HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

“Ki shirya gobe zamuje kaduna dagowa tayi don ta tabbatar da maganar da yayi hakane?ganin ba alamar wasa atare dashi yasa ta “amsa da Allah ya kaimu lafiya amma kuma zata kara magana ya dakatar da ita ” yace this is my order bana son wata magana ta biyo baya.kallonshi tayi da kyau aranta tace anya wannan abu na Yaya Yusuf na lafiya ne bai taba mata haka ba gaskiya amma wannan karon fushi yakeyi da ita sosai.”shikenan Allah ya kaimu lafiya.

Ganin fitar Yusuf shida Asabe yasa Jamila sanin kila wurin Umma zatakai twins don tana tare dasu kuma da alama Hawwa suka bari ita kadai tashi tayi ta nufi part din Hawwa da sallama tashiga Hawwa na zuba kaya acikin akwatinta ta dago tare da amsa sallamar aunty Jamila da fara’a tace ” shigo mana Aunty Jamila wuri tasamu ta zauna ita ma tana murmushi “da alama kamar tafiya zakiyi?” eh wallahi kinsan banje kaduna ba to shine yace in shirya inje gobe idan Allah ya kaimu.”gaskiya ne amma Hawwa wurinki nazo don neman gafararki”nikuma aunty Jamila??”eh ke kuma ina so ki yafe mani abunda nayi maki.”ita kanta Hawwa saida taji wani shock atare da ita sannan “tace bakomi aunty Jamila nidama bana rikeki wallahi ina maki uzuri amma na yafe maki duniya da lahira.hawayene suka zubo ma Jamila cikin sarkewar murya tace ” nagode nasan da wuya ki dawo ki sameni cikin gidan nan saboda nace ma Yusuf ya sakeni yace in bashi kwana biyu to na tabbatar bazaki sameni ba don haka ina me neman alfarmarki da ki rike Yusuf da kyau don Yusuf mutum ne harda rabin mutum kada kiyi wasa da damarki Hawwa ina maki fatan Alkairi.juyawa tayi zata fita don kuka naso yaci karfinta cikin sauri Hawwa ta tashi ta rike mata hannu tace “Aunty Jamila babu saki tsarin Yusuf don haka nasan bazai sakeki ba kuma kema ina mai rokonki kada ki kara furta wannan kalmar saboda bata da amfani agaremu tunda kin gane gaskiya kiyi hakuri ki zauna damu don Allah kada ki gujemana Aunty Jamila.

Mami wai Yusuf yace sati guda zanyi amma yau gashi har kwana goma bai zo ba?” ina tunanin wani abun ne ya tsaida shi.amma ai yasan gida kike ba daji ba bare ki damu kanki kuma ma mutumin da baki san darajarki ba menene abun damuwa don ya barki ki huta.shima ai kinga wadanda suka san darajarsa su lallabashi yasamu kwanciyar hankali keko kije kita fitinarki har kina wulakanta masa yara saboda abunda baki da tabbas akansa.”wallahi Mami inason yarana fiye da yanda nake son kaina wannan ma abun kuskurene amma wallahi sune rayuwata.”kai amma Hawwa baki da kunya yaran dakika ce araba matanshi amma yanzu kike kallon tsabar idona kina cewa kina sonsu har fa madara kike basu don baki kaunarsu tunda ubansu yayi maki laifi gara ki huce akan bayain Allah.”na shiga uku wallahi bance bana sonsu ba kuma bana iya ba kowa yarana don Allah Mami kiba Yaya Yusuf hakuri wallahi nagane kurena yazo mu koma gida.”hhhhh nan ma ai gidanku ne bakida matsala ko kinada ita cikin sauri tace “wallahi akwai matsala Mami Asabe dake gefe tana jin dramarsu har dariya ta kusa kufce mata ganin yanda Hawwa tayi.

zaune yake amma shima hankalinsa yana wurinta yau kwana goma basu tare ga yaransa yana son ganinsu kusa da shi anya ba zai roki Mami ba ta dawo mashi da matarsa ba?gaskiya yakamata in yi mata magana ai yanzu yasan ta gane kuskurenta amma shima din yana kewarta ga rigimar Jamila ta ta cewa dole sai ya saketa saboda baya sonta tun asali itace kawai ta shiga rayuwarsa to inma haka ne ai aikin gama ya gama tunda har sunkai wannan lokacin kuma yanzune ya kamata ya zauna da ita ko don nadamar datayi shibai san dalilin dayasa hankalinta ya tashi akansa ba amma dai zai cigaba da lallabata harta hakura su cigaba da zama shiyasa ma yakeson Hawwa.kusa.dashi ko zai samu shawararta don maganar baya son ko Umar yajita yana son suyi shearing din abun tsakaninsu kawai shida matan nasa.

Dawowarsa kenan har yaga motar mummy gidan koda yayi parking ya shiga cikin gidan baiyi tsammanin dama ganinsu a parlo ba kuma bai kawo komi aransa ba ya shige part dinsa da niyyar ya canza yazo su gaisa koda ya dawo part din Jamila basa ciki dama yanzu yasan bata da wurin zama kamar lambu direct sai ya wuce can yana isa dai dai da inda yatake zama sai ya jiyo muryar Jamila tan fada ma mummy” ni wallahi mummy bazaki kara batar dani ba babu inda zani bare har in sake shiga halaka haba mummy me kikeso dani ne me kuma Yusuf da mahaifiyarsa sukayi maki arayuwa kikeson sai kinshiga rayuwarsu wallahi akan wannan maganar bazan barki ba kuma babu sauran biyayya tsakanina dake indai har ta shirkace ki duba kigani so nake Yusuf ya sakeni amma saboda karamci irin nasa yace baizai iyaba to wallahi da ki cutar da Yusuf gara ki kasheni in huta da wannan fitinar taki daga hannu tayi zata dauketa da mari caraf! taji an rike mata hannu juyowatayi afusace Yusuf ne ke kallon ta ido cikin ido!!!!…

Masha Allah sai mun hadu last page insha Allahu Iluv u all fans Tun Ina Karama…..

Takuce Sa’ar Mataaaaa????????????????????????????????TUN INA KARAMA????????????????????????????????

©????
*Al’umma Writers Asso…✍????*

_{Al’umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al’umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al’umma sai Dan Al’umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al’umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم…

*By SA’ADATU BELLO Saadatu99gmail.com!*

PAGE 59-60

~LAST PAGE IN SHA ALLAHU~????

…………”Mummy duk abunda ke faruwa tsakaninki da Jamil naji saboda haka Jamila bata cancanci bugu ba daga gareki don kawai tace bazata aikata sabon Allah ba.sauke mata hannu kasa yayi.kallon shi kawai takeyi cikin mamaki ta bude baki zatayi magana Jamila tayi saurin cewa”gaskiya ne Mummy Yusuf ya fada maki wallahi bazan kara aikata son zuciyarki ba kawai kibarni nima inyi rayuwata mai kyau kamar kowa.juyawa tayi ta kalli Yusuf matsawa tayi kusa dashi ta tsugunna ta hade hannuwanta biyu cikin kuka tace”don Allah Yusuf ka amshi bukatata ko kasamu masalaha arayuwarka duk yanda kake son zama dani mahaifiyata bazata barka ba amma idan na nesanta kaina dakai zaka samu sauki arayuwarka ka zauna da iyalinka lafiya amma zama dani akwai matsala don haka ka sauwake mani aurenka ka zauna lafiya.shima tsugunnawa yayi ya dagota ta mike tsaye sannan ya kalleta wani tausayinta ya disa azuciyarsa sannan yau ne karo na farko da yajita aransa.”Jamila bazan sakeki ba inaso kisama ranki mutuwa kadai zata fiddaki gidan nan don haka ki daina maganar nan kawai dai kedai ki cigaba da yin kyakkyawar niyyarki ta zama dani da yar uwarki insha Allahu babu abunda zai sameki.”lallai kema an gama dake kai kuma munafuki yaushe ka fara sonta??to wallahi tun wuri ki nemi hanyar dazaki kama don wannan ba ma bullewa bace.kaikuma k shiga hankalinka bari ganin na kyaleka yanzu kana fada mani maganganun banza zanyi maganinka.a fusace ta juya ta bar wurin rai bace.ita ko Jamila fadawa tayi jikin Yusuf ta fashe da kuka shikuma haka ya rungumeta sosai ajikinsa.

yanzu nan Hawwa abunda sukayi maki kenan??”eh wallahi Umma yanzu haka ma Mami cewa tayi babu ranar komawata.”tab aiko kishirya in Allah ya kaimu gobe zan turo a daukeki ki dawo gidanki ni zasu yaudara suna azabtar mani dake?to zanyi maganinsu daga shi har Mamin tashi kada ma kice ma kowa gobe zaki dawo har sai driver yazo zan kirata in fada mata na aiko atafi dake ki shirya da wuri zaizo.”nagode Ummatah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button