HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Babu kowa wurin Hawwa daga ita sai yaranta.shikuma saida yagama shiga ko ina sannan ya taho wurin matarsa Granny natayi masa tsiya shidai bai kulata ba kawai so yake yaje ya ga matarsa yana shiga da sallama ya tura kofar yasa key ajiye Usaina tayi tayo kan Yusuf ta fada jikinsa ya rungumeta yana kissing dinta ta ko ina hankali kwance suke tsose junan su kamar ba mai jego ba da kyar suka fada kan gadon suna maida numfashi.kallonta yayi da kyau yace”looking beautifull sweet heart.murmushi tayi tace”ai kai ma gaka nan kamar baka tunaninmu kayi wani fresh dakai.jamata hanci yayi “kinjita ko.tashi yayi ya isa gadon yaran ya dauki Usaina ya kalli Hawwa wadda ke dariya yana nuna mata itace babba girgiza mashi kai tayi alamar A’a maida ta yayi ya dauko Hassana ya ya rungumeta sosai yayi mata Addu’a ya ajiyeta yadauki Usaina itama haka ya kwarara mata dua’i dama kuma Umar yayi masu huduba.zama sukayi suka sha hira abinsu kamar bazasu rabu ba sunyi kewar juna sosai ya kuma fada mata ya yo ma yaransa tsaraba da ita don dolene yabata gift mai tsoka.Granny kuwa da kyar ta fidda shi wurin Hawwa tana ta mita wai yaran zamani basa tsoron komi ita Hawwa saboda rashin wayo har take kebewa da miji.

Koda ya isa gida sai yaga motar Jamila aransa yace ba wai ance tana can gidan ba ko harta dawo kenan koda yayi parking ya fito agajiye part din Jamila ya wuce direct yana shiga ya sameta kwance har tafara bacci abun mamaki yace azuciyarsa to meyasa meta yanzu takw bacci.jamata kofar yayi ya fita zuwa part dinshi cike da mamaki aransa.

Washegari daren suna gida ya cika makil da yan uwa da abokan arzuki koda ya tashi zai fita saida ya biya ta wajan Jamila amma sai keyin tunanin anya Jamila lafiya take kuwa?tashin ta yayi daga baccin datakeyi.afigice ta tashi tana murza ido kallonta yayi da kyau yace”baki san na dawo bane tunjiya ance kina gidan Umma amma banganki ba na dawo gida sai na sameki har na shigo nan dakin baki san nazo ba mike damunki yanzu kuma naji motsinki amma kuma har kin koma bacci?murza idanuwanta tayi sosai cikin fargaba tace wallahi fever ke damuna sannu da dawowa.kallonta yayi yaga yanda ta canza gaba daya komi nata cool”yauwa ya gida?”lafiya klau to yanzu ki tashi ki shirya in kaiki Asibiti ki nemo magani sauri tayi tace “A’a nayi treating din kai na zan samu sauki ” to Allah ya sawwak.”Amin tace ledar da ajiye gefensa ya kalla yace ga tsarabarki nan dauka tayi tace “nagode har zai juya ya juyo yace ” ki fada mani abunda kike bukata na hidimar suna zanje gidan Umma idan kin gama kisameni can.”ok tace shi kuma ya fita don tafiya.”wayyo Allah na ni Jamila ina zansa kaina kaicho da son zuciyata wallahi bazan bar cikin nan ba saina zubda shi da alama Yusuf zai so ni saboda duk masifarsa yana da tausayi.

 

Kai bayyana shirin sunan nan ai kauyanci ne Hawwa kam tasha kyau kowa yana cikin farin ciki anyi juyin duniyar nan MAmi tazo tace bata da lokacin wannan ga dai yaranta nan gaba daya ta turo da yan uwanta suma sun isa komi amma ita ba inda zata.su Nabila kam da Fatima da Nafisa basa ganuwa hidima akeyi ba kama hannun yaro.komi ya ji muma mungama shirinmu tsab don zamuci mutuniyar mu karya kashi hhhhh.

 

Washegari yara suka ci sunan Umma da kakarsu mahaifiyar su Umma Hassana itace Khadija Usaina kuma Maryam Amma duk sun boye sunan Hassana Amal Usaina Minal kowa yaji dadin wannan abu da Umar yayi.masha Allah sai muce Allah ya raya twins.Ameeen..

Gida fa ba masaka tsinke kyaututuka kam basa faduwa saboda abokan Yusuf sunyi kara ga yan uwa ta ko ina nikam danaji yar tawa kyautar ai sai naita boyewa cikin mayafina amma dayake kunsan mutane masu sanin mutuncin mutane dana mika ma Hawwa ai kamar ta goya ni godiya take tana karawa haka naita rufe mata baki har na sulale na barta ban ankara ba sai naga an biyoni da katon kulli wai naki ne Sis Fatinah Nabilace ke miko mani nikuma ina sunne kai naji kunya fa sosai amma dai sai nazo gida zan bude in ga me na samu??

 

Babu laif Jamila ma tayi ma yaran kyautar dubu dari biyar check tabada gaskiya ita kanta Hawwa tayi mamakin hakan shima dayaji yaji dadi yanda ta kula da yaransa sai kawai ya manta komi yana jin tausayinta kusan mai da wawa ne.anyi hidima hankali kwance batare da wata matsala ba kowa ya kom gidansa lafiya Alhamdulillah.sai dare Yusuf yasamu ganin Hawwa nan fa yaga matarsa da yaransa cikin farin ciki.”to yanzu madam yaushe zaki koma gida kuma?”wai so kake Mami ta tsine mani duk ita fa danayi abu sai tace wai banda kunya.”hhh ai ni bansan kalar Mami ba ita dai bata son Umma taga kamar ta nuna mata wani abu.”kaidai bari kawai.

Kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita tana cewa”Samira wallahi Yusuf ya canza ya fara sona amma gashi ina cikin wani hali wand bazan kubutar da kaina ba kacho ni Jamila nashiga uku kamata Samira tayi ta zaunar da ita tace”ba kuka zakiyi ba yanzu mafita ita yakamata mu nema Jamila….

Masha Allah kuyi hakuri da wannan ba nepa insha Allahu zamu hadu a next page.don jin ina mafita ga Jamila???

Iluv u all fans Tun Ina Karama Allah ya bar kauna nogde sosai ina yinku nima luv u so much…..

Takuce Sa’ar Mataaaaaa ????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

*saadatu99gmail.com!*

 

PAGE 53-54

……….”Haba Jamila ke wace irin sakarai ce dazaki yarda da wannan alamari ki biye ma dan iska yana lalata maki rayuwa gaskiya kin bani kunya ai duk zuwan damukeyi wurin bokayen mu ni ban taba yarda da wannan ba saboda me zai maidake kamar matarsa har ya dura maki ciki kuma wai yace yana son abunda anya Jamila ba asiri yayi maki ba??”wallahi mummy nikaina ban san dalili ba amma inaga dai Allah ne ya tona mani asiri kuma ya kawo karshen mu.saurin rufe mata baki mummy tayi “ke kada kiyi mana baki kawai yanzu mu nemi mafita kamar yadda Samira ta bada shawara kuma idan ba hauka ba kinsan ga halin da kika sanya kanki domi zaki ki yarda da mijinki har nawani tsawon lokaci ai wallahi kinyi shirme yanzu tayaya zamu tunkare shi da wannan cikin muce nashi ne ai kema kinsan karya ne.” Allah yana son Yusuf saboda bashi nufin komi damu yanzu nagane irin cutar da mukayi masa kuma nagane Nabila ita ke hanyar daidai arayuwa dolene take gujema munanan halayarmu mummy kin dorani ahanya karkatatta kin ingiza rayuwata cikin hadari bazan taba ganin uwa irinki ba wadda ke tura diyarta cikin hadarin son duniya irinki ba mummy da ace lokacin da idona ya rufe da soyayyar Yusuf kjn nusar dani illar rashin son dayake yi mani da ban shiga wannan halin ba na son zuciya kin nuna mani zaki iya komi ashe ba haka bane kuma dama kullum maganar Nabila kenan akan indai na wannan halin na son zuciya amma sai ki nuna mani bata kaunar cigabana ne to gashi yanzu zamu fara girban abunda muka shuka kaicho da wannan rayuwar. Fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya mai sauraro.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button