TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Abba ne ya kalli Umma yace”Khadija abunda nake so dake kada kisake kiyi ma Yusuf magana koda kuwa gidan nan zai rinka kwana har ya tafi.saboda idan kika lura yaran nan suna junan su son da Allah kadaine yasan shi don haka kisa masu ido kawai.dariya tayi tace”insha Allahu Alh angama.koda suka gama cin abincin komawa sukayi part din Abba ita kuma Asabe tashi tayi ta kwashe kayan da gyara dianing din.
Hawwa gaba daya Yusuf ya rikicemata wani irin cakudata yakeyi yana romancing dinta ta ko ina ita kanta tana jin dadin yanda yakeyi mata kuma tana bashi hadin kai don tasan waye mijinta.cikin muryayarsa wadda bata fita sosai yace”bazan so takura makiba honey amma ina cikin wani yanayi walhi bazan iya hakuri dake ba amma inason ki taimaki mijinki ki kauda mani wannan damuwar pls sweet heart ya karashe magana kamar zaiyi kuka.”baka da matsala dani mijina zan iya daurewa kasamu natsuwa.kara rungumeta yayi sosai very tightly daga nan fa wasa ya canza nikam tsorona ma kada ace ya jawo mata nakuda.saboda ya manta halin datake ciki ya lula duniyar taurari tabbas ya gamsu iya gamsuwa kuma yaji dadin yanda tayi masa dauriya haka ya taimaka mata
ta gyara jikinta sannan suka kwanta cikin farin ciki da godiyar Allah.
Tabbas nan ya gama kwana biyun daya rage masa saboda kamar yadda Abba yace babu wanda ya kulasu ita kuma Mami takara yima Hawwa fada akan tabi mijinta sau da kafa kada ta kasance kullum cikin wauta irin tata yakamata ta zama mai kawaici da kunya haka dai tayi mata nasiha sosai sannan ta kama hanya ta tafi.shi kam Yusuf ranar tafiyarsa harda Hawwa akayi mashi rakiya Airport haka suka rabu babu dadi ita ko Jamila cewa tayi bazata samu zuwaba tana da aiki bai damu ba don dama yasan bazai samu fatan Alkairi ba daga gareta ba.
Hawwa gaba kuwa gaba daya tunda ya tafi komi ya tsaya mata bata dawata walwala saida aka kwana sannan yasamu kiranta aikuwa yasha rigima a waya haka nan yakeyi idan ya dawo wurin meeting to baida abunyi sai ya kirata suyita hira har sai sun gaji don kansu .kwanan shi biyar da tafiya nakuda ta taso ma Hawwa gadan gadan nan da nan aka dauketa sai Asibiti cikin gaggawa aka amsheta akayi lebour room da ita kowa hankali tashi don taba kowa tausayi Umar ne yaketa kai kawo su Umma kuwa in banda Addu’a babu abunda sukeyi mata adaidai wannan lokacin yaji gabansa yanata faduwa gashi yau shine har bayan magrib bai kirata ba saboda yana da ganawa ta musamman da shugaban company n Extra Panadol hankalinsa baya tare dashi saboda yanda yakebjin jikinsa ba dadi.kuma dama Abba yace kada wanda ya fada masa halin da ake ciki abari aga abunda Allah zaiyi minti 55 ta dauka sannan Allah ya kawo mata haihuwa ai kuwa kukan yaran ne ya karade dakin daya na faduwa dayar ta biyota gaba dayansu mata ne itako mai gayya mai aiki bata san inda kanta yake ba don girman yaran over hhhh nurse dince data amshi haihuwar taketa mamakin kyaun yaran da kwarjini su a ido saida aka gama gyarasu da kyau sannan aka fito dasu aka mika ma su Umma da Ammi dake wurin kowa sai tayasu murna akeyi nurse dince ta juya zata koma ciki Umma tayi saurin cewa “ya jikin uwarsu nurse?” Hmm karki damu mama yanzu zamj kaita dakin huta don ta jigata anyi mata allurai da drip za’a sanya mata don haka insha Allahu zata samu lafiya.”to masha Allah Allah ya Amsa “Amin.
Sai wajan karfe tara ya dawo masaukinsa yana zuwa ko wanka bai shigaba ya kira wayar Hawwa yajita kashe ” Allah dai yasa lafiya amma bari in barmata sako ta whatsapp kafin in gama wanka yana bude data sakonnni sukai ta shigo masa nan da nan ya bude na Umar pic yagani na yara guda biyu kamar larabawa saurin duba kasan pic din yayi yaga an rubuta.Congrat New Daddy hhhhh…..ai cikin sauri ya wuntsulo daga kan gadon da yake ya kwance hhhhhh……????????????
Masha Allah ku biyo ni next page don muje wurin suna fans kada abar kow abaya hhhh.????????????
Iluv u all fans Tun Ina Karama… Takuce Sa’ar mataaaa????????????????????????????????????????????©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
TUN INA KARAMA????????????????????????????
By Sa’adatu Bello saadatu99gmail.com!
PAGE 49-50
…………Kara murza idanuwansa yayi domin ya tabbatar da ba mafarki yakeyi ba kara duba pics din yaran yayi yana kallonsu kamar Hawwa lokcin datana jaririya don bazai mance da fuskarta ba.kiran Umar yayi bugu biyu sannan ya dauka cikin zolaya Umar yace “sirikina ko ka iso ne??” Hhhh kai dai wallahi Abokina ka canza wai ina matata???”to ai wadan nan yaran larabawan dolene in kama daya daga.cikin su ai bana bari azo daga waje akwashesu gaba daya ba.sister bacci takeyi tana hutawa ne wannan iri aikin datayi haka ai gaskiya kai gwarzo ne.congrat my Bros Allah ya Albarkaci Rayuwar yaran mu.”Ameen frnd amma dai bata da wata matsala ko??”No babu komi gajiya ce kawai yanzuma zan samo mata wasu magunguna ne da ake bukata duk su Umma suna wurinta ita da Ammi.”Masha Allah Allah ya bar zumunci Amma Jamila fa?”gaskiya ban ganta ba kuma ban tambaya ba Amma naga Mummy tazo ita da Daddynsu Nabila.”ok to shikenan komi kenan sai mun kara magana.”ok to ba matsala.Daga nan fa yafara kiraye kirayen wasu daddy dasu Umma yana tambayar su ya Hawwa Abokai ko ayan uwa kowa yasamu labari Haihuwar Hawwa.Granny kuwa har ta iso daga kankiya tunda safe.Mami kuwa koda Yusuf ya kirata yace yaushe zata zo katsina cewa tayi”bata iya karashin kunya ba duk mutanen dake wurinta sai tazo to tayi mata me??don haka ita kada ma ya karayi mata maganar zuwa katsina kashe wayarta tayi.shima bin wayar yayi da kallo baiji dadi ba wai ita Mami kamar ba yar boko ba ta cika kawai ci amm ko don saboda shi aita sassauta abubuwa Allah yasama kada ta janye jikinta da jikokinta Amma zan nemar maku mafita awurin Kakarku my sweet child.
An sallami Hawwa saboda jikinta yayi kyau kuma komi normal sai muce Allah ya kara lafiya my Hawwa hhhh anji jiki an tantance aya da tsakuwa Allah ya sakama iyayenmu da Alkairi Ameen ya Hayyu Qayyum.
Wai Jamila me toshe maki basira ne har kika fada taron bokan nan kuma kika saki jik dashi kuma ni dai banga wani cigaba ba kullum suke nasara ke abubuwa sai kara lalacewa sukeyi ba wani cigaba.kuma kinje kin kara jawo wata matsalar yanzu ya kike so muyi da wannan cikin??”hmm Samira bazan iya bayyana maki tashin hankalin danake ciki ba wai shi kuma fa cewa yayi niba doctor bace inje in zubda shi mana don shima bai shirya haihuwa dani ba.”to ai kinyi sakarci tayaya kinsan ga halin dakuke ciki sannan kuma ki ki amincewa da mijinki ada kin dan rika sakar masa jiki tunda harma yana nemanki ai kinga da bai isaba yace ba cikinsa bane ba ko?to amma yanzu kin lalata komi”wallahi Samira bashi da hakina ne shiyasa ninasan Asirina ya gama tonuwa.”yanzu dai kibari tukunna mu samu mafita sai musan abunyi naji kince Hawwa ta haihu har ya biyu?”eh hakane ina son zuwa ingane ma ido na naji ance yaran kamar larabawa.”hhhh to dama ta ina zasuky muni uwa da uba kyawawa.