TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? takuce sa’ar mataaaa????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 8
………..yaya yusuf da umar cousins ne sbd umar shine babba wurin Alh bello kanin Alh bashir baban yusuf, tare suka taso tun suna yara babu abunda ke raba su sai in yazama dole.ko karatunsu tare sukayi shi india couse dinsu ne ba daya ba shi yusuf permacy ya karanta shi kuma umar Account ne.duk da haka dasuka dawo gida nigeria suna tare acompany daya wanda dama na su ne company babu abunda akeyi cikin shi sai hidimar magunguna sakamakon dama abunda yusuf ya karanta kenan.kuma suna samun kwangila daga gwamnati sbd babu kasar da basu kawo magani kuma masu inganci basu yarda su hada hulda da kasashen da suke yaudarar kasarsu sbd kishin kasa.
Jamila tare suka taso don itama dakadan suka girmeta ko a skul shekara daya ce tsakaninsu da ita itama india tayi karatu tare da su yusuf amma ita kwararra likita ce yanzu haka tana cikin likitocin da ake ji dasu a cikin jihar katsina tana aiki ne da fedaral medical center dake cikin garin katsina.jamila tana son yusuf sosai arayuwarta sbd irin mazan da mace zatayi alfahari dasune.kuma tanada wani hali duk abunda take so to bata boyewa ko jin kunyar nuna mashi kuma tana da son kanta da yawa da son zuciya kamar yadda ta gani wurin uwarta.nidai na taso hannun ummatah da Abbanah wanda su nake ma kallon iyayena da suka haifeni.sbd karamci irin na dangin mamana tunda ko su ban taba jin sunce wani abu ba na dangane dani kawai dai abunda nafara fahimta ina dan kama da mamin kaduna amma bana sawa araina akwai wani abu kuma ina jin ina son matar sosai araina amma tunani nako don tana mahai fiyar yaya yusuf ne.na tashi cikin so da soyayyar yan uwana su aunty zainab.
Haka nayi krtuna primary da secondary anan katsina lkcn dana gama secondary ne ina da shekara 17 kuma ashekarar akayi mani aure da yaya yusuf wanda dama wai jirana kawai yakeyi sbd duk matan dake bibiyarsa baya ma kula su ciki ko harda jamila.bai so maganar aurena yanzu ba amma hakan bata samu ba.
Sbda yaso ace na fara jami’a kwatsam sai gashi ya canza shawara sbd wani dalili nashi.hakan yasa aka gaggauta yin auren mu.
Bana manta wannan ranar da akayi bikin wata cousing dinmu Aisha wanda aranar ne ne komi ya canza a sakamakon wani hoto da da jamila ta hada tare da wani saurayi ta turo ma yusuf shi kuma lkcn yana gida.abunda ya faru, mun shirya nida nabila kanwar jamila zamuje wurin dinner to dama gsky itace kawata sai na nafisa autarsu yusuf tunda duk kanmu daya kuma mun shaku da juna sosai, to nafisa tana wurin aunty zainab a Abuja.mun gama shiryawa muka fito daga dakina muka samu ummah tana zaune tana kallon tashar sunnah tv tana ganinmu ta fadada murmushinta cikin kulawa tace masha Allah kunyi kyau yan matana cikin jin kunya muka rufe fuska tare da isowa kusa da ita muka zauna gefen ta muka sata tsakiya.cikin shagwaba wadda tariga ta zame mani jiki nace ummatah ina yayana?tare da kallon kofar da zata sadaka da sashin shi cikin kulawa tace yaje masallaci amma naga alamar kamar ba zai fita ba, yanzu dai bari in sanar ma Adamu driver ya kaiku tana magana tana kallon wayarta dake caji kafin tayi ta kara mgn na mike na dauko wayar na mika mata.bugu daya ya dauka ta sheda masa abunda zaiyi ya amsa da to hajiya mikewa mukayi tare da yi mata sallama tace kada mu wuce karfe tara komi mukeyi insha Allahu muka ce tare da fita waje muna fita muka ga Adamu yana kokarin fiddo wata katuwar jeep prado blue sai shaning takeyi har inda muka tsaya ya iso ya bude mana muka shiga baya muka zauna tare da gashe shi ya amsa mana cikin walwala baba mai gadi ya bude mana muka fita sai liyafa place inda akeyin dinner .
Fitarmu kenan shikum yusuf ya fito daga masallacin kofar gidanmu yana fitowa ya hangi motar gidanmu ta fita daga get cikin mamaki yace to wa yafita yanzu a wannan motar?cikin hanzari ya shiga cikin get din gidan tare da sallam baba mai gadi ya amsa kafin yace komi yusuf yace baba waya fita da mota yanzu cikin mutunci yace ai yallabai Adamu ne hjy tace yaje ya kaisu autarta wurin biki da yake duk ma aikatan gidan haka suke kira na da autar hjy.ok kawai yace ya shige cikin gidan tare da sallama umma ta dago kai tare da amsa masa sallamar babu walwala a fuskarsa ya zauna kusa da umma yace umma saida kika bar yaran nan suka tafi wurin dinner nan ko?”eh tace ai banyi tunanin zasu dade ba kasan hawwa ma da ba son hayaniya ne da ita ba.ai umma da kin kinkirani sbd darene kuma kin san jamila zataje tana iya yima su hauka tunda sakarai ce cikin damuwa ya karashe mgnar.”tace ba komi insha Allahu lfy zasu dawo amma duk da haka shirya ka dawo da su saikace ma Adamu ya taho gida “ok yace tare da mikewa zuwa dakin sa ya canza kaya tunda dama kafin yaje masallaci yayi wanka.yana shiga ya shirya cikin kananan kaya wanda sun karbi jikinsa yayi kyau sosai yana shiri ya na kallon agogon dake manne a dakin.ya dauko perfumes yana fesawa wayar shi tayi kara alamar text ya shigo da kuma hasken da wayar ta karayi.kamar bazai duba ba kuma kawai sai yaji yana son ya duba koda ya dauki wayar sai yaga ashe sako ma na whatsapp ne kuma sunan jamila ne ke yawo akan sakon kamar zai aje wayar sai kuma yayi tsaki mtss ya bude sakon
Innalillahi wa’innailaihin raju’un, haka kawai yake maimaitawa.sakamakon wasu hotona da jamila ta tura mashi na hawwa tare da wani saurayi kamar suna mgn ita kuma hawwa tana dariya wanda ita bama tasan saurayin yana kusa da ita haka ba.
Jikin shi har rawa yakeyi yasa hannu ya dauki key din motar shi a sukwane ya fiti falo babu umma hakan ya bashi damar fita kawai inda yayi parking ya nufa ya shiga motar a rude sbd tsabar kishi.baba mai gadi ya bude mashi get tare da daga masa hannu adawo lfy yace.haba ina ko ji bayayi haka ya fita cikin tashin hankaki da rikicewa hoton hawwa kawai yake gani tana yima saurayin nan dariya.hawwa kina sona kuwa?me nayi maki?
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? taku ce sa’ar mataaaa ????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 9
……..”haka yaketa maimaitawa yana tuki amma gaba daya hankalin shi yana wurin wannan hoto.cikin minti kalilan ya isa liyafa place haka ya shiga ciki.daidai inda motar Adamu driver take yayi parking.cikin hanzari Adamu ya fito yana karasawa wurin shi lkcn da ya bude mota ya fito hannuwan shi cikin aljihun wandon shi, duk dayake cikin bacin rai ba karamin kyau yayi ba.Adamu yace yallabai barka da isowa, yauwa kawai yace atakaice.ina suke?ya tmby shi “ai suna ciki ranka shi dade bai rufe baki ba saiga hawwa ta fito daga hall din tana neman nabila don ta gaji tana so tafi gida haka nan, daidai inda motar su take ta hango Adamu shida yaya yusuf .cikin faduwar gaba ta ambaci yaya yusuf kuma anan?cikin sauri ta nufi wurinsu inda tunda ta fito suka hangota sbd hasken fitilun dake wurin.Adamu ne ya katse shirunsu da cewa gama autar hjy nan isowa.
Yanda taga alamunshi, tasan akwai matsala haka ta karasa jiki ba kwari cikin tsoro tace yaya kaine?” Shiga mota kawai yace mata”yaya nabila kafin ta karasa ya daka mata tsawa!wanda har Adamu saida ya firgita”shiga mota ya sake cewa cikin rudewa ta bude motar ta shiga.ya juyo yace m Adamu kajira nabila ka taho da ita.cikin girmamawa ya amsa da to yallabai.afusace ya isa wurin motarsa ya bude ya shiga ya fita a180_200 hhhh ran maza ya baci to hawwa ina tausaya maki hannun yusuf???? Adamu mamaki kawai ya hanashi motsi har na tsawon minti biyu atsaye sannan ya juya ya koma wurin motarsa cike da tunanin mai ya bata ma oga rai haka?to koma menene Allah ya kyauta.