TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Kuma ai ina nuna mata banbanci tsakaninta dasu nabila da nafisa kuma me yasa dana tafi india kullum mukayi waya sai tayi kuka wai in dawo kuma umma tana fadi mani in rike alkawari kada in yarda wata mace ta shiga rayuwata bayan hawwa don ta lura hawwa akwai soyayyata mai tsanani atare da ita gsky akwai sona ranta saidai bata fahimci sona take ba.haka dole ya samu mafitar cewa mami ce kadai zata nuna ma Abba ya amince cikin sauri ayi auren nan namu.dole ne gobe insha Allahu inje kaduna in samu mami da mgnr.haka bacci barawo yayi gaba da shi.itama hawwa da nabila haka suka shiga daki tare da tunani kala_kala wanda mamaki ya hana su kwanciya kowa da abunda yake tsakawa akan abunda ya faru, haka nabila ta zaunar da hawwa bakin gado itama ta zauna cikin damuwa”ta dafa kafadarta tace hawwa kiyi hkr insha Allahu komi zaiyi daidai amma ki bari kawai koma waye yayi mana wannan abu Allah zai tona masa asiri”cikin kuka nace ni walhi nabila yanda naga yayana ya dauki abun ne tsoro ya kamani yanzu idan har Abbanah yaga wannan pic din ai na shiga uku nabila”nabila tace kema kinsan yaya bazaiyi haka ba kawai dai abunda na lura kishi ne kawai ya ruda yaya, cikin hanzari hawwa ta daga kai ta kai dubanta ga nabila “tace kishi kuma?jinjina mata kai nabila tayi alamar gsky ne ” to ni sbd me zaiyi kishina?sbd yana sonki to ai kuma yana sonku A a hawwa yana mana so na yan uwantaka ne amma ke soyayyace tsakaninki dashi.”haba nabila ni bai taba cewa yana sona ba ai ba sai yace ba mu da muke tare daku mun gane ai juya wa nayi na kwanta nace bar mgnr nan saida safe.
Haka muka tashi da asuba mukayi sallah da addu’oin mu tare da tilawar alkur’ni mai girma, wanda dama mun saba saida gari ya fara wayewa muka tashi.na kalli nabila nace mata sis zan dan koma in kwanta don kaina ke dan ciwa ok ba damuwa tace ki kwanta ki huta ni zanje in taya Asabe break.to shikenan nace na koma na kwanta.nabila tana shiga sashen umma ta shiga dakin tare da sallama.umma tana hada wasu kaya da zatayi amfani dasu ta juyo ta amsa ma nabila sallam cikin fara’ da kulawa nabila har kasa ta tsugunna ta gaishe da umma bayan sun gama gaisawa na ta tmby hawwa ko lfy nabila ta amsa da bacci ne ta koma ta kwanta”umma tace to ba damuwa kema ki koma ki kwanta mana a a ummah zan taya Asabe ne break to shikenan ki sameta kichen din.yaya yusuf koda ya tashi da asuba yaje masallaci ya dawo ya gama abunda yakeyi ya shirya tsab tunda ya gama yanke hukuncin tafiya wurin mami kaduna.bayan ya gama ne ya fito ya wuce part din ummah ya shiga dakinta tare da sallama ta amsa masa ba yabo ba fallasa bayan sun gaisa ne yake sheda mata tafiyar da zaiyi kaduna .hmmm kawai tace tare da fadin Allah ya tsare hanya yasa a adawo lfy.Amin ya amsa mata tare da jin dadin addu’arta gareshi, sbd duk fushin da ummah tayi bata fasa yima yaranta addu’a haka ya tashi duk da baida wata walwala amma yaji ranshi ya fara sanyi.bayan ya futa ta girgiza kai aranta tace zan nuna maka darajarta kafin in tabbatar maka da aurenta bazan bari ka rasata don ita ta dace da rayuwarka insha Allahu.bayan ya fita yaje wurin motarsa tare da budewa ya saka jakar lapton dinsa ya shiga motarsa tare da Addu’a yayi rivos ya nufi get baba ya bude masa tare da ftn alkairi ya amsa da amin
Yana fita bai zame ko ina ba sai wurin umar.to frnd dama shiyasa nace maka indai har zaka saurari jamila to zata samu galaba akanka yanzu kai ka yarda da wannan pic din?da har zaka tada hankalinka?umar yace ni dai ban yarda ba walhi amma kuma auren naku shi zafi tun wuri kafin wannan shidaniyar ta lalata komi ya kamata ka baiyana ma hawwa tun tana karama kake kaunarta simple.yusuf ya sauke ajiyar zuciya tare da kallon agogon hannunsa yace yakamata mu wuce ko?”umar ya daga kai alamar eh haka suka fito daga part din umar inada suka samu Ammi a falon gidan su umar suka gaisheta cikin girmamawa Ammi tace yusuf yasu hjy ya amsa da lfy klau Ammi “to masha Allah Allah ya taimaka suka amsa da Amin suka mike tsaye zasu tafi umar yace Ammi zamuje kaduna sai yanda ta yiwu to ba komi Allah yasa adawo lfy amin suka amsa suka fita tabi su da kallo tana jin dadin alakarsu sosai haka suka shiga motarsu suka fita umar na tuki sai kaduna garin gwamna sai muce Allah yasa a dace yusuf.
Bayan na tashi wurin karfe 10:30 sbd babu wanda ya tasheni saka makon umma tace abarni in huta.ina tashi da addu’a bakina tare da salati na mike na shiga toleit bayi wanka na fito na shafa mai ajikina tare da spray masu dadi ina cikin bude drawer ne in dauko rigar da zan sanya sai wata leda ta fado ina kai hannuna zan dauka gabana ya yanke ya fadi cikin sauri naje wurin window na yaye labulan inda yake parking babu motarsa ya salam!ina ka tafi bayan kace yau zamu bude wannan ledar yaya?why why kayi avoiding me?
To fah???? yanzu aka fara wasan fa menene burin jamila yaya hawwa zata dauki aurenta da yusuf?wace irin kalubale ke tare da rayuwarsu?to koma me kenan mujira dawowar Abba, ngd da kauna masu biyoni a pc suna nuna mani soyayyarsu da littafina mai suna tun ina karama????insha Allahu nima ina tare daku don jin dadinku ????????????masha Allah sai mun hadu a next page takuce ???????????? sa’ar mataaaa????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 7
ASALIN LABARIN:
…….waye yusuf Bashir mado kankiya?Alh Bashir mado kankiya haifafan cikin garin kankiya ne dake jahar katsina Alh bashir su hudu ne wurin mahaifinsu.Alh bashir shine babba a cikin su da shi da kanin sa Alh bello sai kanwar su hjy mariya dakuma autar su rabi atu.sun taso cikin jin dadi da walwala ta rayuwa, sakamakon mahaifinsu yana da ilimi na addini dana zamani yasa yazama wayayye kuma gashi yana amfani da iliminsa wurin iya mu amula da mutane.sannan ga tarin dukiya Allah ya hore masa, yana kasuwancin shi cikin ilimi da gogewa ta rayuwa.matar shi daya hjy hauwa’u wadda itace mahaifiyar su Alh bashir.sunyi auren soyayya da Alh mado itama yar cikin garin kankiya ce.sunyi zama na soyayya da Alh mado wanda har Allah ya azurta su da haihuwar yara guda hudu, shima Alh bashir koda yake dan boko to ya biyo baban shi wurin son business sosai don tunda ya taso ya gama karatunsa na degree akan business ne yayi karatu har master’s din shi.
Shi kuma Alh bello gsky yafi karfi a govment sbd yanzu haka shine commissioner na manoma watau agric.ita kuma hjy mariya sakamakon mijinta mai haline yana da tarin dukiya sosai shiyasa ita bata aiki sai kawai ta fada harkar kasuwanci, tana fita dubai tana kawo kaya sosai.sai Rabi’atu wadda itama tayi aure amma tana aiki da ma’ikatar lfy ta kano.gaba dayansu kowa yana da rufin asiri daidai gwargwado sbd Alh moda koda yake da kudi bai yarda ya bar yaranshi ba babu ilimin addini dana zamani ba.bayan rasuwar maifinsu ne Alh mado Alh bashir ya koma katsina da zama a inada ya auri diyar aminin babansu Alh garba mai dala.wadda dama suna soyayya dashi wadda hakan yasa iyayensu sukayi masu alkawarin auren junan su kuma Allah ya kaddara.shikuma Alh bashir dalilin dayasa ya koma katsina da zama sbd duk harkokin mahaifin shi suna can to koda y rasu sai ya tattara gaba daya ya koma da zama.yaso ya tafi da mahaifiyasu amma ta nuna mashi tafi son zamanta anan kankiya cikin danginta haka nan ya hakura badon ranshi yaso ba.amma duk satin dunya yana zuwa ya kwana biyu wurin mahaifiyarsa saidai idan baya kasar.kuma yana zuwa da matarsa hjy khadija wadda mace ce mai karamci da nuna kulawa ga yan uwan mijinta shiyasa ta shiga ran kowa na family dinsu Alh bashir .ita kanta hjy hauwa’u tana kaunar sirikar tata sosai bata son taji ance ga laifinta.shikuma Alh bashir ganin yanda take kula da mahaifiyarsa da yan uwansa yasa yake kara ganin darajarta da kimarta.