UBAYD MALEEK 32

Qaramin tsoki taja tana dafe goshinta sbd kanta dake sarawa tace”

Afia banason doguwar hayaniya sbd kaina Yana Dan ciwo Dan haka sai anjima idan na huta zankiraki Amma kafin Nan ki sanarwa dad dinki na shirya dawowa rayuwarku.

Shiru afia tayi da zallar mamakin mum din tace”

Mum inaga wannan ba hurumina bane ki nemesa kuyi mgn kokuma uncle jalal ya nemesa.

Da mamaki Lailah tace”

Nasan numbernsa Amma nace ki fada Masa ai.

Mum Dan Allah kidaina haka kufa iyayenane tayaya zanshiga cikin zancen maganar aurenku.

Baqin ciki yasa lailah cewa”

Idan bazakiyi abinda naceba afia karki sake kirana mum sbd bansan alaqata dakeba.

Kashe wayarta tayi tabar afia da idanuwa na cikowa da hawayen baqin cikin irin wannan uwa da Allah yabasu wadda duk duniya kanta kawai ta sani,buqatar kanta kawaice agabanta su ‘yayanta amfaninsu kawai agurinta shine irin hakan idan ta taso Mata.

Kusan Rabin abinda Lailah tafada akan kunnuwan NURU datazo shigowane taji buqatar lailan.

Kasa shigowa tayi ta juya Takoma Palo ta zauna tana Shiga wani yanayi,

Lailah zata dawowa maleek to idan tadawo ita zata tabbata a ‘yar renon farhat da gaske dinne kokuwa ma kila gaba tayi¿.

Numfashi ta sauke tareda dagowa ta kalli kofa da aka bude farhat ce tadawo daga school tayo gurinta da gudu tana Kiran sunanta.

Rungumeta daga zaunen NURU tayi tareda zare Mata school bag tana cewa”

Muje a cire Kaya ayi wanka.

Dakinta suka nufa ta tayata cire Kaya akai wanka ta dauko Mata riga da mini skirts ta Bata ta Sanya itakuma Takoma dakinsu tayi sallah tafito ta nufi kitchen tasa fana ta fito da komai suka shirya dining.

Tana Shirin komawa kitchen hada Masa nasa a tray tajiyo qamshin turarensa na shigowa ta dakata tareda juyowa daidai Yana shigowa dining room din ya zuba Mata idanuwansa dake Dan yawo akanta sbd qarara kwalliyarta da kyawun datayi suke a bayyane.

Kallonsa tayi tana bin bayan Fana data sulale ta fita da sauri ta bude Baki cikin sauti me taushi tace”

Barka da fitowa.

Bai amsaba ya qaraso gabanta kenan saiga farhat tashigo da gudu 

Saiya zauna kan kujera Yana dauke idonsa akanta.

Murmushi tasakarwa farhat tana kallonsa tajata takaita kan kujera kafin ta koma kitchen ta dauko sauran ruwa da drinks takawo.

Sai data zuba Masa komai kafin tazo gurin farhat tazuba Mata kenan saiga afia ta shigo taqaraso ta zauna kan dining din tareda kallon dad dinta tace”

Barka da fitowa dad.

Kallonta yayi yana amsawa cikin kulawa.

Harsuka gama cin abincin idon hankalin afia baya jikinta gabaki daya ita Bata cikin nutsuwarta da walwalarta.

Yana lureda ita Kuma kallo daya yayi Mata yasan matsalarta bazata wuce lailah ba, Saida yagama ya goge bakinsa da Tissue ya dago ya kalleta cikin kamewa yace”

Afia akwai matsalane?hankalinki baya kan abinda kikeyi.

Aje spoon din hannunta tayi tareda sauke ajiyar zuciya me zafi da shakkarsa cikeda zuciyarta Amma tunda ya tambaya zata fada Masa mum dintace matsalarta.

Bude Baki tayi cikin damuwa tace”

Kayi hakuri Dan Allah dad mum tadawo……

Tarin daya sarqe  NURU ba shirine yasa kowa waiwayowa Banda maleek daya jefeta da kallo daya ya miqe yabar gurin Yana cewa”

Farhat kibawa Aunt dinki ruwa.

Ficewa yayi gabaki daya daga gidan Dan dama fita zaiyi.

##MAMUH#

 

***************

Da sauri ta dago ta kallesa lokacinda ya jinginata da kofar dakin bayan ya rufe, ta kalli faffadan kirjinsa dake bayyane sbd fitowarsa wanka kenan daure da brown towel ta ‘dan juyar da kanta ahankali ta iya bude Baki tace”

Afia na Palo tare muke…

Wani kallo yayi Mata da idanuwansa dake kan fuskarta ya sake matseta jikin kofar har jikinta na mannuwa da nashi ta ja wani guntun numfashi tana Dora tafin hannunta kan qirjinsa batareda tasaniba 

Hakan yasa maganar dazaiyi ta bace masa yayi shiru Yana kallonta 

Ta sake dagowa ahankali sai suka hada idanuwa taji wani sanyi da kwanciyar hankali na shigarta sai fuskarta tafara yunqurin bayyanarda murmushi tayi saurin sauke Kai Tana motsawa ahankali sbd qamshinsa daya Gama cika hancinta Yana neman sage qafafunta.

Motsawar datake yasa qirjinta ringa gogarsa ya rintse idanuwansa Yana budesu akanta tareda yin baya Yana sakinta sbd Jin zata iya jawo damuwa.

Closet ya nufa batareda ya waiwayo ba bare ta iya gane halinda fuskarsa take ciki.

Bayansa tabi da kallo zuciyarta da dukkanin gangar jikinta na karbuwar da kowane irin sako ne yasoma isar mata.

Waiwayowa yayi ahankali ya kalleta idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke kanta tana sakin wani boyayyan murmushi Wanda yasashi juyowa gabaki daya Yana Mata kallonda yasata bude dakin ta fito da gudu tanajin gabaki daya jikinta na daukar vibration Kai tsaye dakin farhat ta nufa ta zauna bakin gado tana sauke numfashi tana warware daurin gashinta Dan tasamu iska Tako Ina ya shigeta.

Farhat dataga shigowarta tabiyota dakin itama tana tsayawa gabanta tana kallon fuskarta da mamaki tace”

Aunt NURU you’re smiling???

Dagowa NURU tayi ta kalli farhat din tana zuba Mata idanuwanta tana kallo kamanninta da mahaifinta ta janyota jikinta tayi kissing Kumatunta ahankali Yana rungumeta ahankali tace”

I love you sweetie.

Da farin ciki farhat ta maqale NURUn tana cewa”

I love you more my Aunt.

Zamansu sukayi a dakin saida kowa yashige sallar magriba tukuna ta fito ta haye saman batareda kowa yaganta ba taje sharp sharp tayo aikinta ta fito batareda shima yaganta ba sbd yafita sallah baya saman.

Kodata sauko takaiwa mum Sarah kayan gyaran dakin farhat Takoma acan tayi sallah tukuna ta fito Takoma kicin tasaka hannu a aikin hada abincin maleek din na dare ta jera a tray takai saman tadawo ta nufi dakinsu tashiga tanajin nauyi da kunyar afia nason shigarta Amma ta daure ta danne tashigo dakin tana kallon afian dake zaune da littafi a hannunta tace”

Karatu Kuma ayanxu afia?.

Kasa kallonta afia tayi tace”

Eh wani Abu na dauko Ina dubawa.

Ok kitashi anyi sallah tun dazu.

Toilet ta wuce tayo wanka tana fitowa afia tabita da satar kallo tana cewa”

Kingama aikin?

Dakatawa NURU tayi daga shafa spray ajikinta ta ‘dan waiwayo ta kalli afian tace”

Eh na gama na yau dai.

Cigaba tayi da abinda takeyi tagama tasaka kayan bacci ta fita dakin ta nufa dakin farhat acan sukasha oat suka sallar ishai sukai kwanciyarsu.

Washe gari tunda safe dakin padima ta nufa dan tayata shiri saidai padimar Bata buqata Kamar yanda tafada Mata Dan haka bata takura kantaba ta juya ta ficewarta ta nufa kitchen aikin breakfast tana gamawa ta nufi daki ta tada farhat tayi Mata wanka tareda Shirin school suka fito tabata breakfast da kanta ta rakata bakin mota driver ya wuce kaita tadawo ciki ta hadawa padima kayan breakfast a tray ta nufi dakin datake takai Mata sbd dama bakowa ke cin abincin a dining din gidan ba daga maleek sai iyalansa.

Tana shiga ajiye Mata kawai tayi ta fice 

Qarfe goma driver ya kawo mota bakin kofar shigowa Palo Yana jiran fitowarsu jekadi wadda dukkanin saqon Anneti na miqawa NURU sauran Wanda ya rage ta shanye da safiyar suka fito NURU na gefen padima data matsu su Isa gizah rayuwarta itama ta canza gaba daya.

Shiga mota tayi ta zauna tareda kallon NURU tace”

Allah yabawa kowa rayuwar daya cancanta Dan haka gamo na alkhairi uwar renon farhat.

Wani qayataccen murmushi NURU tayi zancen padiman Bai tabataba ta dago tace”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button