UBAYD MALEEK 31

Kallonta afia tayi da tunanin idan kulawa zatashi mantawa da komai ya dangana ya warke itace tafi kowa kamata tabashi sbd itace sanadin rabasu harya shiga wannan halin Dan haka Inshallah zatai iya kokarinta gurin sauke wannan alhakin dake kanta ko Dan haqqinsu ya sauka daga kanta.
Shiru sukayi dukkaninsu kowa da tunanin daya Dan fada musamman NURU datake ganin gwara Imran din yasan rashinta shine takamaimai matsalarsa idan yaso yaqar matsalar Yana tilastawa kansa mantawa da ita shikenan yayi maganin tasa matsalar
Amma ita haryanzu batasan matsayin kantabama bare tasan meye tata matsalar hartakai ga maganinta
Ita kawai rayuwar take aduk yanda tazo Mata.
Qarfe biyu Sukayi wanka suka shirya
afia ta fita zuwa Taya farhat shiryawa tabar NURU na sauya wasu kayan sbd riga da wando tafara sakawa taga basuyiba ta sauya zuwa riga da skirt Suma taga basuyiba qarshe ta Sanya wasu maroon _Yves Saint Laurent_ riga da wandon Palazzo dasuka fiddo zallar yarintarta na matashiyar wayayyiya musamman kalar ta yiwa fatarta kyau ta Sanya wedges takalmin _CH/HC carolina Herrera_ black tazo gaban mirror zata fesa turarukansu dake jere saita fasa ta dauki _Lady l_ na _Acqua di parma_ ta fesa Wanda ya hadu da kamshin body mist dinta da spray na _ royalle Nina Ricci_ suna bada qamshinda sai ka kusantota sosai zakajishi
Tana daura scarf a kanta afia tashigo ta Isa gaban mirror tasake gyara fuskarta ta juyo tace”
Everyone is waiting for you fa kowa yafito.
Wayarta kawai ta dauka Banda handbag suka fito tareda afia din wadda itakuma heels ne takalmanta kusan Koda yaushe.
Suna fitowa Palo farhat tayi gurin NURU da duk ta cika musu ido musamman padima datake Mata kallon qyashi kafin ta dauke Kai tana sakin boyayyan tsokin da NURUn taji Amma ta qyale kaman bataji komaiba suka fito dukkaninsu afia ke driving sai ita NURUn a gaba sai padima da farhat sai jekadi a bayan.
Mr Omar yaso NURU tabi motar driver sbd ganin kaman sunyi yawa a motar Amma tace tafi buqatan cikinsu din suka fice Yana musu adawo lafiya.
Gurin wasan farhat suka fara zuwa sukayi kusan 2 hours agurin kafin suka fito suka tafi wani qaton mall
acan suka Bata lokaci sosai Dan sai yamma sbd irin kayan da padima tayita dauka Babu Wanda yace tabari
Dan kanta dataga kayan sunmata nauyi tabari suka fito aka aika duka siyayyan kayan dasukai direct zuwa gida da motar mall din.
Har zasu fito afia ta nufa bakery dinsu akai Mata packaging cupcakes guda shida masu icing na chocolate kadan ta biya ta karbo ta nufosu NURU ta kalleta tana cewa”
Mezakiyi da cupcakes?
Zamu biya dubiyan Imran a hospital so nayi tunanin abinda zamu Kai bansaniba kila wannan zaiyi.
Mum manta duka amma da a gida za’ayo Masa wannan din Amma ko hakan ma inaga yayi.
Mota suka shiga suka nufi hanyar asibitin farhat se murna takeyi zataga Uncle Imran sbd akwai shaquwa da sabo tsakaninta dashi Dan Kam acikin dangin mahaifiyarsu shikadai tasani duk da shima bawai tasan asalin asalin alaqarta dashiba kawai abinda tasani uncle Imran kaman family dinsu ne.
Suna Isa harabar asibitin sukai parking dukkaninsu suka fito NURU da afia ne agaba sauran na biye dasu NURU na riqeda hannun farhat wadda sai tsalle tsalle take tana cewa”
Aunt NURU mu bamu siyawa uncle imran komaiba kaman afia.
Murmushi tayi tana cewa”
Munkawo Masa addua ai muma.
Receptionist suka tambaya room number din Imran jalal tafada musu a third floor room 10.
Suna zuwa kuwa dakin na farko farko afia ce tafara knocking tareda bude kofar ta tura tashiga ahankali da sallama abakinta saidai ganin wadda ke dakinta yasa dukkanin bakinta qafewa saidai gudun wani tashe tashen bacin Rai da bazasu qari kowa da dadiba yasa ta danne ta qarasa shigowa dakin NURU da afia suka shigo hannun farhat har lokacin yana riqe acikin hannun NURU.
Kallo daya NURU tayiwa Matar dake zaune ta dauke wuta zuciyarta na harbawa da qarfi ta dauke Kai ahankali tana kallon afia da yanayinta ya sauya gabaki daya ta maida kallonta kan dad din Imran din dake tsaye da Alama fita zaiyi duk saitaji tana neman shiga wani mummunan hali ta samo nutsuwa daqyar cikin kannewa ta saki fuska ahankali tacewa dad din Imran din”
Ina wuni,ya me jikin?
Alhmdlh Mrs MALEEK
Ya gida?ya maleek?and fmly?
Alhmdlh sir”tafada tana waiwayowa gefen LAILAH dake zaune dukkanin qamshinta na turaren _Calvin klein boss lady_ yacika dakin tana sanye cikin wasu set na byredo ash kala komai nata kana gani kasan manyan kudadene suka siyesa musamman makeup din dake fuskarta Wanda akoda yaushe LAILAH Bata rabuwa da ita.
Wani abune ya wucewa NURU da kayar tasamu numfashinta ya saki ta bude Baki daqyar tace”
Barka da yini miss.
Wani irin murmushin tausayinsu su duka yaran tasaki sbd sai yau Allah yayi zataga matarda maleek yake aure yanzu,
Afia ta kalla zatayi magana
Afia tarigata da cewa”
Ina wuni mum.
Kin amsawa tayi tana cewa”
Wannan shine sabon manner dinki da farhat?
Da mamaki afia ta kalleta tace”
Sabon manner kuma mum?
Maida kallonta tayi kan farhat dake jikin NURU tana kallon lailah da dukkanin hankalinta sbd tanason zuwa gurinta tana shakkar irin tsawar da lailan ke Mata wani lokacin duk Bata mantaba sbd lailah batason Ana fado Mata ajiki kokuma yaro yace koyaushe Yana cikin jikinta.
Farhat kixo ki gaida mum.
Wani kallo lailah tayiwa NURU wadda gabaki daya Bata sake kallon inda lailan takeba sbd Jin take gabaki daya dakin ya gundureta ga Mr jalal ya fita ta zare hannunta daga na farhat da har lokacin take tsaye bataje gurin mum dinba ta nufi gurin Imran daya bude idanuwansa alokacin ya zuba Mata ta qarasa gurinsa ta zauna kan sofa ta qaqalo murmushi daqyar tace”
Ka tashi kenan Yaya jikin?
Bai dauke kallonsa daga kantaba ya gyada kai Yana miqawa farhat hannu cewa tazo.
Lailah zuwa lokacin ranta yafara baci sbd kowa sai acting dumb yakeyi ta gyara zama ranta nafara baci akan afia tace”
Afia nice na haifeki komai girman dakike ganin kinyi Dan haka you better stop acting dumb with me kafin ranki ya baci kokuma kinason nunamin zama da bayi kin manta girman uwarki,…
Da mamaki afian take kallon mum din cikin rashin sanin abinyi tace”
Mum please idan wani yabata Miki Rai acikinmu daga zuwanmu kiyi hkr Amma wlh Ni bansan me mukayiba anan,
Farhat kije gurin mum ki gaidata nace….
Just shut up afia
before I lose my cool ki fita daga gabana Dan Naga gabaki daya kin rasa tarbiyanki Kamar Ni Ina Miki magana kina cewa Farhat ta gaidani sbd nace Miki gaisuwan ne agabana kawai.
Hawayene suka ciko idanuwan afia sbd gabaki daya batasan metayiba da mum din keta faman wannan janye janyen ta bude Baki cikin rawar murya tace”
Kiyi hkr mum Amma dai kaman kina saukemin fadan da banawa bane.
Sai alokacin NURU da duk takejinsu ta Dan waiwayo afia din takai hannu zata dafata sbd ganin yanda hawaye suka tsinke Mata
Lailah ta aika Mata wani qanqantaccen kallo tana cewa”
Excuse me miss wannan tsakanin uwa da ‘ya ne stay within ur limits ok
Bana saka trashes cikin al’amurana
For God’s sake ma meyasa haryanxu kikeda auren MALEEK akanki bayan duniyama tasan bazaki tana zama Matar da maleek zai iya zama da itaba
Ke yarinya ce bazaki gane hakan ba Amma nasan Zaki gane kalmar pack and leave sbd ma nafasa komawa San Francisco zandawo gidan sbd afia na wannan little ant din sun dauki wani hali da bazan dauka ba..