UBAYD MALEEK 27

Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?

Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace”

Bansaniba 

Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin 

Abu daya tace shine na jininta na quna.

Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace”

Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu 

Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.

Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al’amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?

Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.

Bude ido tayi ahankali tasake lumshewa har lokacin tanajin dumin jikinsa daya Shiga jikinta sbd ba qaramin full body contact suka samu ba Dan ita yacire rigarta shikuma dama Babu anasa jikin.

Saurin rintse ido tayi da qarfi tana cire tunanin cikin ranta ta gyara kwanciya Dan tasamu bacci ya Dan dauketa kafin asuba.

##MAMUH# 

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button