UBAYD MALEEK 46

Shigowar jekadi ne daukeda tray na silver me Dan girma daukeda dafaffiyar Nonon raqumi da wani ruwan madaran na musamman sai Dan breakfast Mara nauyi
Sai wata kyakkyawar qaramar jaka dake hannunta na akayan NURUn dake ciki wainda ayau din akai odarsu aka kawosu
Cikin girmamawa tace”
Allah ya qarawa maleek lafiya da walwala
Barka da tashi.
Da Kai ya amsa Yana daukan wayarsa dake ringing ta sudada ta wuce cikin palonsa na gaba ta ajiye komai akan dining ta koma palondasu maleek din suke shima
ta zuba Masa breakfast kadan yafara ci Mr Omar naci gaba da koro Masa bayanai.
Sai Sha biyu ta farka ta bude idanuwanta dasukai mugun nauyi fuskarta harta Dan kumbura kadan ta dafa ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya ahankali
tareda rufe ido ta bude tana zuro qafafunta qasa saidai abinda takeji batajin zata iya tashi tsaye.
Shiru tayi agurin zaune tana kokarin miqewa cikin dauriya taji anbude kofar dakin
Bata buqatar dagowa sbd tasan shine yashigo
Jin shiru yasata dagowa daidai isowarsa dab da ita ya rankwafo baice komaiba ya dauketa gaba daya
Tayi qasa da Kai tana rufe idanuwanta yakaita har cikin toilet ya kwantar cikin ruwan dumi ya kalleta tareda shafa gefen fuskarta ya matso da tashi fuskar
yakai bakinsa kunnenta ahankali ya furta”
Sorry.
Zamewa tayi ta kallesa ya sake shafa fuskarta ya juya ya fice yabarta da mamakinsa Bata fito daga mamakinba sai ganin jekadi tayi cikin toilet din da sauri
ta zame cikin ruwan tana shigarda jikinta ruwan tana rufe ido
Kenan shine yake cewa tayi hkr.
Cikin nutsuwa jekadi ta qaraso gurinta tana cewa”
Ni tamkar uwace karki ji komai magani kawai zanbaki wannan sirrinkine da mijinki Nima sbd baisan yazaiyi mikin bane kisamu kyakkyawar kulawa.
Ruwan zafi ta kunna ruwan da NURUn take ciki suka dauki zafi Sosai
Ta bude wata babbar kwalba cikin kayan data shigo dasu ta zuba cikin ruwan take toilet din yadauki wani qamshi NURU kuwa tanajin ruwan na shigarta ta koina
jikinta yafara Dan sakewa Yana Mata wani iri
Jekadi taqara zuba Mata wani abun daban kafin ta dibi ruwan zafin ta zuba cikin wata roba tayi hade hadenta ta ajiye Mata tace”
idan kingama wankan kiyi tsarki da wannan.
Juyawa tayi ta fice sbd tausayin NURUn takeji sbd alamun dasuka nuna tana cikin mawuyacin hali.
Wanka tayi sosai taji dadin jikinta tayi tsarki da ruwan da jekadin ta jiye Mata tun alokacin taji wani irin sauyi Sosai agurin ta Gama tafito ahankali
daureda towel ta nufi gaban mirror dinsa ta shafa mansa tareda spray ta dauki kayan data gani an ajiye Mata Wanda da Alama jekadi takawo ta daga kayan tana
kallo dukkaninsu Babu me nauyi duk na Shan iska ne
Bata wani damuba sbd jirin datake gani ta saka wata doguwar qaramar riga Mara nauyi tayi drying gashinta daqyar ta ‘daure da sabon band fito palon tana
tafiya ahankali jekadi dake tsaye dining tana jiranta tai Mata sannu tareda ja Mata kujera ta zauna tana gabatar Mata da abubuwan dazata fara Sha kafin
komai.
Daqyar ta daure Tasha duka ko abincin Bata iya tsayawa taci ba Takoma daki ta kwanta
Jekadi ta tattare kayan ta fice dasu
tana fita Mr Omar ya sulale yabi bayanta Dan bawa maleek lokacin hutawa
Ya miqe ya koma ciki Yana duba lokacin sallah da yayi.
##MAMUH#*_Mamuhgee 47_*
Bacci takeyi har lokacinda ya Shigo din,ya kalleta tareda sauke boyayyar ajiyar zuciya ya juya ya nufi toilet yayo alwala yazo ya fice batareda ya tada ita
ba Dan baccin Yana Bata nutsuwa da damar yanayinda takeji.
Yana fita bada jimawaba ta farka ahankali ta tashi zaune itama tayo alwala tazo tayi sallar Takoma ta kwanta tanajin zazzabin datake ji na qara shigarta ta
lumshe ido tana sake shigewa bargo idanuwanta a rufe.
Qarfe goma aka Isa da lailah airport acikin wata sirrantacciyar mota
Lokacin afia tafi mintuna ashirin agurin tana jiran isowarsu Dan Haka tana ganinsu ta fiddo doguwar jallabiya da Dan qaramin mayafi da goggles datazowa da
mum din Tata dashi ta nufi motarsu itama tata fuskar Bata bayyanataba yanda za’a gane itace ta bude motarsu ta shiga baya inda mum dinta ke zaune tana
kakkama jikinta tayi wani duhu cikin kwana biyu ga wani irin tsamin dauda da wahala na tashi ajikinta
Cikin tsananin baqin cikin ganinta Haka da kaunar mahaifiyarta me qarfi afia ta rungumeta gabaki daya tana cewa”
Mum.
Zarewa Lailah tayi ta kurawa afia ido idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin baqin ciki da dumuwa tarema da tsoron halinda rayuwarta tashiga kokuma ma
Wanda tariga tashiga,
Ahankali ta bude Bakinta dake rawa wani tsamin Baki ya feso yacika motar Amma afia ita Sam batama jisa sbd Babu abinda uwarta zata zama ta gujeta da rawar
murya tana hawaye tace”
Afia,afia my baby,afia my little princess I’m sorry baby ki yafewa mum dinki Amma ki yarda Dani bantaba aikata kisa ba Kuma bazan taba aikatawaba…ban
aikata ba…bazan taba iya aikatawaba…ban aikataba…banyiba…
Riqota afia keyi tana cewa”
Mum mum na yarda Baki aikataba
Mum na yarda
Na yarda mum”.ganin mum din takasa daina fadar Bata aikataba cikin firgici Kamar lokacin abin ke faruwa yasa afia rikicewa tana korarin kwantar Mata da
hankali cikin kulawa hankalinta na neman tashi sbd ganin alamun kaman mum din har lokacin tana cikin shock saidai Kuma….
Imran ne cikin hali na damuwa daya shiga akan lailan tun lokacinda Mr Omar yayi Masa bayanin komai gameda Dan tabuwa da kan lailan yayi sbd Shiga hali na
shock lafiya zata ringa komai Kamar yanda take sai dai idan ta tuno abindaya faru na kisan abin zai dawo Mata zata fara fizgewa tana fadar ba ita tayiba
cikin tsananin tsoro da firgici,
Shi kansa bazaiso afia tasaniba sbd hankalinta zai tashi yakoma kan kula da neman lafiyar mum dinta bazata taba maida hankali kan karatuntaba Kuma Dan Haka
shima ya shirya kula da al’amarin bazai Bari tasaniba yanzu sai tagama kammala karatunta tsaf yanama fatan zuwa lokacin lailan tasamu lafiya Dan Haka shima
ya yanke shawaran komawa Vegas gabaki daya zai zauna da lailah Dan nema Mata lafiya ta dawo daidai ta gyara rayuwarta ta ingantata yanzu kan tunani da
hanyar dazata bullar da ita sbd Lailah tamkar uwa ya dauketa Dan kuwa itace wadda tafi sonsa aduniya bayan iyayensa sbd itanema yake Paris baibi iyayensaba
Koda tabar maleek dasu afia Basu rabu ba shida ita Kuma sbd itane yake tareda maleek Yana aiki a qarqashinsa farko sbd ya kula dasu farhat dasuka shaqu.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda fitowa ya zagayo yashigo bayan ya zauna dayan gefen lailan suka sanyata tsakiyansu ya dago ya kalli afia data fara
shiga firgici cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace”
Tana cikin damuwar abin daya faru sbd case na zargin kisa wani abune da bakowa ne zai iya daukaba
Dole zata shiga wannan halin musamman yanzu data fito Kuma taganta agabanki Dole zataji wannan damuwar da shauqin son sanar dake ba halinta bane.
Hawayene suka gangarowa afia ta rungumeta tana sakin siririn kukan tausayin mum dinta ta dago tana kallonta tace”
Mum Inshallah komai yariga ya wuce bazai sake dawowaba
Ki yarda da wannan wata jarabawace Allah yayi Miki danki gyara Kuma Inshallah nasan kin gyara mum kimin alqawarin bazaki sake zuwa gizah ba sbd bakida
abinda yarage Miki anan sai tarihi.