwantawa yayi jikinta yana shafa cikinta yana magana da cikin ita kam dariya yabata sosai.bakinta ya kama yasaka nashi ciki yana tsotsa kamar wata sweet.Ummace ta fito tare Abba bayan tagama fada masa abunda ya faru tsakaninta da Yusuf suna fitowa taga babu kowa parlon Asabe ta kwala ma kira cikin hanzari ta amsa ta fito gaishe da Abba tayi sannan tace “Hjy gani” wai tunda Hawwa ta shiga bata fito bane?ko taci abincin ne?”A’a bata fito ba amma taci abinci kuma Alh Karami yazo yana ciki tare da ita.kallon juna sukayi ita da Abba murmushi yayi yace”to kyale su zauna Hjy muci abincin mu zama sukayi ita kuma Asabe ta koma ciki dama Mami tare da Ammi suka tafi don gobe take so ta koma kaduna shiyasa suka tafi tare dama zuwa tayi wata gaisuwa da akayi masu rasuwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button