HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

“hhhhhh wallahi ai Nadiya nafada maki sai na cusa mata bakin cikin daya fi wanda ta cusa mani kuma ni nasan bom din dana dasa mata azuciya kuma wadannan pic din dole ne su samata zargun mijinta don haka yau jina nake i’m free.” wallahi ni baki burgeni ba kuma wallahi sai kinyai nadamar yin wannan abun aure fa kika shiga tsakani haba Suwaiba kema ki saurari naki kuma ni nasan Yusuf bazai taba barinki ba indai har yasan wannan sharrin naki yanxubke baki jin komi ki tura wadan nan pics din koni da nake kallonsu baki ji yanda nake jin kunya ba haba Suby ai ba mutunci kuma wannan ki tura ma matar mutum haka kawai don ki haddasa bala’i acikin gidan aure tirrr da halinki ni kinga kada ki kara sanya ni cikin wannan shirmen naki mutum yace baya sonki baya sonki amma kin nace to naga yanda akeyin so dole.matsa ni ban wuri in wuce fita tayi tana tsine ma Suby.”oho dai na aikata komi zaifaru ya faru banda case kema kyaji da gulmarki.

“Ni wai meyasa kike jan ki da zubda cikin nan naki ko so kike komi ya lalace bayan kinsan kullum kara girma yakeyi haba Jamila ki maida komi ba komi ba ki daure kiyi allurar nan bana son wannan mugun mujin naki yasan halin da ake ciki kada ya haukace mana haka kawai.” cikina ya zube adaren jiya kuma bani na zubar dashi ba asali ma banyi yunkurin yin hakan ba ni kaina bana ce maki ga abunda ya faru kawai na tashi ne na ganni cikin jini faca faca amma ina danganta hakan da damuwa datayi mani yawa sannan kuma ina ganin akwai abunda Allah yake so ya nuna mani na ishara arayuwata.saboda haka dole in kyale Yusuf in fita rayuwarsa nima in koma ga Allah gaskiya Samira na hakura da komi zan fada ma Yusuf irin cutar danayi masa amma fa bazan boye masa komi ba ciki kuma harda maganar cikin nan.sauri Samira tayi ta toshe.mata baki da hannu tana girgiza mata kai”amma Jamila wannnan babban kuskurene tabbas kin cutar Yusuf amma bai kamata ko zaki fada masa komi amma banda wannnan maganar cikin don ba karamar masifa zai jawo ba na yarda ki rabu da Yusuf kuma Jamila wallahi dama nima wani mafarki danayi jiya ya tsorata ni kuma sai naji wannan abun da ya faru dake yakara samani jikina yayi sanyi kuma nima insha Allahu zan bar komi in kama Allah inyi aure tsakanina da Allah.”amma kina ganin rufe ma Yusuf nayi zina da aurensa ba zai zame mani wata masifa ba??”ba haka bane Jamila kedai kamar yadda kikayi nadamar nan tsakaninki da Allah to ki koma ga Allah kawai kiyi ta tuba amma fada ma Yusuf to wata babbar fitina ne tunda Allah yasa baiga cikin nan ba kuma yazo ya zube to ai babu amfani fada masa nidai shawara idan kin tashi rokonsa gafara kisama ranki harda maganar cikin kawai kice da abunda kasani da wanda baka sanifa na bayan idonka ya yafe maki ina ganin ai shikenan kawai ba sai an tsaya tone tone ba.”uhum to shikenan nagode.to ni bari intashi in koma sai naji daga gareki naga ya fita bana son yadawo yasameni kinsan ya tsane ni nima.”hakane to ba komi sai munyi magana.

“Amma uwar dakina meyasa yau zakice mu zauna gida bazamu biki ba nida yaran??saboda ba dadewa zanyi ba.kuma nasan har indawo skul din bazasu nemi nono ba kuma ni nafison yanzufa su kama abinci sosai kinga mun kusa fara exam abubuwa zasuyi yawa” to amma kina ganin Alh karami zai yarda da hakan?”sosai ma kuwa karki damu.

 

Ta bude mota zata shiga taji yace “ki dawo ki tafi da yaranki kokuma ki bar karatun tunda ba dole bane kuma nine mai so yanzu kuma nace abarshi.juyowa tayi a sukwane don jin kalamansa akanta tsaye ta taganshi ya harde hannuwansa babu alamar wasa atare da shi fuska daure itama tace” to ai naga kamar bani kadai bace mai sonka muna da yawa kuma suma zasu iya rike maka yara saboda me kakeso dole saika takurani kuma karatu ai maganar ma ka hanani bata taso ba tunda nafara har nazo karshe yazama wajibi in gama.kallonta yayi da kyau lallain Hawwa kishinta ya wuce wuri tunda gaba daya wai harda yaranta ma wadanda basu san menene duniyar bama amma tana neman azabtardasu why amma xai koya mata hankali”su wadanda kike tunani suna sona aiba su suka haifar maki yaran ba don haka suma zan basu nasu kowa ya rike nashi tunda rashin imanin naki yakai har ki wulakanta mani yara to baki isa ba.matsawa yayi kusa da ita ya kama hannunta ya jata zuwa cikin gidan part dinsa ya wuce da ita direct ya zaunar da ita.wani irin bakin cikine ya taso mata kawai ta fashe da kuka kyaleta yayi ya fita yaje wurin Asabe yace tabashi yaran ita kam Asabe tarasa gane canjin da Hawwa tayi gaba daya ta hargitse mata kuma kwata kwata yanzu bata damuwa da rayuwar yaran Anya kuwa??gaskiya akwai wani abu.kuka takeyi sosai yazo ya sameta karasawa yayi kusa da ita yaran naganinta suka fara dariya suna mika mata hannu itako juyawa tayi ta basu baya shikam abun nata ya fara bashi tsoro uwa da ya’yanta amma takeyin haka??anya ba aljanu suka shafeta ba?? hmmm nace kabar kishi kawai Yusuf ya wuce hakan ba komi bane awurin Hawwa hhhh.

Nafada maka kada kara tunanin kasanni arayuwa bare har karinka kirana awaya in ba hakaba zan tona maka asiri munafuki azzalumi wanda ya dauki sabon Allah Abinci shi mushiriki dan isa bana fatan sake ganinka arayuwata.kit ta kashe wayarta.”tabbas ta samu nasarar zubda cikin nan da ba haka ba da asirin danayi bai karye ba tab lallai amma fa nayi rashin mace to yanzu ina mafita???oho maka dan asara????

“To yanzu mummy meye laifina don na yanke hukuncin rabuwa da Yusuf???gaskiya bazan cigaba da cutar da rayuwarsa ba kuma ni na tuba na koma ga Allah zanyi rayuwa kamar yadda Nabila takeyi zan zauna da kowa lafiya bazan kara shigar da rayuwata ba cikin masif tabbas dama Yusuf ba sona yakeyi ba don haka zan rabu dashi kuma bazan sake shiga rayuwarsa ba.kuma kema mummy ya kamata ki daure ki fita wannan hanyarta halaka kibar duk wadannan abubuwan ki zauna da yan uwanki lafiya wani wawan mari ta sakarmayakeyi, jikake tas!tas!!tas!!!

masha Allah mu hadu a next page don jin wannan badakalar kuyi hakurin rashin jina banida lafiya ne kwana biyun amma Alhamdulillah iluv u all fans Tun Ina karama…

Takuce Sa’ar Mataaaa????????????????????????©????TUN INA KARAMA????????????????????????????????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

BY

SA’ADATU BELLO Saadatu99gmail.com!

PAGE 57-58

………………Dafe kuncinta tayi wasu hawaye masu zafi suna zuba daga idanuwanta kallon mummy take tana tunanin wannan wace irin uwace arayuwa wadda son zuciya yayi mata yawa gaskiyane yanzu ta tabbatar da gaskiyar Nabila akan Mummy to itama dole ta janye jikinta daga gareta har lokacin da Allah zasa tagane gaskiya.”keee!!yanzu har kinkai lokacin da zaki fara yi mani wa’azi Jamila wato kema anyi maki asirin da akayi ma Nabila ta maidani ba Uwarta ba bata jin maganata to kema kin bi layi kenan???to bari kiji in fada maki wallahi baki isa ba ki canza ni kuma indai haka kikace to ko kin kashe aurenki ki nemi wurin zama amma ba nan gida na ba.cikin kuka da tashin hankali Jamila take magana”Mummy ko zaki kasheni bazan kara yarda in koma halaka ba kuma yazama dole in fada ma Yusuf cutar da mukayi mashi saboda ko kina so ko baki so dolene in bar Yusuf ya zauna lafiya.murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace ko kince kada in zauna tare dake ina da inda zan zauna kuma ai Dad kadai zai koreni gidansa amma bake ba shikuma na tabbatar zai karbi tubana tunda dama ya gaji da halinki kuma ina nadamar kasan cewarki mahaifiyata amma ina rokon Allah ya shirya ki .daga nan tafigi jakarta ta bar gidan cike da takaicin Mummy.”Jamila!Jamila!!Jamila!!!ina ai ko juyowa batayi ba ta fice ta barta da mamakin sauyin Jamila lokaci guda.Nikuma nace Allah kenan..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button