UBAYD MALEEK 26

Ganin jekadi cikin yanayin ba daidaiba yasata fitowa dakin gabaki daya tana rufewa tareda kallon jekadin cikin mamaki tace”

Lafiya kike jekadi?

Bakida lafiya ne?

Girgiza Kai tayi wani irin mummunan gumi dayafi kamada Ana sheka Mata ruwan zafi Dan har tsiyaya take ta bude Baki daqyar a Dan wahalce tace”

MALEEK….kije kidubo MALEEK….guba..gubar qona jini a tea…..

Arude NURU take kallon bakin jekadi kayan cikinta na juyawa tsabar kaduwa tace”

Guba…maleek kuma?….

Turata jekadi tayi tana cewa”

Kije da sauri kidubosa akwai matsala babba.

Juyawa tayi da gudu tana waiwayen jekadi akaro na farko tana hawa Daman MALEEK dukkanin jikinta na rawar tsoro da firgici itakuma jekadi Kai tsaye dakin padima ta Isa ta Sanya  mukulli daga waje kafin tafada dakin mum Sarah tana fidda wani gurnani azaba da wahala.

Tana Shiga qaton palonsa na farko taga Kofa biyu daya ta palonsa na biyu daya ta dakin matarsa lailah Bata tsaya komaiba ta nufi wadda qafafunta suka jata zuwa ta bude da sauri ta fada nanma wani palon ne tana hango kofar Master bedroom dinsa ta nufa da gudu ta fada ko ganin gabanta sosai batayi.

Cak ta tsaya tsakiyar dakin sbd fitowarsa wanka kenan dagashi sai towel iya qugunsa dukkanin fatar jikinsa tayi jajir kamar anmasa duka da danqo

Hankalinta take yaqarasa hargitsewa tanabin jikinsa da kallon qafafuwanta na daukar rawar tashin hankalin ganin wannan mummunan al’amarin.

Sbd jininsa nada tsananin karfi yasa yake iya controlling tsananin azaba da radadin dayakeji na juyawa cikin jininsa ya dauke idonsa daga kallonta tareda juya Mata baya sbd rashin kayan jikinsa.

Ganin masifar tafi yawa abayansa yasa batasan lokacinda ta qaraso da guduba ta Dora duka tafin hannuwanta a tsakiyar bayansa Wanda yasa wata ajiyar zuciya me qarfi kufce Masa sbd wani sanyin saukin azabar dayaji 

ya juyo gabaki daya Yana kallonta hannuwanta akan jikinsa ya lumshe fararen idanuwansa dasuka koma jajir yabudesu fes akanta.

Ba sha’awar mace yakejiba ko kadan sbd komaima bazai iyaba ayanxun sbd konuwa da tafasar dayakeji acikin jikinsa Amma haduwar jikinta da nasa ya raunana azaba da zafin dayake ji sosai

 yasake ware idanuwansa akanta tareda matsowa cikin jikinta sosai tayi saurin kasa da ido zuciyarta na harbawa haryana iya gani ta saman kirjinta

Hannu ‘daya yasa ya zagayota tareda matseta cikin jikinsa yasakejin wani sanyi yasake sauke ajiyar zuciya tareda Dan sassautawa yana kallon fuskarta daidai ta dago zuciyarta na harbawa da tsoro da firgici da komaima ta kallesa idanuwansa suka shiga cikin nata kusan atare suka sauke ajiyar zuciya

Ya dago hannunta ahankali Yana kallon fuskarta ya Dora kan botiran rigar baccinta

Ta maida idonuwanta ahankali ta rufe bugun zuciyarta na tsananin Tues tanaji Yana bude botiran rigar har qarshensu rigar ta zame a tsorace ta rungumesa sbd kirjinta dake bayyane qyam.

Atare suka sauke qaqqarfar ajiyar zuciya musamman shi dayaji sanyi na shigarsa ya rungumeta gabaki daya cikin jikinsa idanuwansa alumshe.

##MAMUH#

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button