TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

“Wallahi Nabila yaran nan sun cika shan nono da yawa kinga dai yanzu na ajiye dayar itama dayar ta wani tashi bacci fa takeyi amma don rashin son in huta ta wani tashi tana kuka.” Hhhhh lallai Hawwa da sauranki to ke bakiga yanda yaran suke tubarkalla ba?”bashiyasa nace tun farko ba abasu madara ba” hmmm bu bar wannan issue din kiba yara hakkinsu.yanzu dai yaushene zaki koma?”ai kinga yanzu dai saura one week mu gama wanka amma fa inaso inje kaduna, kuma naji Yusuf yana cewa sai na koma zanje kaduna to amma dai yanzu sai yanda Umma tace tukunna.”to shikenan dama sonake ayi maki wasu hadi masj kyau kafin dai ki koma kinsan yanzu amarya zaki koma mutuniyata hhhhh.”kai Nabila kedai baki gajiya da zolaya.
“Umar wallahi bansan yanda zanyi ba da mayyar yarinyar nan Suwaiba ba kullum cikin yi mani text takeyi ba kuma lokaci any time komin dare kaga haka last time taso hadani da Hawwa kuma kaga yanxu ma ta kusa dawowa kaga ko akwai fitina in har Hawwa tasan hakan.” Gaskiya kam amma kuma me zai hana ka fadi ma Hawwa tunda kaga wancan lokacin ma ita tayi saving dinka yanzu ma banga amfanin yin shirunka ba har sai abun ya kwabe.”hakane bro bari yau zan sanar mata komi”is good
” ke Jamila bafa zan yarda ki zubda cikina ba kawai kije ki kashe Aurenki kizo muyi Aure don gaskiya bazan rabu dake ba ina sonki sosai kuma ina jin dadinki don haka bazan so abunda zai rabamu ba.”amma gaskiya ka cika katon jahili saboda me zan aureka? wallahi bana aurenka yakuma zama wajibi mu rabu ko bakaso ko kana so kuma ni wannan hanya na barta nayi nadama kuma ashiye nake in dauki ko wane irin hukuncin da mijina zai dauka akaina nagaji da wahala haka nan.”lallai yarinya ai ko zaki dauki abunda yafi karfinki”to kabarni in dauki abunda yafi karfin nawa mana kuma bana so ka kara zuwa garin nan da sunan wurina kazo don haka bana son ka kara tunanin kama taba sanina don ni daga yau har abada bazaka kara ganina ba duk tsafinka.bude kofar tayi afusace ta fita daga hotel din data samesa.tashi yayi zai bita kafin ya fito harta sauka kasa ta nufi wurin motarta agaggauce don bata son wani ya ganta ko akasin hakan.juyawa yayi yabkoma tare da cewa aransa bazai barta ba har saita Amince da bukatarsa.itako tuki takeyi tana share hawayen nadama.
“Amma Hjy Lami kinsan haka wannan tsinen mutum din yake shine kika cuceni kika kai mani diyata har yayi mata ciki??” Taya zan san haka yake Hjy Mariya??kuma ita Jamila ina iliminta da har ta yarda ta basa kanta ni tunda na kaita takara zuwa tace mani ga wani abu sai yanzu dasuka gama sharholiyarsu Asiri ya tonu shine zakizo kina tuhumata??”lallai Lami amma ban taba sanin rashin mutuncin ki haka ba sai yau kina tare dani amatsayin Aminiyata amma kike fada mani magana haka lallai makashinka yana tare dakai.”ni yanzu kawai ki tashi kuje ku nemi mafita amma bawai kizo ki tsareni da bakaken maganganu ba don kinsan ba hakuri gareni ba.”zan tafi amma kisani duk abunda yasamu diyata kema ki kuka da kanki.a fusace ta fita tana mamkin wulakancin da Lami tayi mata.
“Ai wallahi Nadiya sai na tura ma Hawwa pics din nan kinsan nawa nabiya aka hada mani su zaki wani hanani inyi kudirina to kibar ma wannan maganar.” Wallahi Suby abunda kike shirinyi bashi da kyau kuma irin wannan abun yana ruguza mutum arayuwa nidai shawara nake baki ki kyale Yusuf arayuwa.”tab!amma Nadiya baki da hankali dazakice in kyale Yusuf to wazan kama??”ki roki Allah yabaki daidai ke mana sai kiga kin samu wanda ya fishi ma.”ke mu bar maganar nan kadama ki bata mani rai ki kyaleni kawai inyi abunda nake so
“Khadija wai me yasa kukeson fifita al’ada bayan addini shine gaba da komi kawai gobe ku shirya Hawwa ta koma gidan mijinta haka nan yaranta sunyi wayo to sai me kuma nasan duk kece da wannan takurar plss ki maida mashi matarsa gida gobe in Allah ya kaimu ki fadama Ammi sai kuyi maganar dazakuyi idan ana bukatar wani abu afada mani.” To Alh ba damuwa zan fada mata.
“Amma Jamila gaba daya kin canza baki da wata walwala nayi maki magana ko kan aikin kine amma kince hutu kika dauka ko ba komi tunda kina karkashin kulawata dolene in sani ko??ya karashe magana cikin damuwa.” Babu komi Yusuf kada ka damu da rayuwata ahalin yanzu don bazai amfaneni da komi ba don haka karka damu kanka babu komi ta karashe magana tana murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo.
Koda Abba ya fada ma Yusuf Hawwa zata koma ai ranar baiyi bacci ba don tun last dayaje da niyyar zai fada mata maganar Suby sukayi fada akan yaga Hawwa tana ba yaransa madara ba nono ba tun ranar baran-baran suka rabu saboda shiyarasa gane matsalarta akan shayar da yaranta amma yau dayaji zata dawo kusa dashi ya kirata ya kai sau 20 amma bata daga ba wai ita batama so dawowarta yanzu ba don haka tunda tashi fushi kawai takeyi wai me yasa Umma zatayi mata haka?ita kuma tace Abba ne ya yanke hukunci don haka dole ta koma yau.Asabe ce da Nabila da Fatima sukaje yima Hawwa gyara agida gaba daya saida suka maida mata ko ina need sannan ga kamshi na tashi kala kala sun fito zasu tafi kenan.Nabila ta lura da part din Jamila bude yake har yanzu alamar tana nan ke nan har yanzu?cewa tayi tana xuwa kasan abun dan uwa shiga tayi da sallama samunta tayi kwance aparlo amma ba bacci takeyi ba amsa mata sallamar tayi tare da tashi zaune daga kwanciyar data keyi da fara’arta take amsa gaisuwar Nabila ita kanta Nabila mamakine fal aranta yanda taga yar uwar tata ta canza Allah dai yasa lafiya ta furta aranta.”Aunty Jamila lafiya kike kuwa Nabila ta jefa mata tambayar “Nabila Hawwa zata dawo yau ne?itama ta tambayeta?” Eh mun gyara mata part dinta ne anjima zata dawo.yanzu kuka bayayi mata wuya kawai saita fara share hawaye wanda bata ma san lokacin da suka fito ba.Ya Salam, Aunty Jamila kuka kuma lafiya dawowa tayi kusa da ita ta rike mata hannuwa cike da tausayin yar uwar tata hankali tashe Jamila ta fada jikin Nabila tana kuka mai tada hankali tsoro fargaba ya rufe Nabila ta kara rungume yar uwar ta ……tofa duniya Makaranta mu hadu anext page wanda zamuji menene mafitar Jamila.Iluv u so much all fans TUN INA KARAMA.!!!
Takuce Sa’ar Mataaaaa????????????????????©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
TUN INA KARAMA????????????????????????????
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
By
SA’ADATU BELLO Saadatu99gmail.com!
PAGE 55-56
………….”Wai meyasa meki ne Hawwa??kin bar yara suna kuka haka ko ajikinki kina zaune kina jinsu!!cikin tsawa yakeyi mata magana itama juyowa tayi a fusace tace”ai kamata yayi ka daukesu kakaima Suby wata kila zatafini iya kula dasu tunda soyayyarku tayi nisan da har zaku iya yin pics masu na badala ku tura ma duniya tunda nima nasan bani kadai ta turamawa ba.Yusuf kabani mamaki kana pretending akan Suwaiba har ina haukan kare maka mutuncinka awurinta don naga yarinya bata da kalar mutunci ni banma san dalilin dayasa Fatima ta yarda da yarinyar nan ba har tazama kawarta ba.”Amma Hawwa wannan wace irin magana kikeyi ni ban san komi ba akan wannan maganar takiba meya faru kuma ni ina naga bansan wani pics dakike magana ba kuma ni ina naganta bare inyi wani pic da ita??kuma ke ina kikagansu kuma ita Suwaibar ce ta aiko maki da pics din???”kada ka kara nuna mani bakasan komi ba.kuma ni nasan matakin da zan dauka akan komi kaje kayi abunda duk kakeso kuma yara ni ba matsalata bane idan naga dama in basu nono idan kuma banga dama ba babu wanda ya isa yasani kana son yara kaje kana zubda mutunka?har zaka wani shigo kanayi mani hargowa wallahi Yusuf indai yaudara zakayi arayuwa to ka toshe ma kanka farinciki wallahi.tashi tayi tafita daga dakin a fusace.shi kam Yusuf bude baki yayi sosai yana kallon fitarta lamarinta ya daure masa kai sosai amma dole ya nemi Suwaiba yaji me tayine haka kuma yayi alkawarin wannan karon bazai barta ba kuma itama Hawwa zai koya mata hankali tunda har yanzu bata yarda da abunda zai iya da wanda bazai iyaba.zuwa yayi wurin yaran cike da tausayinsu ya tsuguna zai daukesu sai yaji sallamar Asabe tana cewa “uwar dakina ce tace inzo in kawo mata su Amal naga ma kamar bacci sukeyi saurin cewa yayi ” A’a daukarsu ki kaimata tana daukarsu ta fita ajiyar zuciya sauke yace” nasan kishi ke damunki Hawwa amma ya kamata ki yarda ke kadai ce mallakina amma kin kasa fahimta.