TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

“Wallahi Suwaiba kifita rayuwata idan ba haka ba zansa adaure mani ke har amanta dake ababin rayuwa haba!!!wannan wace irin jarabace to wallahi billahi duk ranar dakika kara tura ma matata wannan iskanci wallahi ubanki zanci kiji da kyau kuma tunda baki san mutunci ba duka ranar da kiranki ko text dinki ya shiga wayata sai na daureki wallahi sakarai yar iska wadda bata san darajar aure ba ke baki isa ki kashe mani aure ba karamar yar iska kitt ya kashe wayarsa yayi tsaki mtssss mahaukaciya kawai.tun sanda yafara wayar take tsaye tana jinsa wanda shi baima san ta shigoba wata irin kunyace ta rufeta saboda jin makircin Suwaiba tayi amma ta dora alhakin komi akan mijinta karasawa tayi kusa dashi zatayi magana ya dakatar da ita tashi yayi ya fita daga dakin ya barta zaune cike da mamaki lallai akwai matsala Yusuf ya dauki fushi dani.
” Wai ni kinzo kin tasani gaba kinata kuka kamar wadda akayi ma mutuwa kuma kinki cewa komi amma idan kinyi mai isarki kin fada mani matsalarki duk da nasan tatsuniyar koki bata wuce ta gizo.”aikema Nadiya sai ki zubda ruwa kasa kisha yau dai Yusuf yayi mani zagin fitar arziki ya ci mani mutunci kuma wallahi na tsorata da abunda yace wai zai iya sawa ka kulleni har a manta dani.”hhhhhhhh Allah nagode maka ai wanda baiji bari ba to zaiji hoooo to ni ina ruwana lokacin da nake fada maki gaskiya ai ba saurarena kikeyi ba in banda kema butulu ce duk mutuncin da Fatima tayi mana arayuwa amma kike bin mijin yar uwarta kuma mu kinsa Fatima tafimu matsayi ko skul tunda Babanta mai kudin ga mukami amma ta zauna damu me muke dashi??amma ki rasa da abunda zaki saka mata sai wannan shiyasa ni tun wuri na fita hanyarki don haka kadan ma kikagani indai son zuciya ne.”gaskiyane na yarda dake kuma ke da baki sama ranki ba ai gashi Allah ya baki mai arziki kuma dan gayu nima Allah na tuba.”to yanzu kika dawo hanya amma kuma dole ki roki Hawwa ta yafe maki in har kina son Allah ya yafe mai don kin cutar da ita.”insha Allahu zanyi haka kuma kema nagode maki dakika zama kawa tagari nima ina fatan Allah ya bani daidai ni.Amin kawata karki damu kedai ki dogara da Allah.
Kin san Allah Hawwa ki tashi ki bani wuri kada ranki ya baci ya ina aikina zakixo ki dameni kuma bayan kinsan yau ba ranar aikinki bace ita mai aikin ma bata zo ta takurani ba sai ke to bana bukatar ganinki yanzu kifitar mani daki tun kafin in saba maki.sakin baki tayi tana kallon yanda Yusuf ya rufe ido yake shuka mata rashin mutunci.”amma ai da ka saurareni in fadamaka abunda ya kawoni kuma ni ban san kasa dokar sai mai aiki zata rinka zuwa wurinka ba?”from now nasa dokar daga kanki don haka get out!!!hankali tashe ta mike ta bi hanyar fita da gudu don yanda kuka ya taho mata gaba daya tana toshe bakinta.shikuma jiyayi kamar ya bita amma ina ya riga yayi niyyar hukuntata don yana so ya nuna mata shine sama da ita kuma yakamata tasan matsayinsa akanta.”so sorry Hawwa ke kadai ce in my life.
Saida sukayi kwana uku basu haduba duk ta rasa inda zata bulloma alamarin Yusuf gudunta yakeyi sosai ko yaran sai ya tabbatar bata wurin Asabe yake zuwa ya gansu saidai Asabe tace mata yazo ya fita ita kanta Asabe tarasa gane alamarin nasu amma tasanya masu ido taga iya gudun ruwansu.
yau yana Kd wurin Mami ita Hawwa bata ma san ya tafi ba suna zaune da Mami haka ya kwashe komi ya fada mata babu abunda ya boye mata tsakaninsa da Hawwa don ya lura tafi jin tsoron Mami saboda ita Umma goya mata baya takeyi kuma yasan Mami zatayi mata komi cikin hikima kuma zata gyara zamansu tsakaninshi da ita.kuma yana so ko gaba ta daina hukunta yaransa akan laifin ubansu shine dalilinsa na fada Mami komi.nisawa tayi tare da cewa”ai dama abunda nake nuna maka kenan kadaina sake mata da yawa irin abunda ake gudu kenan amma to shikenan yanzu in koma kace ta shirya ka kawo wurina in tazo zan fada maka abunda za’ayi.”to shikenan Mami zanyi hakan”aidai Ummanku bata sani ba ko?”eh gaskiya bata saniba nasan data fada mata da sai tayi mani magana amma nasan bataji ba.”to shikenan haka za’ayi gobe ko jibi kazo mani da ita tayo shiri kamar na sata guda saida gaban ya fadi jin tace sati guda shifa koda yake haka yana so yarinka jin motsinta kusa dashi ita kanta Mami saida ta lura da tsoron daya ji sharewa tayi “ko baka jiba??” naji Mami zanyi hakan.
“Amma uwar dakina gaskiya baki kyauta ba sau nawa ina nuna maki irin wadannan abubuwan basu da amfani kuma bai kamata mace tagari tana irin wannan ba kekin san tunda Jamila ta saduda akan Alh Karami to babu fa wadda zata kwace maki shi kuma ke kinsan abunda kike zarginsa da shi bazai aikata ba don me zaki biye ma zuciya kisaka mijinki cikin tashin hankali agaskiya kin fusata shi da yawa shiyasa kikaga ya fita harkaki amma kema ba gajiyawa zakiyi ba da bashi hakuri kuma ki nisanci irin wannan abun.” gaskiya ne kuma zan kiyaye insha Allahu.
“What ??Jamila kinsan abunda kike fada kuwa??saki fa kikace??cikin kuka tace ” eh Yusuf nasani…
masha Allah mu hadu next page don jin ya za’a kare tsakanin Jamila da Yusuf Happy Juma’at Iluv u All Fans Tun Ina Karama…
Takuce Sa’ar Mataaaa????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????????
©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*
_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم…
By
*SA’ADATU BELLO Saadatu99gmail.com!*
“`PAGE 57-58“`
~SECOND TO THE LAST PAGE IN SHA ALLAHU~……..
*Ina mika godiya ta ga duk kan masoyan wannan littafi nawa na TUN INA KARAMA.kuma ina mika godiya ga kungiyata na irin gudun mawar dana samau daga shugawagabanni na Allah ya saka ma kowa da Alkairi bazan fasa jinjina maki ba Aunty nah Aseey Beauty agaskiya bakida bakin ciki arayuwa na koyi abubuwa da dama a harkar rubutuna daga gareki don haka ina maki fatan Alkairi arayuwa Allah ya kara mana daukaka gaba daya Ameen ya Hayyu ya Qayyum*
………..”Tabbas na cancanci haka agareka Yusuf don haka bazan cigaba da zama dakai ba amatsayin miji ina rokonka da ka yafe mani akan irin cutar dana yai maka arayuwa hakika nakasance azzaluma kuma mai son kanta dayawa hakan kuma bai kareni da komi ba sai asara don haka ina nemam alfarma agareka da matarka Hawwa don komi nayi shine akan na cuta mata amma dayake Allah ba azzalimin sarki bane sai gashi dukan sharrina ya dawo gareni ina girban abuna kuma abunda nike neman samu da karfin tsiya ya gagareni shiyasa nake son ka sauwake mani aurenka Yusuf plsss kona samu rest of peace arayuwata don haka ka taimakeni ka sakeni Yusuf takarashe magana cikin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.hakika ya girgiza da maganganunta kuma ta karya mashi zuciya amma tayaya zai saketa bayan shi ba mai ra’ayin saki bane kuma duk abubuwan datayi masa arayuwa baiyi attempting din rabuwa da ita ba sai yanzu da nadama ta bayyana agareta karara.”agaskiya Jamila ba ra’ayina bane sakin mace kuma babu abunda kika yi mani wanda ban yafe maki ba wanda nasani da wanda ban sani ba Allah ya yafe mana gaba daya kuma ina maki fatan Alkairi akan nadamarki arayuwa kyma wuri bai kure maki ba idan kinsa kyakyawar niyya tubar ma Allah nima ina rokon Allah ya yafe maki amma kibar maganar saki tsakanina dake ki daure ki zauna mu cigaba da zama har mai rabawa ta raba.share hawayenta tayi sannan ta kalleshi da kyau tace”Yusuf nagode da karamcin dakayi mani arayuwa amma ko baka sakeni ba ni zan nisan ta kaina dakai arayuwa ina so ka zauna lafiya da matarka wadda soyayyarta ta ginu a zuciyarka TUN TANA KARAMA wadda naso shiga tsakaninka da ita amma Allah bai amince mani ba don haka yanzu nima ina son in samu wanda yake sona tsakani da Allah batare dana cusa kaina wurinsa ba.plss ka taimakeni Yusuf nima insan dadin soyayyar gaskiya wadda ake yinta don Allah plssss Yusuf!!!”Jamila kibani nan da kwana biyu inyi tunani kuma kema kije ki natsu kiyi tunani.tashi yayi yabarta wurin yana jin wani babban alamari atare dashi mai wuyar ganewa.