UBAYD MALEEK 31

Jekadi da padima dake bakin kofa suna Jin komai dadin duniya yagama kashe padima duk da Jin takeyi Kamar tashiga tayiwa lailan mugun duka Amma dai Kuma yanda take nuna isarta akan ‘yayanta da NURU ta mallake yasata Jin Dadi taji inama tanada ikon shiga dakin taga yanayin NURU sbd har lokacin NURU Bata juyo ta sake kallon ko gefenda lailah maleek takeba sai lokacinda tace zata dawo rayuwar MALEEK NURU ta waiwayo ta kalleta daidai suka hada ido lailan ta gyara zama zatayi magana aka turo kofar data Sanya NURU kallon kofar da idanuwanta dasukai jajir sukai ido biyu da MALEEK Wanda Mr Omar ya budewa kofa 

Shima ita ya kalla dakyau sbd baisan da zasuzo asibitin ba Amma ganin su jekadi a waje yasa yasan suna ciki.

Dauke kanta tayi tareda maidawa kan Imran sbd rashin sanin abinyi Dan gabaki daya dakin jintake numfashinta a toshe yake.

Lailah dake zaune har lokacin ta zubawa maleek fararen idanuwanta tana jiran abinda zai fara fitowa daga bakinsa idan ya idanuwansu suka Shiga cikin na juna.

Da fararen idanuwansa ya kalli Imran dake kokarin tashi Amma Babu me kamasa sbd NURU ce kawai a kusa dashi afia har lokacin tana gaban mum dinsu hawaye take na baqin cikin wannan halin da mum ta nuna.

Cikin kamewar murya Kai tsaye MALEEK yace”

Kana samun sauqi kenan,

Allah yaqara lafiya.

Maida kallonsa yayi kan NURU dataqi waiwayowa ta sake kallon kowa ahankali yace”

Muje.

Dagowa tayi ta kallesa direct cikin ido kafin ta dauke tana miqewa tsaye da wayarta a hannu ta wuce batareda ko sai anjima tayiwa Imran ba sbd a rayuwarta Bata taba yin mummunan danasaniba Kamar zuwanta asibitin Nan yau.

Tana fitowa Jekadi ta taso zata bita Mr Omar yayi saurin Yi Mata hannu Yana  nuna Mata MALEEK da ido Takoma ta zauna tana cewa”

 Allah ya tsare hanya MALEEK.

Harya fita ko afia alamu Basu nuna yasan dasu a dakinba bare lailah harya fice,

Ita kanta afia tashiga shock

 ta dago ta kalli mum dinsu da Bata nuna damuwaba sbd tasan halin MALEEK dama Dole saita fuskanci fushinsa kafin yasan yanda zata sauko dashi dakanta sbd soyayyarta me qarfi dake ransa,

Ganin NURU yanzu datayi yasa taji bazata iya komawaba tana buqatar kasancewa da maleek yanzu Dan kuwa batai tunanin NURUn takai hakanba duk da yarinyace Amma tanada wani irin kwarjini me fizga.

##MAMUH#

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button