TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

“haba Yusuf saboda me zaka raba masu gida tun lokacin ma da take fitinar bakayi wannan tunanin ba sai yanzu kuma ai ba mai takura wani tunda kowa part dinta daban.” gaskiya ne amma kasan wani abu ni yanzu nafi jin Hawwa don wallahi na lura yarinya karamace amma tana da zafin kishi tana iya ganin zaman lafiyarmu kaga ta bullo da wani abun amma dai yanzu ya kagani??”kawai kabarsu wuri daya kowa tayi hidimarta amma fa kaima sai kanayi kana rage wasu abubuwa akan Hawwa don kasan babu dadi cin fusaka shawarar dazan baka shine ka daure ko yayane kasa Jamila azuciyarka ita rayuwa ana kyamar mutum ne abisa wani dalili amma idan mutum ya dawo hanyar daidai jan shi akeyi ajiki ka dauka zamanka da Jamila wata jarabawace wadda kake kokarin cinyewa amma gaba daya kaida Hawwa nuna mata zakuyi kuna tare da ita ta hakan zata kara jajircewa wurin gudun duk wani aiki mara kyau ni kaina da Nabila ke bani labarin shiryuwarta naji dadi araina kuma bamu da yana zamuyi da Jamila tunda gaba daya jininmu ce ita kanta Mummy ba fasa yimata Addu’a zamuyi ba Allah shine yasan dai dai itama idan tana da rabo sai kaga komi yazama tarihi Allah dai yasa mu dace.”Ameen Umar nagode daka nusar dani hakan kuma insha Allahu zanbi abinda kace.”Yauwa bros amma ya kamata kaba Mami hakuri Hawwa ta dawi haka nan don itama fa kun shiga hakkinta nayi mamaki da Umma bata ji wannan tsarin naku ba”hmmm ai ina ga Mamice ta hana Hawwa fada mata kaima kasan yanda take tsoron Mami don batayi mata da wasa.amma nimafa nagaji haka nan insonta kusa dani ga yaran nan nayi missing dinsu sosai ni inaga can ma zan kwana gobe mu taho.”hhh ashe duk karyace abun inace zaka iya kai wata uku kuna haka”haba malam saikace ba Hawwa bace kaima kasan kawai nadai daurene kuma dana san haka za’ayi da nabar maganar ni kadai ban kaita wurin Mami ba amma ai dan ba kari wallahi naji jiki bakaga ba har wata rama nayi saboda bani da wata natsuwa.hhh gakiya ne mutumina..
Ummah tayi mamakin ganin Jamila agidanta yanzu amma sai ta kauda abun aranta tabbas ta ganta cikin shiga ta kamala abu na farko kenan sannan kuma wai yau Jamila ce ke tsugunnawa har kasa tana gaisheta cikin girmamawa lallai ne akwai wani abu akasa Allah ya jishemu alkairi.”Jamila lafiya dai daga ina haka yanzu da marece?murmushi tayi kanta na kasa tace Umma daga gida nake na zo in gaisheki kuma in nemi gafararki akan abunda na aikata maki ba dadai ba kuma ku yafe mani kada Abba nidai na gane gaskiya na tuba na koma ma Allah in neman afuwarku ku ma.daga hannu sama Ummah tayi tace”Alhamdulillah Allah nagode maka da ka nuna mani wannan lokacin Jamila tashi ki zauna kan kujera mun yafe maki duniya da lahira Allah ya shiryemu gaba daya.”nagode Ummah Allah ya kara girma yasa kifi haka.”Ameen ya Allah.
Mami tayi mamakin da Ummah ta aiko aka dauki Hawwa don wallahi taso ace Hawwa tayi wata hannunta don horu da kyau amma bakomi ko yanzu dai taji ajikinta kuma zata gyara halinta.koda Ummah ta kira Mami tana ta fada hakuri Mami taita ba Ummah.
Mummy Dad dinsu Nabila yayi mata saki uku sakamakon kamata dayayi tana zuba masa magani acikin abinci hankalinsa ya tashi sosai shiyasa ya yanke hukuncin rabuwa da ita.dama ance 99days ta koma bata da madafa su kansu yaranta gudunta sukeyi saida Ummah ta nuna masu bacin ranta sannan suke kulata don tana nuna masu dole su girma mata tunda matsayin mahaifiyarsu take.shi kam dad har ya auri wata matar mai kirki ko su su Jamila sun yaba da kirkinta zama na jin dadi sukeyi sosai.
Tunda Hawwa ta dawo ko musu bai kara hadata da Yusuf ba itama Jamila ta ja girmanta zaman su sukeyi lafiya babu ha’inci Hawwa tazama barrister girma ya shigeta bayan twins ta haifi yara hudu yanzu haka twins hannun Jamila suke sakamakon rashin haihuwarta kuma an tabbatar mata da mahaifarta ta lalace saboda magungunan da taita sha shiyasa gaba daya Hawwa ta tausaya mata ta ba Yusuf shawarar abata su Allah ya raya da yaso yaki amma Hawwa ta lallaba shi suka koma hannunta haka ta rike su amana kuma tana jin yaran aranta.
Nabila tana da yara hudu biyu maza biyu mata sannan Fatima na da uku duk mata Nafisa kuwa da ba’a dade da bikinta ba tanada ciki yanzu.
haka rayuwa ke tafiya cikin jin dadi da kwanciyar hankali abubuwa sun faru da dama bayan wasu shekaru wata yarinya na hango wadda zata kai shekara 17 tana saukowa daga matattakalar jirgi tare da wani kyakyawan saurayi sai iyayensu guda manyan mutane suma cikin haiba da kamala saida na kura ido sosai nagane Minal ce da Afan ashe hadin da Umar yayi tunda aka haifesu ya hadu soyayya sukeyi sosai don ma ita tana cewa ai ta girmesa amma dai duk da haka tana son abunta.
Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah….Barrister Hawwa da Doctor Jamila nabarku lafiya Allah ya kara hada kanku agidan Alhaji Yusuf.
Ina ma Allah godiya daya bani ikon kammala wannan littafin nawa lafiya kurakuren danayi Allah ya yafe mana inda aka karanta yayi amfani Allah yasamu cikin ladan gaba daya dafatan anji dadin kasancewa tare dani awannan littafin Tun Ina Karama!!!Allah yasa muyi amfani da darasin dake ciki kuma ina fatan sakon da nake son isarwa ya isa.wato arayuwa duk wanda ya rike Allah da Manzon Allah ya gama komi. kuma iyaye mu daina sanya ya’yanmu akan hanyar banza kada mu nuna masu duniyace gaba da komi wannan ba dai dai bane Allah yabamu ikon gyarawa.Ameen
[ad_2]