TUN INA KARAMA Complete Hausa Novel

Innalillahi wa’innailaihin raju’un, haka kawai yake maimaitawa.sakamakon wasu hotona da jamila ta tura mashi na hawwa tare da wani saurayi kamar suna mgn ita kuma hawwa tana dariya wanda ita bama tasan saurayin yana kusa da ita haka ba.
Jikin shi har rawa yakeyi yasa hannu ya dauki key din motar shi a sukwane ya fiti falo babu umma hakan ya bashi damar fita kawai inda yayi parking ya nufa ya shiga motar a rude sbd tsabar kishi.baba mai gadi ya bude mashi get tare da daga masa hannu adawo lfy yace.haba ina ko ji bayayi haka ya fita cikin tashin hankaki da rikicewa hoton hawwa kawai yake gani tana yima saurayin nan dariya.hawwa kina sona kuwa?me nayi maki?
Masha Allah ku biyoni yawan comment yawan typing ???????????? taku ce sa’ar mataaaa ????
TUN INA KARAMA ????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 9
……..”haka yaketa maimaitawa yana tuki amma gaba daya hankalin shi yana wurin wannan hoto.cikin minti kalilan ya isa liyafa place haka ya shiga ciki.daidai inda motar Adamu driver take yayi parking.cikin hanzari Adamu ya fito yana karasawa wurin shi lkcn da ya bude mota ya fito hannuwan shi cikin aljihun wandon shi, duk dayake cikin bacin rai ba karamin kyau yayi ba.Adamu yace yallabai barka da isowa, yauwa kawai yace atakaice.ina suke?ya tmby shi “ai suna ciki ranka shi dade bai rufe baki ba saiga hawwa ta fito daga hall din tana neman nabila don ta gaji tana so tafi gida haka nan, daidai inda motar su take ta hango Adamu shida yaya yusuf .cikin faduwar gaba ta ambaci yaya yusuf kuma anan?cikin sauri ta nufi wurinsu inda tunda ta fito suka hangota sbd hasken fitilun dake wurin.Adamu ne ya katse shirunsu da cewa gama autar hjy nan isowa.
Yanda taga alamunshi, tasan akwai matsala haka ta karasa jiki ba kwari cikin tsoro tace yaya kaine?” Shiga mota kawai yace mata”yaya nabila kafin ta karasa ya daka mata tsawa!wanda har Adamu saida ya firgita”shiga mota ya sake cewa cikin rudewa ta bude motar ta shiga.ya juyo yace m Adamu kajira nabila ka taho da ita.cikin girmamawa ya amsa da to yallabai.afusace ya isa wurin motarsa ya bude ya shiga ya fita a180_200 hhhh ran maza ya baci to hawwa ina tausaya maki hannun yusuf???? Adamu mamaki kawai ya hanashi motsi har na tsawon minti biyu atsaye sannan ya juya ya koma wurin motarsa cike da tunanin mai ya bata ma oga rai haka?to koma menene Allah ya kyauta.
Duk abun nan dake faruwa tsakanin yusuf da hawwa, su jamila na kallonsu tana cikin motarta inda tayi parking suna zaune itada kawarta dama suna jiran ganin shigowar yusuf sbd ba kowa zai lura da ita ba a inda tayi parking suna zaune ita da kawarta samira wanda dama samira ce ta shiga ta dauko wannan hoto wanda shi kanshi wanda ta hada tayi masu hoton baima san tanayi ba har tagama kulla sharrinta ta fito.motad yusuf na fita daga get din suka tafa ita da samira suka kyalkyale da dariyar mugunta”jamila tace yau na fara dasa masu tashin hankali atsakaninsu ke nan kinga yanda dai ya fusata gashi dama akwai zuciya kuma na lura irin mazan nan ne masu kishi kinga tunani da yawa zaiyi akanta yarinka ganin dama tana kula maza awaje”yes samira tace wannan haka yake cikin dariya samira tace to yanzu me kike ganin zaiyi mata?”jamila tayi murmushin mugunta tace ubanta zaici kawai.
Ke bakiga yanda ya fusata ba”hakane amma baki ganin mamanshi zata taka mashi burki akan hakan tunda dama kince bata son abunda zai taba yarinyar samira ta tmbyi jamila.”kada ki damu kawata shine dalilina na bata alkarsu sbd uwarshi ta dauki burin duniya ta dora ma wannan shegiyar yarinya walhi na tsaneta mtsss nasan zata fusata da zaran mata wani abu kuma kinga daga nan sai abubuwa su fara canzawa nikuma alkcn zan fara game dina wanda duk families dinmu zasu san muna tare da juna walhi samira zan iya aiwatar da komi akan yusuf bcos ilove her with all my heart:hmmm kawata komi zaiyi dai dai don ma mommy bata kasar amma komi zai zama normal”samira ta jinjina kai alamar gamsuwa da maganar kawartata.”jamila tace mu wuce ko?”samira ta amsa mata da eh, haka suka tashi mota suka fita dama abunda ya kawo su kenan kuma sun ai watar zuciyarsu wasai saura suji feedback
Nabila ta duba bataga hawwa ba kuma ga wayarta a hannun ta bare ta kirata.haka ta yanke shawarar fita waje don tasan haww ba hayaniya take so ba, tana fitowa tayi wurin da Adamu driver yayi parking yana kwance a mota yana jiranta kwankwasa gilas din motar tayi ya tashi tare da bude gilas din yana tmbyrta nabila kin gamane?eh ta amsa masa tare da tmbyr shi hawwa bata fito bane?”ai yanzu ba dadewa yallabai yazo suka tafi .cikin razana tace yaya yusuf yazo nan lfy dai ko?walhi bansani ba amma dai naga ranshi a bace yake, “ta jinjina kai tace Allah dai yasa lfy” Amin ya amsa mata ta bude motar ta shiga ya ja suka tafi cike da tunanin me ya faru aranta.
Hankali atashe yake tafiya da mota sbd gudu kawai yakeyi kamar zai bar gari .nidai jikina rawa kawai yakeyi zuciyata na bugawa tunda nashiga motar kafin mu shiga unguwar mu naga ya gangare gefen titi yayi parking, cikin razana na dago kaina da nufin yin mgn “waye shi?naji yace, cikin rashin fahimta bansan abunda kake nufi ba” ki fada mani tsawon wane lkc kuke tare shi?yakara tmby, “walhi yaya bansan abunda kake nufi ba.juyowa yayi cikin tsawa!yace shut up!my frnd ki sanar dani alakarki da shi tun kafin ranki ya baci!bansan lkcn da kuka ya kufce nani ba nace ni bansan komi ba amma kaki yarda.” ok kawai yace tare da jefo mani wayar shi akan cinyata duba kigani tunda nasa ba yi maki karya, cikin sauri na dauki wayar tare da ganin wani pic nawa da wani saurayi kamar muna mgn ina dariya
TUN INA KARAMA????????????????????????????????
By sa’adatu Bello saadatu99@gmail.com!
Page 10
……….cikin sauri na dauki wayar nice zahiri ba karya amma ban san wanene wanda yake kusa dani ba har ina dariya nasan dai fatima kawata nake magana da ita a lkcn amma ya akayi wannan mutumin kusa dani haka.na shiga uku!an bata ambata wallahi yaya ban san shiba asalima nasan na tsaya wurin nan amma bada shi nake maganaba amma ban sanshi ba yaya cikin kuka na karashe maganata tare da jin wani zafi a zuciyata “tunda nafara magana yake kallona yaso ya gasgata maganata amma kishi ya hana yaga hakan tare dani.” Ok bani wayata na mika mashi zan kara magana ya daga mani hannu sbd gaba daya kukan da nakeyi har cikin ranshi yake jin shi.kamar bashi yayi maganar ba naji yace hawwa aure kike so?cikin sauri na girgiza kai alamar a’a to ko ba kiso yazama dole sbd bazan iya wadannan abubuwan”walhi yaya banida saurayi bare ince ina son aure to wazan aura?
Bayan nasan bani da kowa kuma karatu nake buri.na cigaba da cewa duk wanda yayi mani sharri bazan yafe masa ba tunda ban aikataba, “batare daya kalleni ba ya tada mota tare da cewa ki cigaba da shirye shiryen aurenki nan da lkc kankani insha Allahu.wayyo Allah !nace shikan shi saida ya tsorata afusace yace kika kara yi mani ihu amota sai na fasa baki.nasa hannu na toshe bakina, ya figi mota muka karasa cikin unguwarmu.muna isa gida cikin get din gidanmu, tun kafin ya gama parking na balle marfin mota na shiga gida da gudu tare sakin kuka mai karfi ummace tare da nabila suna maganar to ina muka tsaya ba iso ba