UBAYD MALEEK Page 61 to 70

Afia ta kalla zatayi magana
Afia tarigata da cewa”
Ina wuni mum.
Kin amsawa tayi tana cewa”
Wannan shine sabon manner dinki da farhat?
Da mamaki afia ta kalleta tace”
Sabon manner kuma mum?
Maida kallonta tayi kan farhat dake jikin NURU tana kallon lailah da dukkanin hankalinta sbd tanason zuwa gurinta tana shakkar irin tsawar da lailan ke Mata wani lokacin duk Bata mantaba sbd lailah batason Ana fado Mata ajiki kokuma yaro yace koyaushe Yana cikin jikinta.
Farhat kixo ki gaida mum.
Wani kallo lailah tayiwa NURU wadda gabaki daya Bata sake kallon inda lailan takeba sbd Jin take gabaki daya dakin ya gundureta ga Mr jalal ya fita ta zare hannunta daga na farhat da har lokacin take tsaye bataje gurin mum dinba ta nufi gurin Imran daya bude idanuwansa alokacin ya zuba Mata ta qarasa gurinsa ta zauna kan sofa ta qaqalo murmushi daqyar tace”
Ka tashi kenan Yaya jikin?
Bai dauke kallonsa daga kantaba ya gyada kai Yana miqawa farhat hannu cewa tazo.
Lailah zuwa lokacin ranta yafara baci sbd kowa sai acting dumb yakeyi ta gyara zama ranta nafara baci akan afia tace”
Afia nice na haifeki komai girman dakike ganin kinyi Dan haka you better stop acting dumb with me kafin ranki ya baci kokuma kinason nunamin zama da bayi kin manta girman uwarki,…
Da mamaki afian take kallon mum din cikin rashin sanin abinyi tace”
Mum please idan wani yabata Miki Rai acikinmu daga zuwanmu kiyi hkr Amma wlh Ni bansan me mukayiba anan,
Farhat kije gurin mum ki gaidata nace….
Just shut up afia
before I lose my cool ki fita daga gabana Dan Naga gabaki daya kin rasa tarbiyanki Kamar Ni Ina Miki magana kina cewa Farhat ta gaidani sbd nace Miki gaisuwan ne agabana kawai.
Hawayene suka ciko idanuwan afia sbd gabaki daya batasan metayiba da mum din keta faman wannan janye janyen ta bude Baki cikin rawar murya tace”
Kiyi hkr mum Amma dai kaman kina saukemin fadan da banawa bane.
Sai alokacin NURU da duk takejinsu ta Dan waiwayo afia din takai hannu zata dafata sbd ganin yanda hawaye suka tsinke Mata
Lailah ta aika Mata wani qanqantaccen kallo tana cewa”
Excuse me miss wannan tsakanin uwa da ‘ya ne stay within ur limits ok
Bana saka trashes cikin al’amurana
For God’s sake ma meyasa haryanxu kikeda auren MALEEK akanki bayan duniyama tasan bazaki tana zama Matar da maleek zai iya zama da itaba
Ke yarinya ce bazaki gane hakan ba Amma nasan Zaki gane kalmar pack and leave sbd ma nafasa komawa San Francisco zandawo gidan sbd afia na wannan little ant din sun dauki wani hali da bazan dauka ba..
Jekadi da padima dake bakin kofa suna Jin komai dadin duniya yagama kashe padima duk da Jin takeyi Kamar tashiga tayiwa lailan mugun duka Amma dai Kuma yanda take nuna isarta akan ‘yayanta da NURU ta mallake yasata Jin Dadi taji inama tanada ikon shiga dakin taga yanayin NURU sbd har lokacin NURU Bata juyo ta sake kallon ko gefenda lailah maleek takeba sai lokacinda tace zata dawo rayuwar MALEEK NURU ta waiwayo ta kalleta daidai suka hada ido lailan ta gyara zama zatayi magana aka turo kofar data Sanya NURU kallon kofar da idanuwanta dasukai jajir sukai ido biyu da MALEEK Wanda Mr Omar ya budewa kofa
Shima ita ya kalla dakyau sbd baisan da zasuzo asibitin ba Amma ganin su jekadi a waje yasa yasan suna ciki.
Dauke kanta tayi tareda maidawa kan Imran sbd rashin sanin abinyi Dan gabaki daya dakin jintake numfashinta a toshe yake.
Lailah dake zaune har lokacin ta zubawa maleek fararen idanuwanta tana jiran abinda zai fara fitowa daga bakinsa idan ya idanuwansu suka Shiga cikin na juna.
Da fararen idanuwansa ya kalli Imran dake kokarin tashi Amma Babu me kamasa sbd NURU ce kawai a kusa dashi afia har lokacin tana gaban mum dinsu hawaye take na baqin cikin wannan halin da mum ta nuna.
Cikin kamewar murya Kai tsaye MALEEK yace”
Kana samun sauqi kenan,
Allah yaqara lafiya.
Maida kallonsa yayi kan NURU dataqi waiwayowa ta sake kallon kowa ahankali yace”
Muje.
Dagowa tayi ta kallesa direct cikin ido kafin ta dauke tana miqewa tsaye da wayarta a hannu ta wuce batareda ko sai anjima tayiwa Imran ba sbd a rayuwarta Bata taba yin mummunan danasaniba Kamar zuwanta asibitin Nan yau.
Tana fitowa Jekadi ta taso zata bita Mr Omar yayi saurin Yi Mata hannu Yana nuna Mata MALEEK da ido Takoma ta zauna tana cewa”
Allah ya tsare hanya MALEEK.
Harya fita ko afia alamu Basu nuna yasan dasu a dakinba bare lailah harya fice,
Ita kanta afia tashiga shock
ta dago ta kalli mum dinsu da Bata nuna damuwaba sbd tasan halin MALEEK dama Dole saita fuskanci fushinsa kafin yasan yanda zata sauko dashi dakanta sbd soyayyarta me qarfi dake ransa,
Ganin NURU yanzu datayi yasa taji bazata iya komawaba tana buqatar kasancewa da maleek yanzu Dan kuwa batai tunanin NURUn takai hakanba duk da yarinyace Amma tanada wani irin kwarjini me fizga.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 31_*
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215 / 09044191709_
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
*************
Mr Omar ita yafara budewa kofar mota tashige kafin ya zagaya ya budewa MALEEK yashige shima ya zagaya yashige ya tada suka bar asibitin sbd fita irin wannan Mr Omar shine yakejan MALEEK hardai idan zasuyi sirrantacciyar magana sai basa fita da drivern maleek din.
Tafiya suke Babu me magana acikin motar sai numfashinta dake fita ahankali ahankali sbd nauyin da kirjinta yayi.
Dan dagowa yayi ya kalleta ahankali tareda ajiye wayar hannunsa ya maida kallonsa kan wani envelope daya bude da muryar me kamewa yace”
Today shud be the last time.
Ajiyar zuciya ta sauke me dumi kafin ta waiwayo ahankali ta kallesa da idanuwanta dake bayyanarda halinda zuciyarta ke ciki na tsananin tarin damuwa me nauyi sbd Jin guntun zancensa.
Batareda ya kalletaba Yana cigaba da karanta takardar yace”
You deserve it.
Wannan karon cikowa idanuwanta sukai da hawayenda batasan lokacinda suka balle mataba dama kukan take buqata kozataji saukin damuwarta.
Mr Omar guri yasamu gefen hanya Mara mutane sosai da hayaniya yayi parking tareda budewa ya fita ya rufo musu kofar yana matsawa daga gurin.
Ahankali shehekar kukanta yafara fita sbd takasa daurewa kuka takeson yi.
Shiru yayi tareda dungurar da takardar sbd gabaki daya baya gane me yake karantawa ya lumshe ido ya bude ya juyo ya kalleta
Kuka takeyi hawayenta na gudu akan fuskarta ya zuba Mata idanuwansa gaba daya akaro na farko dabaisan mezaiceba.