HAUSA NOVELTUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

 

 

Duk abun nan dake faruwa tsakanin yusuf da hawwa, su jamila na kallonsu tana cikin motarta inda tayi parking suna zaune itada kawarta dama suna jiran ganin shigowar yusuf sbd ba kowa zai lura da ita ba a inda tayi parking suna zaune ita da kawarta samira wanda dama samira ce ta shiga ta dauko wannan hoto wanda shi kanshi wanda ta hada tayi masu hoton baima san tanayi ba har tagama kulla sharrinta ta fito.motad yusuf na fita daga get din suka tafa ita da samira suka kyalkyale da dariyar mugunta”jamila tace yau na fara dasa masu tashin hankali atsakaninsu ke nan kinga yanda dai ya fusata gashi dama akwai zuciya kuma na lura irin mazan nan ne masu kishi kinga tunani da yawa zaiyi akanta yarinka ganin dama tana kula maza awaje”yes samira tace wannan haka yake cikin dariya samira tace to yanzu me kike ganin zaiyi mata?”jamila tayi murmushin mugunta tace ubanta zaici kawai.

 

 

Ke bakiga yanda ya fusata ba”hakane amma baki ganin mamanshi zata taka mashi burki akan hakan tunda dama kince bata son abunda zai taba yarinyar samira ta tmbyi jamila.”kada ki damu kawata shine dalilina na bata alkarsu sbd uwarshi ta dauki burin duniya ta dora ma wannan shegiyar yarinya walhi na tsaneta mtsss nasan zata fusata da zaran mata wani abu kuma kinga daga nan sai abubuwa su fara canzawa nikuma alkcn zan fara game dina wanda duk families dinmu zasu san muna tare da juna walhi samira zan iya aiwatar da komi akan yusuf bcos ilove her with all my heart:hmmm kawata komi zaiyi dai dai don ma mommy bata kasar amma komi zai zama normal”samira ta jinjina kai alamar gamsuwa da maganar kawartata.”jamila tace mu wuce ko?”samira ta amsa mata da eh, haka suka tashi mota suka fita dama abunda ya kawo su kenan kuma sun ai watar zuciyarsu wasai saura suji feedback

 

 

 

Nabila ta duba bataga hawwa ba kuma ga wayarta a hannun ta bare ta kirata.haka ta yanke shawarar fita waje don tasan haww ba hayaniya take so ba, tana fitowa tayi wurin da Adamu driver yayi parking yana kwance a mota yana jiranta kwankwasa gilas din motar tayi ya tashi tare da bude gilas din yana tmbyrta nabila kin gamane?eh ta amsa masa tare da tmbyr shi hawwa bata fito bane?”ai yanzu ba dadewa yallabai yazo suka tafi .cikin razana tace yaya yusuf yazo nan lfy dai ko?walhi bansani ba amma dai naga ranshi a bace yake, “ta jinjina kai tace Allah dai yasa lfy” Amin ya amsa mata ta bude motar ta shiga ya ja suka tafi cike da tunanin me ya faru aranta.

 

 

Hankali atashe yake tafiya da mota sbd gudu kawai yakeyi kamar zai bar gari .nidai jikina rawa kawai yakeyi zuciyata na bugawa tunda nashiga motar kafin mu shiga unguwar mu naga ya gangare gefen titi yayi parking, cikin razana na dago kaina da nufin yin mgn “waye shi?naji yace, cikin rashin fahimta bansan abunda kake nufi ba” ki fada mani tsawon wane lkc kuke tare shi?yakara tmby, “walhi yaya bansan abunda kake nufi ba.juyowa yayi cikin tsawa!yace shut up!my frnd ki sanar dani alakarki da shi tun kafin ranki ya baci!bansan lkcn da kuka ya kufce nani ba nace ni bansan komi ba amma kaki yarda.” ok kawai yace tare da jefo mani wayar shi akan cinyata duba kigani tunda nasa ba yi maki karya, cikin sauri na dauki wayar tare da ganin wani pic nawa da wani saurayi kamar muna mgn ina dariya

TUN INA KARAMA????????????????????????????????

 

 

By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!

 

 

Page 10

 

 

……….cikin sauri na dauki wayar nice zahiri ba karya amma ban san wanene wanda yake kusa dani ba har ina dariya nasan dai fatima kawata nake magana da ita a lkcn amma ya akayi wannan mutumin kusa dani haka.na shiga uku!an bata ambata wallahi yaya ban san shiba asalima nasan na tsaya wurin nan amma bada shi nake maganaba amma ban sanshi ba yaya cikin kuka na karashe maganata tare da jin wani zafi a zuciyata “tunda nafara magana yake kallona yaso ya gasgata maganata amma kishi ya hana yaga hakan tare dani.” Ok bani wayata na mika mashi zan kara magana ya daga mani hannu sbd gaba daya kukan da nakeyi har cikin ranshi yake jin shi.kamar bashi yayi maganar ba naji yace hawwa aure kike so?cikin sauri na girgiza kai alamar a’a to ko ba kiso yazama dole sbd bazan iya wadannan abubuwan”walhi yaya banida saurayi bare ince ina son aure to wazan aura?

 

 

 

Bayan nasan bani da kowa kuma karatu nake buri.na cigaba da cewa duk wanda yayi mani sharri bazan yafe masa ba tunda ban aikataba, “batare daya kalleni ba ya tada mota tare da cewa ki cigaba da shirye shiryen aurenki nan da lkc kankani insha Allahu.wayyo Allah !nace shikan shi saida ya tsorata afusace yace kika kara yi mani ihu amota sai na fasa baki.nasa hannu na toshe bakina, ya figi mota muka karasa cikin unguwarmu.muna isa gida cikin get din gidanmu, tun kafin ya gama parking na balle marfin mota na shiga gida da gudu tare sakin kuka mai karfi ummace tare da nabila suna maganar to ina muka tsaya ba iso ba

 

 

Ba ” nabila tace ma ummah Adamu yace rai bace yaya yazo cikin mamaki tace to koma menene ai sai ya dawo mani da ita gida ko.bata rufe baki ba na fado falon da kuga gaba daya juyo sukayi cikin mamaki suna tmbyta me yafaru?cikin kuka nace umma kada kibari yaya ya fadi Abbanah ina son aure na hade hannuwa na alamar rokonta.cikin rashin fahimtar maganata ta zaunar dani kan kujera nabila kuma ta zauna gefena tare da rike hannuna “ummah tace wai meke faruwa?waye baki so kuma?” Yusuf ne ya shigo tare da sallama amma fuskar nan tashi babu annuri sai ji sukayi yace dama kin daina kuka ki fara shirin aurenki.”cikin daga murya umma tace wace by irin mgn kakeyi yusuf?me ya faru ne?”umma ki tmby ta abunda tayi dama ni nace abarta ta fara jami’a to yanzu ra’ayina ya canza zan jira dawowar Abbah tunda ya fara mgn umma ke kallonsa tana nazarin irin soyayyar hawwa tsantsa a idon shi da kishin ta cikin kauda kai umma tace baka isa ba yusuf babu wanda zai takurata da mgnr aure”amma umma ya kamata ki saurareni mana”cikin tsawa tace banda lkcn saurarenka zai kara mgn ta daga masa hannu tare da cewa ya isa haka bai kara mgn ba ya nufi sashensa yana jin wani zafi a zuciyarsa ta juyo tace na nabila tashi ku shiga daki ku kwanta.

 

 

Masha Allah don Allah frnds kuyi hkr da typing din nan ba yawa sakama kon ina cikin hidamar biki ne next page zan biya bashi.ku biyoni ???????????? taku ce sa’ar mataaaaa????

TUN INA KARAMA ????????????????????????????????

 

 

 

By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!

 

 

Page 11

 

 

……….( koda ya wuce daki yana shiga ya cire kayan jikin shi ya wuce toleit yayi wanka, wanda ya zame mashi jiki duk idan zai kwanta sai yayi wanka.haka ya gama ya fito daure da towel ajikinsa yana daure da daya yana kuma tsane jikinsa da dayan saida ya gama goge jikinsa sanna ya dauko mai lotion din shi mai dadi da laushi yabi jikin sa ko ina ya shafa sanna ya dauko spray dinsa na jiki ya fesa ko ina haka ya gama shirinsa na bacci ya dauki wasu kaya T shit fara da shot nick yasanya ya dauko lapton dinshi ya dawo falo ya zauna da niyyar duba wani aiki da yake son kammalawa amma abun ya gagaresa gaba daya ji yayi baya iya aiwatar da komi, haka ya tashi yakoma cikin bedroom din sa ya kwanta ba don yana jin dadi ba.tunanin kawai yakeyi aransa ina zai samu mafita?yasan dai umma ba sauraren.gsky dana bi shawarar Abba dayace in fito ayi mani aure da hawwa da haka bata faru ba gashi tun ba’aje ko ina ba abubuwa na shirin lalacewa .naso in barta ta fara karatu domin ta kara samun wayewa ne amma kash, kishinta bazai barni ba ina sonta itace mace ta farko dana ke jinta araina amma bata sani ba ina ganin tayi kankanta da zan nuna mata wacece ita agareni.don har yanzu kallon dan uwanta takeyi mani na jini ba wai ta fahimci sona take ba.gsky nayi kuskure yakamata hawwa ta san tun tana karama nake dakon sonta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button