UBAYD MALEEK 46

Kallon afia kawai lailah keyi da idanuwanta dasukai jajir tanajin radadin abubuwa da dama data rasa arayuwarta sanadin son zuciya da son Rai,
Ta rasa MALEEK namijin da bazata taba samun kamarsa ba a fagen komai Dan kuwa ya nuna Mata so da kauna da gata da kulawa da komaima Amma duk ta watsar ta
tsallake a tunaninta zai zauna dakon jiranta,
Ta rasa Farhat dinta yarinyar da Bata morewa komai na soyayya ko kulawar mahaifiyaba da shaquwa Dan kuwa tasan NURU tariga tashiga ran farhat ta yanda
bazata iya rabuwa da itaba ko yiwa wani kallon uwa idan ba NURUn ba,
Ta rasa darajarta,sunanta,mulkinta, dukiya da career dintama gabaki daya
Afia ce kawai abindake gareta yanzu sai Imran datasan har abada shima bazai gujetaba adaidai yanzu datafi buqatan masoyanta atareda ita.
Kama hannun afia tayi ahankali hawayenta suka gangaro kan fuskarta ta kalli afian tareda gyada Mata Kai tace”
Nayi alqawarin Inshallah bazan qara zuwa gizah ba sbd Nima na tabbatarda banida sauran komai anan sai tarihi Wanda bana alkhairi ba Dan kowa zai ringa
tunoni amatsayin wadda tayi kisa labarinta ya Bata.
Sake karyewa zuciyar afia tayi da tausayin mum dinta ta yanda lokaci daya ta rasa komai Kuma tana fatan zatai tawakalli ta karbi hakan.
Kayan data shigo Mata dasu ta Sanya Mata tareda rufe Mata fuska ta Sanya Mata goggles din ta bude motar suka fito dukkaninsu ta sake damke hannun mum din
cikin kulawa da qauna ta tsakanin ‘da da mahaifi tace”
Mum ki kula da kanki Zan ringa kawo Miki ziyara lokaci lokaci kinji¿
Ajiyar zuciya lailah tayi tareda kallon afian akaro na farko rayuwarta tace”
Allah yayiwa rayuwarki albarka afia
Allah yabaki ‘yayan dazasu San darajarki irin Haka da Miki biyayya.
Amin tace ahankali tana dagowa ta kalli Imran tace”
Mum na hannunka.
Guntun murmushi ya saki Yana gyada Kai yace”
tana hannu mekyau.
Murmushin yaqe tayi tana cewa”
Thank you.
Kama hannun lailan dake waiwayen afia tana daga Mata hannu yayi suka wuce itama afian tana musu har suka bace Mata ta saki numfashi a hankali tanajin
nutsuwa ta juya ta fada motar da kanta ta jawo ta tada taja tabar airport din.
Ko data koma sashenta ta nufa sai alokacin tasamu nutsuwar cin abincin data manta rabon dataci
Taci ta koshi ta miqe ta wuce bedroom dinta tayi sallar azahar ta kwanta Dan tasamu baccin dazai qarasa wargaza damuwarta Dan kuwa dukkanin damuwarta ta
yaye takeji.
NURU zazzabi yakamata sosai Wanda ya Hana musu bacci da daddare daga ita har maleek din sbd sosai jikinta yayi zafi tana kwance cikin jikinsa Yana rage Mata
zafin jikin da nasa Dan kuwa yanajin yanda dumin jikin nata ke shigarsa Yana saukan Masa da kasalar sake shigar da ita jikin nasa itakuma tana lafe tana
sauke numfashi ahankali cikin sanyi.
Kallonta yayi cikin Dan qaramin hasken dakin Ya shafa bayanta ahankali Yana sake ce mata”
_Azinalehu_ (Sorry) cikin kunnenta da wata sirrantacciyar muryarsa da tsakanin jiya zuwa yau tasanta.
Ahaka yayita lallabata suka samu bayan sallar asuba tasamu bacci ya dauketa me nauyi sai alokacin yasamu nutsuwar kansa ya gyara Mata kwanciya tareda fitowa
Palo sanyeda milk jallabiya me taushi ya zauna Yana daukan wayoyinsa ya kunna sbd yau yakeson Kai qarshen matsalar komai tunda sungama hada dukkanin
shedodinsu dasuka tabbatar musu da zarginsu Akan Wanda suke zargi
Yana buqatan komawa Paris kodan rashin lafiyan Nan daya sameta.
Mr Omar yakira Kai tsaye yace”
A bayyanarda duka shedu akan yakoob a cikin kotu yau.
Cikin girmamawa Mr Omar yace”
Maleek haryanxu Yana maganar son ganin ‘dansa Kuma idan aka bayyanar a kotu cewan ‘dansa ne ya mutu zai iya bayyana komai a gaban kotu Wanda zai taba gizah
da Kuma Anneti sbd al’amarin zaizo Mata da tashin hankali tunda Bata taba tsammanin hakan ba daga Wanda take aure
Kana ganin yakamata mu fitar da zancen duka a kotu?
Yan media zasu yada abin fiyeda komai ta yanda zai Yi Muni.
Shiru maleek yayi na wasu mintuna kafin yace”
Yanada damar yasan mutuwar dansa saidai baida damar fadar komai bayan abubuwan daya aikata da wannan za’a yanke Masa hukunci basai anbari yafada komaiba
bayan wannan…..
Shiru yayi Yana kokarin daure abin dayake ji a zuciyarsa dasuka bayyana a idanuwansa yaci gaba da cewa”
Neges Kuma sbd daraja ta auren Anneti zanji da matsalarsa ta cikin gida batareda duniya tasan abin daya aikataba sauran haqqin Rai dake kansa Kuma
tsakaninsa da ubangijinsane.
Cikin yanayi na sanyi shima Mr Omar yace”
Allah ya kyauta ya sake tsare imaninmu
Allah Kuma yaqara maka tsarkin zuciya.
Ba Haka suka so ba duk su dukan Amma Kuma wani lokacin kanayin abinda shine zaman lafiyar kowa da Hana fitina.
Lokacinda aka tafi da yakoob har mortuary aka jawo gawa tareda yaye Masa yaga gawar ‘dansa amed datai fari tas sbd ajiya da sanyi.
Sarewa qafafuwansa sukai sbd firgicin ba zata daya fizgesa lokaci daya da wannan mugun ganin dayayi
Cikin tashin hankali ya zube gaban gawar Yana ihun Kiran sunan”
Amed Amed Inidēti ibakíhìni¿
Yaushe wannan mummunan Abu yasameka batareda nasaniba?
Amed katafi kabarni Banda kowa sai kai.
Dagowa yayi cikin ficewa hayyaci da tashin hankali ya kalli Mr Omar Yana cewa”
Meyasa???meyasa??
Ta yaya?
Yaushe kuka kashesa?
Meya muku?
A Daren ranar daya tafi aikin neges yamun saqon cewa Yana lafiya tafiyan gaggawa yayi…..ko shekaran jiya yamun sakon Yana lafiya Dana kira..yaushe kuka
kashesa…..
Kukan tashin hankalin masifa yakeyi sbd sanin tsaf wannan umarnin maleek ne ya sake gangaro da hawayen baqin ciki jikinsa na daukan rawar Shiga tashin
hankalin rashin tsammani na wannan afkuwar dabai taba kawowa aransaba ya rasa dansa kwalli kwal Wanda duk suke wannan fafutukar rayuwar dansu tsira su Tara
abin kansu su gudu wani gurin su Gina rayuwa.
[ad_2]