HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Granny ce zaune tana ta ba Hawwa hakuri akan ta bude nononta taba yaranta amma sam takiya wai bazata iya jure zafin datake ji ba don haka gara ma anemo masu madara tunda yunwa sukeji”wallahi Hawwa ki bude nonon nan kiba yara kafin in batamaki rai Aunty zainab ce ke magana cikin fushi.kwabe fuska tayi ta daga rigarta kamar zatayi kuka daukar hassana tayi ta mika mata amsarta tayi ta kanga mata nonon abaki ai kuwa yarinya ta cabke kamar zata cire kan nonon wata irin kara Hawwa tayi ta fashe da kuka riketa Aunty Zainab tayi sosai har saida yarinyar ta koshi sannan itama usaina akabata kuka shabe shabe Hawwa takeyi babu wanda ya kulata don anga abun nata bana hankali bane haka take so akyale yaran da yunwa.kowa fita yayi yabata wuri sai ita kadai a dakin jawo wayart tayi ta kira Yusuf bugu daya ya kashe ya kirata tana dagawa ta fashe da kuka ciki kidima da razana yace”Hawwa meke faruwane!!??”ni wallahi bazan iyaba wadannan yaran zasu cire mani nono wallahi kace arinka basu madara ni bazan iyaba.”dariya ta bashi sosai amma sai ya danne yace”haba Hawwa yanzu yarana baki iya taimakonsu don bana kusa?kuma meyasa ni da nake shan nonon baki ai baki ce mani da zafi amma wadanna yan yaran har kin fara korafi akansu wai baki son yaran su zama masu basira ne idan aka basu madara ba lallai bane su zama very sharp plsss my loverly wife nasan ki da kokari da aon abunda nake so don haka gaskiya ni dai banda ra’ayin ki basu madara saidai idan bazakiy mani wannan alfarmar ba ya karashe magana shima kamar zaiyi kuka.maganganunsavsun kwantar mata da hankali don haka nisawa tayi tace”shikenan zan basu tunda haka ne ra’ayinka.”yauwa good girl yanazu ina yaran suke?”gasu na kwance amma ba bacci sukeyi ba.”to bude data zan kiraki video call in gaisa da.”tom kashe wayar tayi ta kunna data kirane ya shigo na video dauka tayi kwance yake akan gadonsa gani tayi ya kara mata kyau.cikin zolaya yace mata maman Yara kinga yanda kika koma kuwa gaskiya wannan jegon yayi maki kyau dole ne fa in dawo saboda asamar ma twins gambo.sauri tayi ta rufe bakinta alamar maganarsa ta bata kunya.”haba daddyn twins ai ka tausaya mani insamu ko 5years ne nan gaba sannan kayi maganar wani Gambo.hhhhh gaskiya yarinya baki isa ba so nake in cika gidana da yara.turo baki yatayi tace”baga Aunty Jamila nan ba itama tayi kafin in kara.”yauwa wai tazo tagansu kuwa??”A’a bata zo ba.”hmm to kinga alamar wadanda nasamu ma bakin ciki takeyi dasu bare kuma tayi kokarin in samu daga jikinta.”ai zata zo tunda itama dole nata ne.haka dai suka dade suna hira har saida Usaina ta fara kuka sannan yace ta dauketa sai yakara kiranta kuma duk yanda zaiyi zai dawo nan da 3days insha Allahu taji dadi sosai itama don tana son ace yana nan za’ayi suna.

 

 

Yanzu ke Jamila neman yanda zakiyi da ciki har wahalane??kije kawai kisamu magani ko injection kiyi yauwa wai ina injection din dakikayi ma Hawwa wadda cikinta ya zube to kije kiyita mana kawai.”yauwa Samira kin kawo shawara ni gaba daya ai namanta da ita kai amma fa naji dadi dakika tuna mani amma fa wani hanzari ba gudu ba bari zanyi sai angam sunan yarinyar nan kinsan family dinmu da sanya ido tunda kinga tana bada wahala.”gaskiyane hakan yakamata to wannan issue din is Done.

 

“Nabila wannan dinkin yayi mani kyau ke gaba daya ma dinku nan sunyi mani kyau.” To ai ina so ki fito kamar daga jirgi kika sauka akasa gane amaryar jegon kuma naji Yaya Umar yace zai dawo nan da kwana biyu kinga ai gara in shirya kawata hhh.”kai Aunty Nabila kina kara hura mata kai kinsan dai yanzu ta zama mummy n yara hhhh”wai ke Fatima akwai wanda ya kaiki shagwaba munsan komi Mami ta gama shagwaba ki amma ai kema sauran kiris ki zama mummyn.nidai yaushe kikace mai kunshin zata zo ne Nabila???

 

Ke kuwa Suby meyasa baki jin magana ne??to menene ribarki idan kin shiga tsakaninsu ??ni kin ganni nan yanzu bana son inga ana shiga tsakanin masoya.”eh lallai Nadiya don kin kama wanda kike so ne shiyasa kike jin hakan amma gaskiya ni sai na rama wulakancin da Hawwa tayi mani kuma saina sanya mata zargin mijinta wanda take ganin babu kamarsa don haka babu ruwanki kisa mani ido kawai.”to shikenan kije kiyi yanda kike so ni kinga tafiyata.

 

 

Wai kai wane irin mara hankaline dazakace wai yanzh kuma kanaso in bar maka cikinka bayan na fada maka babu abunda ke shiga tsakanina da mijina to taya zan bar cikin daba nashi ba???”Jamila kuskure na karshe da zakiyi arayuwarki shine ki ki bin abunda nace maki!!!don haka ki tashi ki tafi gida yau ma banida bukatarki inaso kije gida ki huta bana son kina wahalar mani da cikin nan.daga yanzu ni zan rinka zuwa idan kina bukatata sai muje hotel agarinku ba sai kinyi tafiya ba ni kuma zan rufe bakin mijinki.jinjina masa kai tayi alamara ta Amince…Tirka shi wai wata sabuwa!!!!!

Wai Hawwa baki barin wannan sakarcin ko yanzu saida kukayi yanda kukayi Yusuf ya dawo lokacin dawowarsa baiyi ba ko ???”wallahi Mami babu ruwana ki tambayi Yaya Umar kiji.”ke da Allah ki rufe mani baki indai sakarci abunyi ne kije kiyi Granny tace “Isuhu da Hawwa ai sai kallo don haka ki daina bata lokacinki Mami kaduna.

Daidai zata shigo gidan taji Umar yana cewa zanje ne in dauko Yusuf ne Airport Nabila ki bari in dawo sai muyi magana yanzu bai wuce 20 mins ba jirginsu yayi landing kallon kallo sukayi sannan ya fice ita kuma tashi ga cikin tashin hankali gabanta ke faduwa nashiga uku ni Jamila me yasa zai dawo ban ai watar da kudirina ba????

Masha Allah ku biyoni don jin menene damuwar Jamila???akan dawowar Yusuf??

Ina ma all fans Tun Ina karama godiya aduk inda kuke fatan Alkairi.

Takuce Sa’ar Mataaaaaa????????????????????????©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

TUN INA KARAMA????????????????????????????

By Sa’adatu Bello Saadatu99gmail.com!

PAGE 51-52

………Nikam nace saboda Allah ya fiki Jamila.karasa shigewa tayi amma ranta cike da fargabar dawowar Yusuf ita fa taso kada ya dawo har a yi suna ita kuma ta aiwatar da kudirinta na zubda cikinta.tana shiga wucewa tayi part din Umma suka gaisa ita kanta Umma ta zargi ganin yanayin Jamila ya canza ga wani haske datakeyi kauda tunanin tayi tace”keda Mijinki zai dawo yau ai da baki fito ba.”ai ba za n dade ba zan koma”to shikenan “kin shiga part din su Hawwa” A’a yanzu dai zan shiga.”to masha Allah tashi tayi tafita zuwa ganin yaran Hawwa wanda tunda aka haifesu sau daya tazo ta gansu.da sallama tashiga dakin amsawa Hawwa tayi da fara ‘arta “Aunty Jamila sannu da zuwa gaskiya yaranki sun fara fushi dake.” Hhhh ai gani nazo ayi hakuri tsugunnawa tayi gaban gadonsu suna kwance “hy my babeis yanda suke daga kafafuwansu gwanin ban sha’awa daukar daya tayi ta zauna shigowar Granny kenan ta ganta ” aaha ashe zaki zo ko kuma don mijinki zai dawone yau shine kika lallabo to ai can gidanku zai sauka ba nan ba.”eh din kuma ai nafiki sanin ba nan zai sauka ba zaki wani dameni.’nikike ya tsinama fuska to uwarki Mariya kike murguda ma baki mara kunya kawai.Dariya Hawwa tayi tace”kem kin iya cin fuska shikenan da mutum yayi maki abu sai ki zage mana iyaye jiya ma inajin kina ma Aunty zainab harda zagin Umma.lallai ma ashe haushi kukeji?sai ni dakuka raina kuke fada mani yanda kuke so ko?”wai yanzu dai me kikeso kika shigomana nan??”kaji mara kunya to nono nazo kiba yara don naga tun safe baki kara basu ba.”to ai sai ki koma tunda bacci sukeyi ai sai a saurara mani ko?fita tayi tana cewa zan kama ki yarinya.kallon Hawwa Jamila tayi taga yarinyar takara yi mata kwarjini ga wani irin kyau dake bayyana ajikinta kamar ba ita ta haifi yaran nan ba.yanzu nima da cikina na hanya mai kyau ne ai da taji dadi amma kash !akawai matsala.bata gama tunaninta ba taji muryar Nabila nacewa oyoyo ga Yaya Yusuf ya iso Jamila ji tayi kamar ta nutse kasa don tsoro gida ya kaure da murnar dawowarsa yana ta gaisawa da mutanen gidan baki da yan gida direct part din Umma ya wuce yana shiga da sallama ya nemi wuri ya zauna Umma ta shigo tana cewa”ni ina baya naji kamar ka shigo”eh wallahi mun shigo gaisheta yayi tare da tambayarta ya samesu lafiya.”lafiya klau saidai da ka taho hankalinka ya kwanta ko?”wallahi Umma mungama dama sauran kwana biyun zamu cika lokacin ne kawai kuma dana bada Uzuri an yarda na taho.”masha Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button