UBAYD MALEEK 37

Barka da tashi.

Kallonta yayi ya amsa Yana nufota itama taqi tafiya yaqaraso gabanta Yana kallon kayan jikinta Kamar zaiyi mgn saiya fasa ya nufi kofa Yana cewa”

Ki siya kayan sawa ta online su kawo miki.

Da wani kallo tabi bayansa kafin tabiyosa zuwa cin abincin 

Takasa sakewa ta kallesa sai idanuwansa datake na yawo jikinta Haka suka Gama ta miqe ta tattara gurin tagyara ta dawo Palo ta tararda Yana waya saita zauna ta kunna tv takai murya qasa sosai sbd lurada bayason qara ko kadan.

Cartoon ta kunna sbd kewar farhat 

Yana gani ya tsaya kallonta Yana aje wayar ya kalleta ya kalli TVn sai abin Bai bashi mamakiba saima murya daya qara Mata ta remote ta waiwayo ta kallesa tareda sakin wani kyakkyawan murmushi batareda tasaniba tana cewa”

Thank you.

Akaro na farko ya saki murmushi kawai Yana daukan wani file da Mr Omar ya aje Masa wainda zai sakawa hannu.

Zamansa gurin yasa takasa kallon yanda takeso yana lureda yawan kallonsa datake saiya dan dago ya kalleta ya nuna Mata kusa dashi ta taso ahankali tadawo Nan ta zauna ya miqa Mata wayarsa Yana cewa”

Ki siya kayan.

Karba tayi tana cewa” thank you ahankalin shima ya maida hankali kan aikinsa.

Da daddare yau da zazzabi takwana sbd sanyi daya ‘dan shigeta yinin sbd rashin kayan arziki ajikinta shiyasa har asuba tana cikin jikinsa a lullube sai abin yazo Mata da sauki Dan duk Rabin zafin jikinta a nasa jikin ya shige duk da hakan sunsamu yin bacci sosai.

Guraren Sha daya Mr Omar yakawo Dr Damien yazo yadubata yabata yace wancan maganin daya Bata na farkoma zaiyi tashasa kawai zata ji sauki.

Da daddare da kanta tace adawo Mata da farhat baice Mata komaiba sbd baida tsarin komawarta yanxu so yake taji sauki gaba daya ta dawo normal kafin su tafi can sabon gidan.

Sabuwar rayuwar su biyu kadai aka bude a gidan Dan kuwa tuni ta warke ba wani sauran  ciwon komai atareda ita sai period dinta da duka duka kwana hudu takeyi zuwa biyar ya dauke Dan Haka gobema takesa ran yin wankan tsarki.

Da daddare Mr Omar ya sanar dashi wata tafiyar gaggawa da ake buqatan maleek din Dan haka yau din batai wani bacci ba da safe karfe goma Mr Omar yazo daukansu ta shirya cikin riga da wandon pencil jeans da doguwar kimono suka fito Mr Omar yasaka kayansu mota suka shiga suka wuce har lokacin hankalinsa duka na kan waya sbd al’amarin babbane Dan ayanda takeji kaman daga gizah ne.

Zibrian suka Isa cikin qatoton sabon gidansa dake cikeda ma’aikatansu na tsohon gida kowa yakomawa aikinsa tun na tsohon gida hakama kayanta nacan duk ankwaso muta abinda duka,

 suna shigowa har bakin kofar palon Shiga Mr Omar yayi parking mota suka fito Yana kallonta Yana karantar yanayinta 

Suna shiga farhat ta qaraso da gudu ta fada jikin NURU tana cewa”

I miss you aunt.

Sakinta tayi tafada jikin dad dinta tana cewa”

I miss you both.

Janyota NURU tayi tana cewa”

Sweetie zo Naga kafanki 

Ta warke ko?

Bata sakaki zazzabi ba ko?

Na warke aunt NURU kawai dai banajin Dadin bakya Nan Afia Bata nan daddy ma bayanan.

Murmushi NURU tayi tareda duba kafar tana cewa”

Shikenan ai gashi muntaho ko

So muje kifadamun me mum Sarah ke Baki Naga kin qara karfi.

Aunt kema me daddy yabaki kin qara kyau aunt, daddy Nima zanci abinda kasiyawa Aunt NURU.

Shiru NURU tayi cikin tsananin kunyar Mr Omar daya dauke Kai Yana sosawa da mum Sarah data Dan janyo farhat din tana cewa”

Muje mukaiwa aunt dinki kayanta dakinta.

Wucewa maleek yayi Yana Hana murmushinsa bayyanuwa ya nufi hanyar zuwa dakinsa 

NURU ta miqe tabi bayan farhat data Kama hanyar dakin dasukace nata.

Kofar da maleek yashiga Nan suka Shiga wani palon ne dayafi na farko tsaruwa sai kofofin bedrooms guda biyu na maleek shine kurya nata farko Kuma da Alama nashin zaifi nata girma sosai sbd ta fahimci shi mutum ne me raayin makeken daki kokuma tace daga sarautane hakan.

Dakinta ta bude tashiga sanyin AC Dana qamshin turarukanta dake jere a gaban madubi Kamar za’a bude shago dasu suka doki hancinta ta qaraso tsakiyar dakin tana kallon koina cikin burgewa sbd komai na tsarin dakin Kamar ansan raayinta.

Wardrobe ta nufa ta bude tana waiwayowa ta kalli farhat saitaga ba ita zata tambaya ba ta maida kallonta kan kayan dake shaqe da wardrobe din ta waiwaya gefen kayan bacci batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana Jin kunyar abinda tagani ta rufe tana duba bangaren takalma Suma dai kusan duk kowane designer brand akwai.

Gurin wayarta dake gaban madubi ta Isa bayan ta jera kayan data dawo dasu a dauka tareda kunnawa zata Kira gidansu saiga farhat data fita tadawo dakin tace”

Aunt kizo daddy na Kira.

Aje wayarta tayi suka fito tare ta nufi palonsa na cikin kofar bedroom dinsa suka Shiga tareda farhat Yana zaune kan kujera Yana duba wayarsa yaji shigowarsu Bai dagoba saidata kusa isowa dab dashi ya kalleta kafin ya kalli farhat data naniketa Kamar zata gudar Mata.

Kashe wayar yayi tareda Miqewa tsaye da wayar a hannunsa Yana kallonta yace”

Gizah zamuje da Mr Omar duk abinda zai faru ki sanar Dani a waya.

Akwai tight security anan Babu Wanda zai shigo bada izininki ba dan Haka ba kowa za’a bawa izinin shigowanba.

Wani card ya ajiye Mata akan table ya wuce harzai gota ta ya tsaya tareda kallonta yayo qasa ahankali setin kunnenta yafada Mata password na card din Yana fada Mata lips dinsa na gugar kunnanta ta lumshe ido ta bude ahankali tana kasa dagowa ta kallesa sbd kunya ga farhat a tsaye tana kallonsu cikin burgewa duk da batasan meyake faruwa ba farin cikin kawai takeyi.

Kallonta yayi yaso sakin murmushi ya fuske ya wuce ta biyosa baya daf da zai fice palon ta tsaya bayansa ahankali tace”

Allah ya yadawo dakai lafiya.

Yace Amin batareda ya waiwayoba ya fice tabi bayansa da kallo.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button