UBAYD MALEEK 36

Kashe wayarsa yayi ya fita harabar gidan yahau hanyar zuwa zibrian din Yana yiwa farhat ‘yar Wasa tadawo yanda take sbd yarinyar ta Dan razana da komai daya faru.

Bayan tafiyar Mr Omar ya juyo Kai tsaye ya nufi hanyar dayan bedroom Wanda ba nasaba ya Murda Kai tsaye ya tura yana kallon koina baiganta acikiba ya fito tareda rufo qofar ya nufi bedroom dinda yake gefe dabam Wanda yake matsayin nasa Yana zuwa ya bude kofar ahankali ya shiga tareda rufowa yana kallon yanda ta kwanta a dungule ya ajiye wayoyinsa kan qaramin glass table dake gefen sofar dakin ya qarasa gadon tareda tsayawa akanta Yana kallonta har saidataji mutum tsaye akanta ta bude idanuwanta ahankali ta dago dasu ta kallesa ta Mayar ta rufe tana yunqurin tashi zaune ya dakatar da ita ta hanyar Kai hannunsa daya ya maidata kwance Yana kallon wuyanta daya taba yaji zafi.

Wayarsace tayi blinkin na wuta batareda ya daukaba ya waiwaya ya kalli wayar yaga massage din Mr Omar ne daya rubuto” _Dr Damien na ya iso Yana kofa_

Zaunawa yayi bakin gadon tareda yaye bargonta ahankali tareda tayarda ita zaune da kansa Yana kallonta ahankali yace”

Dr Damien zai dubaki.

Zuba Masa idanuwanta dasukai laushi tayi tanason ce Masa Bata buqatar likita Amma sai batace komaiba ta gyada Masa Kai tana matsowa bakin gadon ta zura qafafunta qasa ya miqa Mata hannunsa ahankali ta dago ta kallesa kafin ta Dora nata akai ta Kama nasa ya miqar da ita hannunta cikin nasa suka fito Palo suka sake wucewa zuwa na farko acan suka tararda Dr Damien tareda Mr Omar dake tsaye Yana ganin fitowarsu ya sauke Kai tareda juyawa ya fice Dan Basu guri.

Daga yanda Dr Damien yafara tambayarta tabashi amsa Kai tsaye Dr Damien ya fahimci ciwonta yace”

Bawani matsala bane menstrual pains ne kawai 

Ya Bata pain reliever da wasu maganin ya miqe ya fice.

Kallonta maleek yayi Kai tsaye yace”

Kina buqatan wani Abu?

Gyada Kai tayi tana miqewa suka nufi ciki tana cewa”

Zanyiwa Mr Omar texting dinsu.

Kallonta yayi bayan sunshiga dakin ya matsota jikinsa sosai ya ranqwafo da kansa daidai fuskarta yace”

Kiyi online shopping akawo daga can Mr Omar baya buqatan sanin abubuwan dazaki buqata.

Kasa dagowa tayi ta kallesa sbd sai lokacin ma takejin kunyar ciwon nata da maganar Dan kuwa itama bazaso Mr Omar tayi Masa texting su pad da panties da kayan bacci da komaima.

Rintse idanu tayi tareda zamewa ta juya ta nufi bakin gadon ta zauna tana tunanin dame zatayi shopping din ba tunda batada wayarta atareda ita.

Miqa Mata wayarsa yayi bayan ya bude Mata password ya fice daga dakin.

Panties da bra dasu pad sai turaruka da kayan bacci data siya guda uku sbd tasan zuwa anjima ko gobe za’a kawo musu kayansu na sawa itada farhat sai brushes data siya musu itada farhat da kayan baccin farhat din tayi payment dakomai duk da komai nasa kafin ta aje wayar sbd Nanda mintuna goma zuwa Sha biyar kayan zasu iso ta miqe tareda zare doguwar rigar data Dora kan kayanta ta nufi toilet din dakin ta bude taga wani irin girmane dashi tashiga tana mamakin komai na dakin da toilet din harta tube tasakarwa kanta ruwan zafi ta gasa mararta datai nauyi Dan har lokacin be saukoba period din.

Saidata Gama ta janyo towel ta daura zata fito ta drwer jere da kalolin shavers da hair clippers a jere masu shegiyar tsada ta dauko ta kalli towel din jikinta sai alokacin tunanin dakinsa ne wannan din kenan yashigo Mata ta dafe kanta tana Jin wani iri kafin tafito.

Tana fitowa Yana zaune kan sofa yayi crossing legs Yana waya ahankali cikin nutsuwa da kamewa Amma tunda ta fito idanuwansa suke kanta duk wayar dayakeyi Kuma batareda yanayinsa ya sauya ba.

Jin idanuwansa akanta yasa takasa fita daga dakin ta nufi gaban madubinsa ta tsaya tana tunanin abinyi sai kawai taji mutum a bayanta tsaye Yana kallonta ta cikin mirror din da ido ya nuna Mata oil na Neutrogena ta Kai hannu ta dauka ta zauna gaban madubin tana shafawa ahankali 

Ganin yanda takeyi yasashi juyawa ya fice Yana gyaran murya sbd muryarsa data Dan shake da wainda yake wayar Dan Haka ya fice yaci gaba da wayarsa.

Tana gamawa saigashi yashigo ya ajiye Mata jakar kayan shopping dinta daya iso yakuma ficewa

Ta bude kayan ta dauki pant da bra tasaka ta shafa turare saita tsaya tunanin kayan sawa sbd gabaki daya ta manta da cewa kafin kayansu su iso saisun buqaci kayan sawa.

Kayan baccin ta daga taduba tana fitarda numfashi me zafi sbd wainnan kayan sanyima kamata zaiyi idan tace ta yini dasu ajikinta Dan babu ta arziki ita saiyanzuma tunanin waya kaita siyansu yafado Mata.

Tattara kayan tayi tasaka wardrobe ta dauki riga daya ta saka ta daure kanta tareda Dora jallabiyarta akai ta tada sallar la’asar da akai hadda azahar da batayiba.

Tana cikin yi yashigo dakin ya Dan kalleta ganin tana sallah saidai baice komaiba ya nemi guri ya zauna Yana waya da Mr Omar dake basa bayanin komai na tafiya akan tsari.

Tana idarwa ta miqe tareda warware nadin kanta takasa cire rigar jikinta batareda ya aje wayar dayakeyi ba yace taje ankawo abinci.

Tanajin yunwa Dan Haka Bata tsayaba ta wuce Ashe Yana bayanta ya zauna dining din me kujera biyu rak ta waiwaya ahankali tace”

Farhat zandubo tazo taci abinci…

Aje wayarsa yayi tareda kashewa gabaki daya yana cewa”

Batanan tana gurin Sarah zata kula da ita.

Da marairaice fuska ta kallesa bama tareda tasan tayi hakan ba 

Ya Dan bude idonsa akanta ganin yarintar datake Shirin zuba Masa Dan kamar zatayi kuka ta langwabe kai.

Saidata zuba Masa komai kafin ta hada ruwan zafi da kanta tazo ta zauna Tasha black tea me zafi tana lumshe ido sbd nutsuwar datakeji ruwan dumin nashiga cikinta.

Abincin kadan taci Tasha magani ta Dan daddaure ta gyara gurin Takoma daki ta kwanta take bacci ya dauketa sbd maganin yanasa bacci shikuma ya hau duba wasu tarin emails daya samu duk a yau din hadda na jiya dabai Samu damar dubawaba.

Bacci tayi sosai sai magriba ta tashi bawai Dan ya saketaba saima kashe Mata jiki da maganin yayi ta tashi da qyar tayo alwala tazo tayi sallah tana gamawa tadawo Palo tadan zauna tareda kunna tv Amma tsoron ganin ita kadaice yasa tana ganin lokacin ishai yayi ta koma daki tayi sallar ishai din tana gamawa ta tube tasake komawa toilet taduba har lokacin shiri period din Bai saukaba sai tayi wanka tafito ta shafa turare kawai tasaka kayan bacci kenan tana tunanin yanda zata koma dayan daki ta kwana ita kadai saigashi yashigo.

##MAMUH#

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button